HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Suna isowa ,suka Fara murna suna d’aukan baby, Bayan sun gama d’aukan baby suka gaisa d su Aishatu d suffaya d ‘yan uwan suffaya d sukazo barka …..

Kusan a gidan suka wuni sai d kyar sukama mazajensu waya sukazo suka daukesu d Alk’awarin zasu dawo kafin suna …..

Mai jego nata samun kulawar ‘yan uwanta d dangin miji ,har akayi suna Mai kayatarwa d akasha shagali yaro yaci sunan Muhammad auwal sunan mahaifin suffaya ,suna kiranshi d Waleed ….

“Wata Rana mlm mamman hafeez suna Hira a shago suna lbr bikin su Saleem , sadeeq yake cemai yauwa ranar muna magana kace na nunama kanin Alhajin mu d baku hadu ba har aka gama bikin d amaren nasan har yau baka taba ganin amaren ba ,tunda b iyali bane dakai d sunkaima ziyara ,Amman kaga kanin Alhj a hoto d amaren!

Mlm mamman hafeez y karba wayar Yana cewa wanan shine Alh karamin? Sadeeq yace eh kasan Saleem shi ya d’ebo kamarsu daya ,mlm yace tabass na hango kamar Nima …

Ya dinga kalon hotunan har yazo hoton d sadeeq y d’auki Amarya d Ango d Aishatu d safwan ,mlm na gama ganin kowa a hoton Yana zuwa Kan Aishatu kirjinsa y bada daram ,gaban shi yayi mumunan fad’uwa yaji idonsa y kafe d kalon Aishatu ,sai sadeeq d y lura d kalon d mlm yakema hoton ,yasa sadeeq Mai bayanin wacan itace amaryar Saleem ,wanan Kuma yayanta ne ,wanan Kuma matarsa ce , abinda ze baka mamaki itace Kuma yarinyar hajiya zainab Mai saran Kaya d take fada Mana ,kasan n fadama mun hadu d ita har mun gaisa d yaranta d take mugun so nawara d Aishatu ,har mun gaisa shi mijinta ku a school senior nane dama nasan shi duk sai a bikin muka Kara had’uwa …

Mlm y dinga mamaki , musamman d idonsa y tsaya Kan Aishatu y rasa y ze yi ,yanajin wani Abu agame d ita y tuno ko y taba ganin t a wani waje ko a saudiya Amman Ina y kasa tunawa Amman fa ,Abin y samu matsuguni a zuciyar ,ga sunan yamai daya d wani suna d baze taba mantawa dashi b Arayuwar sa……

 

Nawara ciki y shiga wata Tara ,haihuwa yau ko gobe , Bayan kwana Tara t haihu ta yaifi yarta mace Mai Kama d ita ,murna wajen dangin mijinta d dangin ta Abin sai Wanda y gani Aishatu anata tafiya d kyar har yau Basu Kara had’uwa d NAWAL ba …

Aishatu kulin Ana gidan nawara Ana suna sauran kwana 3 akayi gidan mama d ita Dan wankan gida ,Aiko Aishatu t Fara cewa itama gidan Inna zatazo wankan gida har t fada safwan yaji ,yace t ma cire aranta suna tare waje daya bazata ta takurama Inna b za’a kawo Mata wacce zata zauna d ita sanan Kuma ,Inna ai Tana tare dasu ,ganin d gaske yake har fushi tayi y dinga lalab’ata Yana aikin rarashi sanan y Sami kanta …..

Aishatu kulin sai anga Inna tunda nawara t koma gida ,Haka ranar suna kwana tayi acan ,harse washe gari suka dawo d ita d Noor ,yarinya taci sunan maman hydar suna kiranta d Mami …..

Aishatu t koma gidanta yanzu ita akasa agaba d cikinta kowa tausayinta yake ,safwan d tace wash! Zece inane? Haka dai taketa lalabawa ….

Wata Rana t tashi d matsanaicin ciwon Mara maramisaltuwa , safwan a rude y dauketa zuwa asibitin kayan baby ko Ammy be gayama b sai aunty zainab ,d sauri tayi asibitin har t had d mlm mamman hafeez a asibitin sunje dubiyar wani abokin Alh su Saleem ,suka hadu d ,hajiya zainab suna gaisawa y ganta a rude ,take sheda Mai Aishatu b lpy harda shi akatafi wajenta besan haihuwa bace ma y manta ance tanada ciki ….

Koda aunty zainab d mlm suka karaso ,safwan d Aishatu ,suna fitowa daga labour room angama dubata antabatar Mai b haihuwa bace juyin ciki ne da wasu matan sukeyi wasu Kuma basa yi ,Aunty zainab d sauri t rungume Aishatu Tana Mata sannu ,likita yazo Yana ma safwan Karin bayani d bashi hakuri ganin yadda rude y fita hayacin sa ,mlm mamman hafeez ko tunda yayi tozali d Aishatu jikinsa y dinga bashi wani Abu ,sai sannu yake Mata duk tausayinta y gama kamashi ,jikin sa yayi sanyi sai y tuno d rasuwar matarsa umaimah sakamakon haihuwar d tazoyi t haifamai ya tilo sanan ita Kuma tabar duniya ,Yar d ayanzu y Gaza gano inda take ,kulin d ita yake kwana yake tashi atake hawaye suka fata bin kumatun sa , Aunty zainab CE t Fara tmby shi lpy yake kuka Kuma?

Cikin tashin hankali yake nuna Mata tausayin Aishatu ne yamai karfi sakamakon tunawa d matar Sa d ta rasu umaimah ta barmai yarsa tilo d besan halin d take ba ko araye ko amace oho ,kulin Addu’a shi ALLAH y bayana Mai ita d marikiyarta ….

Yana Gama bada lbr , Aishatu t d’ago a sukwane t kaleshi sai taji tausayin say gama kamata har safwan d y dawo yaga babban mutum Mai Kamala n kuka sanadin Rashi lpy matar shi !

Safwan d aunty zainab ne suka dinga rarashin shi , Aishatu ko tausayi y hanata furta ko ufan ,atake taji ciwon da yake damunta ya gushe y rabu d ita Dan Haka t Sami karfin gwiwar tausayama wani ….

Saida yayi Mai isarsa ,safwan d aunty zainab suka Fara tmby sa yanzu besan inda suke b besan inda ze samesu b d sun tauashi neman su …

Mlm yace wlh nayi iya nema na n Rasa ganowa ,shekara Ashirin d watanni fa baya shekarun d yawa d a saudiya yake ko shekara beyi d dawowa nageria ba ….

Jikin Aishatu ne yayi mugun sanyi ,can tace ALLAH y bayyana maka su baba ! Cikin kidimewa y juyo Yana kalon Aishatu Yana matuk’ar mamakin yadda muryarta tayi iri daya sak d ta umaimatu matarsa , ko shekaru dari zeyi inyaji muryar umaima zai iya ganewa ,y akayi muryar ki take Kama d ta umaimatu , Aishatu ,…..

Sai kalon kalo y koma ga ,safwan d aunty zainab ,kowa Aishatu d maLam yake kalo…..

Kai wanan Abu ,shifa wlh muryar umaimatu yaji atare d Aishatu , Aishatu t sake firta wace umaima baba nibansanta ba …

Yasake cewa wlh ,inada shaku ,inada ayar tmby ……

Cikin kuka yake basu lbr abinda y faru dashi tun farkon Rayuwar shi har Auren shi d umaima har tijarar d Dan Maliki yamai d sanadin barin shi gari d kasa Baki daya ,har zuwa dawowar shi neman yarsa d marikiyarta har zuwa yanzu d yaketa neman su …..

Aishatu rikicewa tayi Jin wasu kalamai daga mlm , jikin tane ya shiga Bari ,t Rasa nutsuwarta gaba daya ganin yadda jikinta yake rawa ,aunty zainab t zaunar d ita Tana tmby lpy?

D sauri , Aishatu tace a Kira Mata Inna ,safwan y kidime yace sbd me? Cikin kuka d tashin hankali tace Dan ALLAH su Kira Mata Inna ,safwan bashi d zabin d y wuce n zuwa dauko Inna ….

 

D sauri take tuki Yana tunanin dalilin Kiran Inna d Aishatu takeso Ayi ,amnan shi burin shi t sauka lpy shiyisa y tafi d’auko Inna ….

Inna n zuwa ita d safwan ,taji b Wanda takeson gani sai , Aishatu ta jikale ,sai d tazo daidai kusa d mlm mamman hafeez ,tacema safwan Ina indon tawa ? D sauri mlm mamman hafeez y d’ago suka had’a Ido shida Inna ….

 

Inna na katemai kalo ,shima Yana kare Mata kalo ,tabas taso sanin fuskar Amman lokaci be Bata dama b Dan t Indo take ,shima yaso sheda ta ,Amman gani yakeyi kamar kizo idon sa yake Mai ……

 

Inna na zuwa ,inda Aishatu take , Aishatu t kamo Inna Tana kuka ,Inna Dan ALLAH ki gaskata mafarkina ,ki farkar Dani kece Zaki iya warware komai ,inbam manta ba ,Ai sunan mamana umaimatu ko? To sunan mahaifinta fa fadi d bakin ki inkara ji …..

Inna t Fara ridewa ,tace maman hafeez Mana kamar yadda Kika sani ,safwan be fahimci inda Aishatu t sa gaba ba ,aunty zainab ce tafara Gane Kan lbr d sauri t Fara tmby mlm sunan shi nagaskia ,yace sunan shi mamman hafeez Mana ,ta koma t fada ma Inna d safwan d Aishatu ,shima wacan datijon na waje sunan shi mamman hafeez ,idan zargina y tabata shine mahaifin Aishatu kenan ….????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button