HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Duk abinda ke faruwa NAWAL n gani ,itama takaici y kusa sheke ta ….

Har suka koma suka zauna ,safwan waya akamai y fita waje ,itama Aishatu t tafi wajen su aunty zainab d nawara d heedaya t gansu tare ,suka Fara Hira Tana tambayan su Babu abinda suke bukata ko?

Nawara tace eh ,me ciki d angon ki me tsaron ki ,ko rawar kin kasa sai d kikaga za akwashe shi ayi rawa dashi Kika zabura , Aishatu tace munafuk kina kalon komai Ashe ,y nauyin jiki d jiwon kafar ,Amman kin Dena yanzu ko?

Nawara tace d saiki za’ace , Aishatu tace heedaya y dai komai normal ko Naga yau ustazanci kikeji ,heedaya tayi dariya tace har yanzu ba’azo wakarmu bane ,e lokacin d zan zabura bazanyi shawara d kowa ba saidai agani cikin fili ,sukasa dariya ..

Aunty zainab dai cewa tayi , Aishatu karki motsa jikinki d kyaufa ,bazakiji jiwo b sai kinzo kwanciyar bacci ki taka a hankali ,Noor CE tazo d gudu t fadoma Aishatu tana aunty Kinga momyna tanata kirana naje?

Kowa y Kali inda NAWAL take , Aishatu neman safwan t farayi

Ta tuna Yana waje ,ganin Noor n neman umarnin t ,kawai tunawa d tsakanin da d mahaifi sai kawai tace Noor din taje t gaisheta ta dawo d wuri Amman kafin dadyn t y shigo ….

D sauri Noor t tafi ,rungumeta NAWAL tayi Tana yaba tsarin Noor din d irin kwaliyarta amman acikin zuciyarta ,girman Kai baze barta bayanawa a zahiri ba ,cikin tarbiya Noor t gaisheta t amsa ta juya t gaisheta lawy itama cikin fara’a t amsa …

Noor ,Baki sake cema dadyn ki y kawo ki kigaishe d mama d Abba ba ko? Noor tace ai zance wani lokacin, NAWAL tace au sai wani lokacin ma? Ashe har yanzu Baki isar d sakon d n bakiba ko? Noor tace wane sako momy? NAWAL t yi ajiyar zuciya tace d nace ki dingama dadyn ki mgn kidinga d kuka Akan d’auko ni y dawo Dani gidan ku ,Amman karkice Ni nafada Miki f ,Dan b wani wayone dake ba , sai lawy t sa dariya tace shegiya wayace Miki barno gabas take ,rashin dabarun ki su suka hanaki komawa ga megidanki ,ko Baki fada b Abun n damunki munsani …

NAWAL t harari lawy tace magulmaciya eh din ,Noor kinji abinda n fada Miki ? Noor tace eh ,Amman momy kema ai Zaki iya tahowa d kanki yau kizo mu tafi kawai ki kwana acan !

NAWAL t dafe kanta ,lawy tace ato kince Bata d wayo gashinan t nuna Miki iya wayonta ,NAWAL t harari lawy tace kifa Dena shiga sabga ta d ta Noor Naga wani lokacin bakya tsayawa a iya matsayin ki! Ganin ran NAWAL na Shirin baci sai lawy tace ALLAH y bada hakuri me yarinya ,gyara kayanka baya zama sauke mu raba , …

Noor d tagaji d hiran momyn ta sai tace zantafi wajen aunty Aishatu ,tace n koma kafin Dady na y shigo ya tafi amsa wayane waje ….

Jin Haka ,NAWAL tace ,iyeee har umarni take Baki ko Ni takeba? Barin je na Sami safwan din naji meyake nufi d sakarma Indo komai nagidan sa?

T Kama Noor sukayi hanyar waje neman safwan …..

Aishatu Bata luraba sai d heedaya t tsegunta Mata ,Aiko d sauri Aishatu t yi yunkurin binta ,sai Aunty zainab t dawo d ita tace karsuje suyi hayaniya …..

Sai Aishatu tace hakane Dan ashirye take barin Fara Kiran safwan din naji ,t daga waya t kirashi y d’auka ,y Fara tmby tajishi y Dade ko?

Tace eh ,yace wlh wani abokin shi y hadu d shi Kuma sunjima basu hadu b sai yanzu shine hirar yaushe gamo t tashi ….

Yana cikin waya d Aishatu y hango Noor rike d hanun NAWAL suna doso shi ….

Aishatu tace dama momyn Noor ce t fito d Noor karna biyota kasan Abin hayaniya baya Mata wuya shiyisa n Fara sanarma ko kun hadu d su?

Yace eh gatacan Bagan ta kyaleta bani d ita ,inda wani Abu zan kiraki nagansu gasunan suna zuwa inda nake ….

Aishatu tace yauwa shikenan ….

NAWAL n karasowa ,tace safwan wai me kazamane Dan ALLAH d har zaka dinga tinkaho d iko akan Kai namijine tsayaye Amman wata kucaka Mai wanke wanke d shara Tana juyama gida?

Ba ko sallama bare Gaisuwa ,yace me akayi Kuma sarauniyar neman magana?

Ta Harare shi tace ,wai nace noor tazo mu gaisa a matsayina n uwarta ,sai waccan banzar tace wai karta Jima tadawo yanzu kamar ita ta haifarmin ita?

Safwan yace hmmmm Mai Hali baya fasa halinsa ,ba ita ta haifar Miki itaba kawai dai ita Mai bin umarni ce ,Ina nufin umarnina take bi Ni nace ayi hakan…

NAWAL tace ok ,yayi directer ,kun rabani d haneef me kuke nufi Akan Noor ne Dani?

Safwan yace , ALLAH buwayi maiyin yadda yaso asanda yaso bame hanashi Kuma Dan kuwa ba Wanda y Isa ko yakai a fad’in duniyar Nan ,shine y rabamu d haneef gaba dayan mu b ke kadai ba Dan Haka kidinga sanin abinda kike furtawa ….

NAWAL tace hmmm ,Haka zakace dama ,Amman kasan inada hakki akan Noor ko? Yace sosai ma kuwa !

Tace ngd d kasan haka ,inaso k bani Noor t koma wajena d zama n d’auki nauyin komai nata har school d’inta …

Safwan yayi murmushin takaici ,yace Baki Kai ba har yanzu ,Ina nufin Arzikin ki yayi kadan wajen insakar Miki ragamar Rayuwar Noor ,bangaza ba bazan gaza ba Kuma ,Arzikin ki baikai Nan ba ,ki Kara nema kafin ,wanan ai sai safwan mahaifi ga Noor duk nauyinta b Wanda nataza ,har nangaba insha ALLAH!

NAWAL t Zo wuya ,tayi tsaki mtswww ,matsalar ka girman Kai halinka Yana Nan Babu canji ko safwan ?

Yace yess indai naki be canja ba y nawa ze canja ? Barin gyara Miki Ra’ayi ne Dani ba girman Kai ba …

NAWAL tace wlh girman Kaine , d karya d rashin cika Alkawari ,wanne irin Alkawari ka daukar min kafin Auren mu d Bayan Auren mu Amman ka kasa cikawa? Wlh safwan Kai butulune Kuma maha’incin soyayya mayaudari ,kabama duniya mamaki Mai matawa d kalmarnan Mai nauyi d daraja wato “so” wlh kaci amanar so ,wai nice abar wulakantawa agareka safwan ? Kamanta d abubuwa d dama muryarta n rawa tanata tuno Mai d abubuwanda tajima Tana neman damar d zata fadamai su tayi imani d Dole tasashi cikin yanayin begenta matuk’ar kalamanta sun shige shi ! ..

Daga baya ma kukan kwace Mata yayi ,tanata tuno Mai d abubuwan d suka gabata na rayuwar su ,jikinsa har yayi sanyi sbd wasu abubuwa d ya tuna ,ganin Tana Shirin cin galaba Akan sa kawai y daga Mata hannu !

Ya Isa Haka n gaji d sauraran kalaman ki Basu d guri atare dani kome y faru ke kikaso , nidai inan a safwan Dina dai d Kika sani ,Dan Haka Noor ce kawo wasu maganganu ko?

Bazan barmiki itaba ,bakida Arzikin d Zaki d’auki dawainiyar ta Dan bangaza ba kinfi kowa sani ,y Kama hannun Noor yayi niyar tafiya d ita ,sai NAWAL t kamata itama Kam t durkusar Tana kuka Tana Mai magiya akan y barmata Noor !

Ganin Noor din n kuka itama yasa jikin safwan sanyi y tsaya Amman baida niyar sake Noor din ,ganin baze saketa ba Kuma yaki naam d maganar ta yasa NAWAL Kama hannun safwan din cikin kuka batare d tasan hakan badace ba ……

Jin hannun ta a nashi tsigar jikin shi tabada Yar yaji wani sak’on d ya Dade d manta irin shi ,gashi y kasa kwace hannun sa gata sai kuka takeyi ,can dai yaji baze iya jurewa hakan ba kawai y saki Noor din y yarfar d hannun y raba kansa d NAWAL din ,har ze tafi y juyo y fizgi Noor yayi gaba d ita sukabar NAWAL a durkushe Tana kuka Mai tsuma Rai ….

Shiko jiki b kwari yayi ciki Yana rarashin Noor tanata kuka itama son momynta y Motso Mata ….

Aishatu n ganin su ga Noor anata kuka t taho d sauri t karbi Noor tana tmby shi meya sameta yace ba komai tazo su tafi y mayar d ita gidan Ammy ko su wuce gida !

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button