HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Maza anci ansha ,kowane Dan uwan Alh d Yan uwan Ammy sunyi sanbarka d bikin ,Bayan sunci sun k’oshi masu nisa suka Fara d’aukan hanya wasu Kuma sai gobe ,Amman fin rabi sun tafi ….

Gida y cika ‘yan wuni sun Fara zuwa ,anata fama ci d Sha su suffaya d Aishatu ancire shadda an sake shigar wani material Mai matuk’ar kyau d tsada ,yayin d amaren suketa Shan kwaliya d shiga takece raini ,su heedaya d nawara har anbayana har Inna d maman nawara d aunty zainab duk sun Zo ,ammy nata Nan Nan dasu anwadatasu d kayanci d Sha ,iyayen suffaya ma sun Zo ,har maman NAWAL ita kadai sai karya t musu NAWAL ma na Nan zuwa ….

Ansha shagali anci ankoshi ,har yamma tayi magriba tayi anfara Shirin tafiya dinner ,Bayan sallah Isha ,wasu d dama Basu salaci ishar ba Amman anshiryama dinner ,Dan da dama haka wasu sukeyi basa tunanin mutuwa zata iya ruskar su ako Ina , ALLAH y bamu ikon kiyayewa ,Ameen ….

 

Ankawo motoci gidajen angwaye Bayan angama tsarama Amare kwaliya sunyi kyau tun agida anata kwasan hotuna dasu …

An dibi mutane sosai kusan ankwashe su sai kadan masu dahir din mota a hanun su irin su amaren d su aunty balaraba dake d motar ta zata tare d huzna Dan tasan Bata d waje cikin motar safwan …

Sai safwan din d Yaya ,sune Yan karshen tafiya cikin wata shiga ta codelece Mai kyau d tsada blue d zaiba to March jaka d takalmin ……..

 

NAWAL ma d kyar aka kece raini aka d’auki lawy aka zari makulin mota Dan ta Fara gajiya d mitar mama Dan Haka ta tafi ko t huta ……..

 

*Maman shaheed*????
[3/3, 3:31 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAM SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi n sittin d uku_

 

“`mosoyan novel din Kuskure masu cewa 2 page per day 1 page din ma Yaya “ku Kara hakuri Ina matuk’ar kokartawa kude kasance tare Dani har zuwa karshen novel din sona y isa“`

????????????????????????

 

“NAWAL ta riga Aishatu d safwan zuwa hall din dinner tun zuwanta take raba Ido kamar me neman akuyarta Dan ganin wacce shiga ‘yar Aikin tata ta dacan tayi wacce ayanzu ta zama matar mijinta …..

Har t gaji t nemi waje ta zauna suka ita d kawarta ,suna wani kalon kurila…..

Aunty zainab d nawara kusan tare suka karaso Dan seda suka biya suka d’auko aunty zainab nawara d mijinta ….

Aunty zainab nashirin shiga suka hadu d sadeeq yaron shagon *SAUDIY PASSION* inda take saran Kaya ….

Cikin girmamawa y Fara gaishe ta ,ta amsa d fara’a ,tace bade bikin d kuke cemin y shige muku gaba bane har y Hana sana’a Kai d oganka ?

Sadeeq yace wlh shine ai gagarumin bikine kinsan brother na Saleem shike Auren daya daga cikin amaren ,bade kema shine bikin dangin mijin su Aishatu Taki d kike fada Mana ba?

Aunty zainab tace shine wlh ,to amaren ai kannen mijin Aishatu tawa ne ,sai sadeeq yace ayya rashin sani Ashe duk Abu dayane ,rashin sani ,Ina Aishatu mugaisa ?

Aunty zainab tace eh wlh zuwanmu kenan bamu hadu d itaba ,Amman ai inkatuna yaran nawa guda 2 ga nawara dayar Yar tawa ….

Sadeeq yace hakafa su biyu Ne kamar yadda Kika fada Mana nida mallam …

Nawara tayi murmushi tace Ina wuni?

Yace lpy ,y gida y oga?

Tace lpy lau ,y juya haka ze tafi ,Yana cewa ma hadu d Aishatu ko zuwa anjima barin duba wani brother na ! Sai Aishatu hannun ta rike d Noor cikin wasu mayun ‘yar kanti doguwar Riga kanta d Abun sarauta Mai zaiba ankame Mata kanta d ribom tayi matuk’ar kyau harda jaka ga wani takalmi Mai kasan kwalba harda glass d Abin hannu d agogo Mai kyau n yara taci kunshinta Baki d ja Noor tayi kyau Aishatu t gyara kayanta ,d sauri Aishatu tazo t rungume Aunty zainab Tana aunty na bade kugaji d jirana b sai yanzu muka karaso wlh …

Aunty zainab tace aa zuwanmu kenan ,sadeeq ga Aishatu ,suka gaisa Yana binta d wani kalo kamar yaso yasanta ko yane shide y rasa ganewa ,har safwan y karaso shima y gaishe d su aunty zainab suka gaisa d sadeeq ,Ashe sunsan juna sadeeq junior safwan ne a school ,Bayan sundanyi Hira sadeeq y tafi su aunty zainab suka yi gaba ,safwan d Aishatu na bayansu d Noor a tsakiyan su ,suna wani takun birgewa d Sha’awa ko Amarya bazata nunama Aishatu had’uwa ba …

 

Suna shiga kalo y dawo kansu yayin d kowa y Fara Jin sunan safwan d Aishatu na tashi a speaker ,Ana musu barka d karasowa duk d sunzo a makare Dan Haka kowa hankalinsa yayi kansu , Aishatu batasan d hakaba ,ganin anata kalon su ji tayi kamar kasa ta tsage ta shige ,ganin karta kwafsa kawai t maze ta Fara taku daya Bayan daya cikin birgewa hanun ta rike d na Noor kowa kalon su yake harda masu binsu d coverage d camera har zuwa masaukin da aka tanadar musu ,sanan aka saki wani kida…

Yaya nee kusa d safwan dake su sunrigasu zuwa ,suka Fara Hira kasa kasa …

“NAWAL hawan ruwanta d na jinin tane gaba daya suka hau Dan ganin bazata iya jurema kalon safwan d Aishatu ba ,idonta ruwa y kawo ga tafasa d zuciyarta takeyi ,sai d suka doshi wajen zamansu ,taji bazata iya zaman ba kawai ta zari makulin motarta t fice daga hall din …..kawarta ce ta bita waje ….

Lawy Ce ta dinga
Bata Baki Tana ladaftar d ita dabarun d zatayi Amfani dashi Dan kwato mijinta d ‘yarta tilo ,t nuna Mata fushin fari b nata bane Tabi komai d sauki ,da kyar ta dawo d ita cikin hall din ,Amman duk lokacin d da kalesu sai kirjinta y buga ,t Rasa Gane dalili ,kishi? Ko bacin Rai? Can tace duka biyun ,Indo d safwan a inuwa daya ? Safwan meya zama harda murmushi ji yadda suke Hira irin wata shakuwa ta ratsa tsakanin su ? Safwan kansa daya kuwa ? Shine Wanda n sani? Kai d sake wlh badai Indo ba gwanda kowace iriyar macce y aura Amman b Indo ba ,dubi Indo kamar wacce akama wankan injin a kasar India? Shegiya karuwa Daman boyayyen kyau ne ita?

 

Duk wanan karatun cikin zuciyar NAWAL ne ,ruwanta gab yake d hawa ,Dan Kara hango kyawun Indo take ,ga wani shakuwa tsakanin indon d Noor wani ma yace ita ta haifeta ,tace Kai Ina Bata Isa haihuwar my Noor b shegiyan yarinya , ALLAH yasa Bata d kwayayen haihuwa ma shegiya t dawama a rashin yara ,mayar yaran mutane kawai d wanan t yakeni a cikin gidana ta kwace su d mijini ….

“itako Aishatu d safwan sunata hirar su t so d k’auna ,’yan police band sunata gwangwajesu ,Noor nata takawa Ana Mata liki….

Waje y kawatu Abinci d Sha b irin Wanda Babu inbe makaba ka kara sai abinda kakeso zakaci bame kulaka ,su nawara d aunty zainab anata hira….

Aka gayaci amaren d angwayen domin daka rawa ,tare d gatansu sufito su nuna musu gata na liki ,Aiko aunty balaraba d huzna sune farkon fitowa aka Fara musu liki ta ko Ina Ana wani kwarkwasa huzna …

NAWAL ganin huzna aka saki wani uban tsaki ,aka zageta ,harara a duhu …..

Safwan d Yaya suka fito d matayen su ,suka dingama amaren d angwayen liki ,anata musu coverage d camera t ko ina ,huzna harda wani iyayin likama safwan kudi Tana wani Abu kamar zata shiga jikinsa ,Aiko ganin huzna na Shirin afkama mijinta Aishatu t zaro kudin d yafi n huzna ta Fara likama mijinta tanayi Tana fadawa jikin shi ,shima ganin Dan akular d huzna NE Fara mayarma d Aishatu liki d manyan kudi Yana rungumota Yana Mata dariya ko so 1 be likama huzna b sai aunty balaraba d y likama sai amare sai matarshi sai Noor din shi ,huzna Abin y kular d ita ba shiri t fita a filin rawar ,suffaya t Kali Aishatu t daga Mata gira Alamar tamata daidai …..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button