KUSKURE Complete Hausa Novel

Safwan cikin yabawa d nuna kulawa ,ya tafi Yana tunanin wanan ai ko b mahaifin Aishatu bane n gaske y zama Dan uwansu ,duk d tashin hankali y hanasu fahimtar hakikanin gaskia ….
Bayan y dawo har anmaida Aishatu d’akin hutu ,babyn na hanun Ammy tabata Mai Addu’a murna d’auke a fuskarta ,sanan taba Inna itama tayi tamai addu’a ,sanan taba aunty zainab ,safwan ji yake kamar y kwace dansa ,Amman hankalin sa y figa Kan Aishatu ….
Har yaron y koma wajen Yaya ,safwan n kusa d Aishatu ya Kura Mata Ido Yana binta d Addu’a…
Y zura yatsun hanun shi cikin nata Yana Mata wani kalon sauki Mai tatare d sanar Mata yanzu na Fara son ki “my happiness ” yaji t matse hanun acikin nata ,d sauri y Kali hanun ya tabatar motsi takeyi dashi ,t bude Ido a hankali Tana kare ma d’akin kalo Tana tuno wasu abubuwa d take zaton duk mafarki ne b gaske ba ,ganin t yunkura zata Mike safwan yayi saurin dakatar d ita yace kibi ahankali CS aka Miki fa duba kikani ,t zaro ido ta shafa d hanun ta tace yaushe? Bazan iya haihuwa d kaina ba?
Muryarta t dawo d su Inna ,Ammy,auny zainab d Yaya wajen ta ,…
Safwan ne yace Mata aa kawai dai kinshiga wani yanayine shiyisa ,Amman Baki d matsalan haihuwa …
D sauri tace wanne yanayi n shiga ,karde duk Abun d nake tunanin mafarkine da gaske y faru?
Ganin inda t dosa ,Inna tace ba wani Abu d y faru inajin dai mafarkin kikayi ,ki hutu ki kwantar d hankalin ki inji Dr …
Safwan yaji dadin bayanin d Inna tayi Mata ,Ammy d Yaya dai sun sasu a duhu …
Aunty zainab ma matsawa tayi kusa d ita Tana kwantar Mata d hankali Tana nuna Mata jaririnta …
Safwan Kiran Ammy d Yaya d Inna yayi awaya Dan karta Gane Bayan y fita ,sukaje suka hadu harda mlm mamman hafeez ,sukayi mgn Akan tunda t d’auka duk Abun d y faru a mafarki ne su d’auka hakan ne zuwa wani lokaci kadan in ankoma gida sayi magana ..
Inna ta bama mlm hakuri akan karya Kara Bari t ganshi harse ranar d za’a hadu Ayi magana ta fahimta Dan tantance gaskia tunda ansha wuya kafin t samu kanta yanzu …
Mlm din y fahimce su shima ji yakeyi kamar yafisu son kwanciyar hankali Aishatu ayanzu ,Dan Haka y musu Alk’awarin kauracema ganin Aishatu harse lokacin d suka dibar Mai ….
Safwan y dafa kafad’ar shi ze bashi hakuri ,mlm yace karka damu Dana ,b komai ,nagode d girmamawa ….
Sanan mlm y musu salama yace zai tafi sai sun kirashi ,sai d yaba kowa tausayi musamman Inna …
Shiko safwan kasa hakuri yayi ji yayi y gama yadda dashi 100% Dan Haka yace Bari y kaishi shagon shi harma y karbi number wayar shi ,suka tafi ,Ammy d Inna d suka koma ciki ,Yaya Kuma y tafi karbo tea flacks d Abinci wajen suffaya…
Suna shigowa , Aishatu t Fara binsu d ita Alamar tmby ,Amman ganin Bata d hurumin tuhumar su sai kawai tayi shiru …
Amy t dinga Mata sannu Tana tmby ta b Abin d t
Yake damun ta? Tace eh Babu sai jinta d takeyi a dadaure musamman cikinta wajen dinki …
Ammy tace ai Dole wanan sai kinyi hakuri ,Zaki danyi jinya ki dinga kula d kanki sosai ,sanan ki Dan dinga kwarara jikinki zakiji sauki d wuri insha ALLAH….
Bayan safwan y dawo ,Ammy t Fara mgn sai iya t dawo t dinga zama dasu ko?
Sai aunty zainab tace laa Ammy anzama dayafa ,ita ai Tana temaka Miki yadda Babu Yan biyu yanzu kina bukatar taimako gashi bakwa rabo d baki,kawai tunda b gida zata ba na zauna d ita tunda b wani nauyi ne Dani ba , kowa yaji dadin kalaman aunty zainab maccen Arziki har Ammy d Inna suka dinga Mata fatan samun miji nagari ,har taji kunya ,sai safwan yace inyaso heedaya t dinga temaka musu d wani Abun ,Ammy tace haka za’ayi ….
Duk masoyan Aishatu sunyi murna d haihuwata ,saidai sun tausaya Mata C’s din d aka Mata ,Amman duba d Mata nawa akayima Kuma gasunan bazakace Anmusu ba ba kanta farau ba bakanta karau ba sai subita da fatan samun lpy kawai …
Makiyanta ko d lbr yaje musu irin su huzna ,d taji a bakin mamanta jitayi kamar ta mutu ,tayi bakin ciki kamar tayi hauka ,kulin d Abin take kwana take tashi ,mama tace t kirasu t musu ALLAH y Raya ,Taki Kira Amman tace t Kira ,ganin Ana suna sauran kwana 4 batace zata b har mama t Fara Mata dayi ,sai tayi karya wai tanada biki ne ,mama t futa harkar ta ..
Bayan an salame Aishatu t koma gida ,Noor murna duk ‘yan school d Yan islamiyar su seda t fada musu aunty t ta samo musu baby boy Mai kyau yafi haneed ma kyau take cewa ….
Su twins Anzo har so 2 wai se sun sake dawowa kafin suna ,nawara d mama duk sun Zo ,Yan uwa d abokan Arziki duk sunzo barka ,safwan b yadda beyi ba a daga shagalin sunan Aishatu tace taji sauki Ayi kawai ,ganin t dage y haukra ,kula kulin cikin Bata yake ita d baby ,damma Yana kunyar aunty zainab ne da wuni ze dingayi a gidan ….
Y nemi shawarar Aishatu wane suna za’a sama baby Dan y Bata hakinta amatsayinta n uwa ,sai tace Mai ita Haneef ta Haifa harda guntun hawayenta …..
Ganin irin karamci d halaci d nuna kulawar d mlm mamman hafeez y Basu shida matar shi ga hakikanin gaskia d yake hangowa atare dashi ,kawai y gama sadakarwa ko b mahaifin Aishatu bane y saka sunan shi Dan Haka yace Mata sunan yaron shi hafeez Amman ya amince a dinga Kiran shi d haneef ,zata Mai tmby yace my happiness Banda tmby nabi naki kema kibi nawa kawai!
Tace to dadyn Noor komai kayi daidai ne ,tamai “salute”ta Sara Mai ,yasa dariya y rungumota Yana sake murnar Dace d macce Mai bin umarni d NAWAL ce ko zatabi sai ankai ruwa Rana kafin ,Dan Haka y sake Amincewa d Aishatu …..
Safwan cikin kula d junior Haneef d maman shi yake Naman gashi d su balangu kaza gashin Romo d gashin ruwan kulikuli d farfesun kulin cikin jibgama Mai jego yakeyi ,t ko Ina be rageta b y jibgo Mata su Madara kayan tea dai komai Akwai wai babyn y samu Abinci ….
Tana kula d kanta d taimakon aunty zainab ,Dan Babu Wasa ,Kuma Tana samun lpy…
Safwan Yana zuwa wajen mlm su gaisa ,Kuma Yana Kiran shi a waya har y Kara bashi hakuri Akan Subaru zuwa Bayan suna sai su tatauna maganarnan Mai mahimmanci ,mlm yace dama shima Haka yace ….
Safwan yaje y Sami inna y sanar Mata yadda sukayi d mlm ,tace ba komai hakan yayi kyau ,yanata b Inna hakuri Aishatu batazo wankan gida ba ,Inna tace b komai ,tunda Akwai Mai kula d ita karya damu ,yace y gode Amman ai insunyi 40 zatazo tayi sati a gidan inba tace b komai …yaba Inna kudi d kayan Abinci harda kaya y dinko Mata kusan kala 5 har take tsokanar shi itama Ashe jego takeyi ,yace eh Mana itace me jegon asalin ai shiyisa be manta d ita ba ,suka dinga dariya har y tafi ….
Me jego Tasha Kaya dinkaku d Wanda ba’a dinka ba ,hatta aunty zainab kusan kala 4 safwan y dinka Mata masu kyau ,har heedaya t samu kala 3 masu kyau baby d Noor ma sunsha Yan kanti masu tsada ,har Ammy sai d Yama dinkuna kusan kala 5 y gwangwaje mutane d farin ciki d dama yasha addu’a kuwa …
Abinci suna komai order aka bayar ,ba Abin d zasuyi sai suyan kayan ciki Dan sa d raguna biyu ze yanka …..
Ana gobe suna gidan acike d mutane har aunty balaraba ta k’araso ,sunata Hira d safwan su twins ma suna gidan su nawara ma d heedaya anata Hira kamar Kar arabu ,sai wajen 10 mijin nawara yazo y dauketa su twins ko kwana zasuyi Dan sangarta Aiko d safwan yaji sunsha fada kamar y mayar dasu haka yaji ,har Ammy ma d taji sunsha fada shiyisa sukaki kwana gidan Ammy ,itako aunty balaraba bada motar ta tazo ba ,safwan ne y kaita gidan Ammy ,bayadda beyi ba d ita t kwana gidan shi Sam Taki yadda ,Aiko Saida y sai Mata fruit d su tsire Mai dad’i ahanya sanan y karasa d ita gidan Ammy ,har suka Kara tataunawa agame d shagalin suna Ammy tace Bata bukatar komai ,be bar gidan Ammy b sai 11:pm y shigo gida y samu su twins d heedaya anata shewa d Hira sunga baya gidan sun samu sake ….