KUSKURE Complete Hausa Novel

Inna t Fara Mai nasiha d yayi Aure Dan samun Nutsuwa d kwanciyar hankali d iyali nagari ….
Shidai sai murmushi yakeyi ,suna cikin Hira aunty zainab tayi sallama t shigo batasan yazo bama tayi kwaliya tayi Ado tayi kyau dake juma’a ce ranar ,Koda y kaketa y amsa salamar sai taji wani matsanaicin kunya y ratsata ,Inna t Mata iso t shigo …
Mlm nata kalonta Yana murmushi ,Inna n lura dasu sosai ,har tace musu ALLAH y tabatar Mana d Abin d yake Alkhairi ,gaba daya sukaji nauyin Inna suka kasa amsa Amin din sai ita t amsa Inna har d’akin t barmusu ….
Sun Sha Hira sama sama aunty zainab nata jin kunyar mlm d nauyi ,shiko y Dan sake dake namiji ne ,kodan Aishatu yaci ace yasota kaso me son naka ,matar d tun besan yarsa ba yasan son d takema jinin sa karshe kusan itace sillar sanadin had’uwa d gudan jinin sa,Kai baida matar aurema sai ita Amman d yarsa ze Fara shawara yaji kafin …..
Aishatu ,nata nunama mijinta kulawa d dansu d yarsu Noor Mahaifinta kuwa shima kulin cikin waya d nuna kulawarsa agareta yake g Kaya d yake jikasu d shi ita d Noor ko yaran larabawa sai Haka ,gashi kulin cikin tmby t kotanada matsala t kudi ko wani Abu ashirye yake Dan yaye Mata damuwarta indai befi karfin Shiba ,Dan Haka takejin b wata mecce a duniya Mai gata kamarta t samu gata kashi Kashi t Miji t uba t Kaka gata ‘Yan uwanmiji d jama’ar gari makiyanta ko Bata tasu Sam bare su dameta …..
Cikin kwanciyar hankali take Shan Kan safwan t salonta d dabarunta na kwarariya agun mijinta ,Tana kula d kanta sosai Dan har mamaki nawara take akan yadda Aishatu tasan takan iya sarafa miji Haka ,aunty zainab m n Bata wasu sirrikan har nawaran ma ,sosai suke bin mazajen su d nunamusu kulawa d kaunar juna ….
NAWAL n takurama safwan d chart ,magiya d kalamai masu son sa shi karaya ,kariyar son Aishatu Mai karfi d take sake samun matsuguni a zuciyar sa kulin cikin nunamai sabon salon kulawa take ,uwa uba biyaya inyace yi sai tayi inyace Bari sai t Bari ,yanzu mgn karatun t tunda y umarci d t yi hakuri harse t haihu tanason karatun Amman Haka t hakura Dan biyaya y ji Dadi ayanzu y shirya Mata komai ma n cigaban karatun Bata tunda t sauka lpy har ansami wata Yar uwar iya kakar heedaya t Nemo musu wata datijuwa d zata dinga kula d haneef a makaranta Dan tare zasu dinga tafi d Aishatu komai y Kamala yau y Gaya Mata ,murna d Addu’a seda yaji Dadi matuk’ar Dadi ,t dinga farin ciki on Monday zata Fara zuwa d ze dinga kaisu d Noor ita Kuma baban zata dinga zuwa Tana samun su a makarantar ……
Komai Yana tafiya yadda akeso ,NAWAL naci tanata fama d safwan shide bangaren shi baya wani kulata Kuma bayaso Aishatu tasan me ake ciki duk d Yana tunanin bashi d matsala d ita Amman yayi imanin zata iya nuna kishi duba d so d kulawar d take bashi ,to bayason wata matsala t gifto cikin zaman su Dan Haka yake goge chart din Dan y blacking d’inta t sake biyoshi d wata number ……
Ita Kuma sai wasu abubuwa takemai ,yau harda Kiran waya ta dinga Mai magiya d rarashi d ban hakuri akan y maida ita dakinta t Gane *KUSKURE* y zama lbr insha ALLAH ,y talafi soyayar su shida ita Kar y zama butulu y Mata halaci y auna irin son d takemai y sani tanason shi so tsantsar so ,y Mata Alkalanci harda kuka tayi tayi yayi magana Akan taji t bakin shi yaki cewa komai ,d ta dameshi yace ze duba y gani t dinga Mai magiya Tana had’awa d yarsu Noor har Haneef d y rasu duk t karyar Mai d zuciya harse d yaji tausayinta ,ganin karya furta Abin d beze yiwu ba y kashe wayar ……
A washe garin ranar y ji Kiran wayar Abban NAWAL ,seda hankalin shi y tashi,d yaso kin zuwa Amman ganin rashin girmama babba b dabi’arsa bace kawai y hak’ura yace zeje ,Amman yasan tatsuniyar gizo Bata wuce t koki ,yasan maganar NAWAL ce ,Dan Haka seda yayi shawara d Ammy d Yaya kafin ,Ammy dai t bashi umarnin girmama nagaba akodayaushe ,sanan Mata Kuma shiyafi sanin wacece NAWAL ,yayi abinda yake ganin baze maimaita karatun baya ba ,ya Gane manufarta atunanin t haryanzu yanason NAWAL Dan Haka Bata bashi shawarar kin Amincewa ba …
Shidai Yaya cemai yayi ,inyaga b matsala to ,Amman fa y sani me Hali baya fasa halinsa ,wani Kuma yakan canja ,Amman y kasance adali baiwar ALLAH Nan Aishatu Yar halak ce t cancanci azauna d ita ita kad’ai har wani lokaci duk d basunan yin ALLAH ba ,Amman fa yayi abinda y Dace Kar tsoro ko ganin girma ko tuno wani Abu d ya wuce yasa kayi yunkurin aikata Abin d ze dameka y damemu ,kadai fahimta ,duk safwan y fahimce su sosai….
Bayan safwan y Isa gidan su NAWAL ,mama tamai tarba Mai kyau NAWAL anci kwaliya ta kece sa’a ,anata wani murmushi d kalon so d tatali tun zuwan safwan har wani mgn d ido take Mai ,shiko ko kalon kwayar idon ta bayason yi ,hankalin shi n gida wajen Aishatu d yaranta duk wai Dan ya karfafama kanshi gwuwa Kar y samu tazgado NAWAL din taci nasara akanshi …
Har Abba y umarce d takaishi parlour Baki ,ba Wanda y Bata umarni t cikamai gaban shi d kayan motsa Baki , ganin yaki Mata mgn t Fara janshi d Hira Yana amsa Mata sama sama ,Tana cewa Dan ALLAH y saving life d’inta ayau karya juya Mata baya ,badan itaba badan *KUSKURE* d ta aikata a baya b y fuskanci rayuwa Mai cike d anushiwa d zasu samu anan gaba shi d ita ,yayi murmushin takaici yace ke ai cikin *KUSKURE* kike sake aikata *KUSKURE* bakya lura ,Bata gama Gane mgn Shiba ,amman tace insha ALLAH anyi final …..
Yace ,hmmmm da kanki Zaki wargaza komai ….
Sai ga Abba y shigo Bayan dogon milki d y zauna yi,cikin girmamawa safwan y gashe shi ….
Bayan gaisawa ,NAWAL nata sunkuyar d Kai tunani nata adabarta Dan sanin makomarta komawa gidan safwan ko Auren faruq??
Abbanta yayi gyaran murya yace ,safwan n kirakane Don mgn t fahimta d Kai ,Akan NAWAL duk d aka’ida Kai y kamata kabimu b mubika ba ,duk d Haka yanzu b binka mukayi ba ,Albaekacin yarka Kuma yarta mukuma jikarmu mukeson gyara zamanku d ita uwar ‘yar ,nace meye shawarar ka akai?
SFwan ji yayi kamar andora Mai wani nanauyan Abu andanne shi ,Yama kasa cewa komai …
NAWAL dagowa tayi idonta y ciciko jiran amsar sa take t rushe d kuka ,Tana Mai wani irin kaltaa daA baze manta d irin kalon ba Dan y gama tunowa dashi sosai ,ganin Taki d’auke nata idon ,shi sai y d’auke idon shi yace….
Abba Ina bukatar shawara tukunna ,karna yanke hukunci …..
Abba katse shi, yace safwan kaikeda komai a hanun kafa ,amsace daya tal eh ko aa …
NAWAL t sake kalon shi ,Tana Mai magiya d idanu …
Safwan y sake cewa ai bawai ban amince bane Abba ,kawai dai zan Kara shawara ne …
Abba yace kadai amince d komawar gidanka ? Safwan baida zabi sunmai yawa g wani kwarjinin Abba ,duk Yama Rasa yadda zeyi ,ga wayarshi n ringing Aishatu n Kiran shi a waya Nanda Nan y rikice kamar Mara gaskia har wayar t katse ,Dan Haka besan lokacin d y amsama Abban NAWAL d eh y amince ba ….
NAWAL d sauri d murna t juyo tana kalon safwan ,shiko burin shi y Mike y tafi sun hanashi ,Dan Haka y Mike ,Abba d NAWAL suka dawo dashi t hanyar ai ba’a Gama magana ba ,kira mamanki ,d sauri t tafi Tana murna watan zayano dokarta t Kama dake tunanin NAWAL ragage ne …
Bayan sun shigo d mama ,shiko safwan kamar jikaken tsumma y koma y zauna ….