KUSKURE Complete Hausa Novel

Aunty zainab tace haka zakace ma ko? Tace safwan bantaba saka Bayan da ba tun lokacin d n shirya Auren mlm har gobe Kuma Abu daya kuke agareni kai da Aishatu,so baka d matsala Ina tare daku har abada insha ALLAH !
Mgn Tama kowa Dadi sosai ,sunsha Hira Abba d aunty zainab sun saki jiki daga baya ,sunci iya abinda cikin su ze d’auka Noor nata musu Hira ,daga baya mlm yace to mufa zamu gudu ,safwan yace Kai Abba tun yanzu ?
Mlm yace bakaga matar mutane a waje b y kamata t koma gida ,wato aunty zainab ,duk sukasa dariya , Aishatu tace nagode Abbana tun yanzu munsan zakabamu kulawa ta mussaman muda mamanmu aunty zainab,Tana Dan rungume shi ,shima yanakara jin son y’arsa inama y rayu d ita d taga shakuwa d kulawa ,Amman yanzun ma yanakai bataga komai ba insha ALLAH!
Sanan t rungume aunty zainab tanajin Dadi …..
Safwan ne yace to Abba tunda k matsa Bari muje mu ajiyeku …
Mlm yace aa kuyi zamanku ,zan kaita har gida kafin natafi wajen kwanana Nima ….
Safwan yace Sam su zasu kaisu ,har gida Dan hankalin su seyafi kwanciya Kuma hakan shine girmamawa Dan ALLAH Abba karya ce komai ,bashi d zabin d y wuce to muje Yan Albarka ,sukasa dariya y dauko makulin mota , Aishatu t d’auko gyalen ta t rungume Haneef aunty zainab t Kama hanun Noor suka fita cike d nishad’i…..
Safwan na tuki Abba n zaune a kusa dashi Aishatu d aunty zainab d Noor suna baya ,mlm nata tsokanar Noor wai matar ,safwan nacewa Kar anty zainab t tatosheta a baya fa taji ka Kira Noor d matar ,anata dariya sunata Raha cikin farin cikin suka Fara sauke aunty zainab a gida sunata Mata godia d fatan Alkhairi ….
sanan sukaje suka sauke mlm a gida sunata Mai godia ..
Suma suka dawo gida ,cike d nishad’i ,yau kwanan farinciki Aishatu tayi Bata boyema safwan b seda t gayamai yau yasa ta ciki farinciki maramisaltuwa ta gode ,yace ba komai aikin shine ai ,yace Nima sai aramamin ko ? Tace kwantar d hankalin ka kamar kayi matashin Kai d gawa Tana dariya …
Y zaro ido ,Ashe ko b lpy ,Ina kwanciyar hankali kayi filo d gawa ,ranar dai kwanan nishad’i sukayi ….
**********
Faruq sun gama mgn d Abban NAWAL ,har Abba y Mai izini zuwa y yanke wata daya kacal ze auramai ita duk yayi binciken shi acewar shi Babu abinda ze tsaya jira …
Lokacin d taji anbada ita wata daya kacal tayi kuka kamar ranta ze fita ,mamace kawai take rarashin t d kwantar Mata d hankali yanzu Abban y Dena sonta acewarta gashi Bata ganin fara’a sa ,Dan Haka takeson tayi hakuri t amince ko ya dawo kamar da y dinga Mata dariya ….
Bayan sun Hadi d su ,docass ,t labarta musu irin tsaka Mai wuyan d t shiga ,suka dinga Bata gurguwar shawara ,lawy Ce kawai t Bata t Arziki t nuna Mata amfanin bin mgn iyaye d hakuri t nuna Mata amfanin Auren faruq sanan tadau shawarar lawy tayi watsi d tasauran ….
Mama kulin cikin nasiha d Jan kunne takema NAWAL ,yanzu NAWAL Bata samun sasauci wajen kowa se mama ,safwan d Indo kuwa Jitake kamar t harbe su ,dande mama Tana cemata t manta dasune kawai Kuma t fuskanci hakan shi zesa t samu sasauci a zuciyar ta d kulin dasu zata kwanta takuma tashi …
Zuwan faruq ,wajen NAWAL n farko ,Yana daga kujera nesa d ita itama tana daga kujera nesa dashi tanata cika Tana batsewa ko kwaliya babu bare turare ,shiko be damu b ze d’auki bazawara sakin Wawa d’aukan me wayo acewar shi burin shi t shigo kawai ….
Sai fara’a yakeyi gakora kamar gonar Kashi tsabar fara’a ,yanata lalab’ata Yana bayana Mata irin son d yake Mata d irin kulawar d dadin d ze jiyar d ita inta shigo gidan shi ,wai harda cewa y sa matarshi tsayar d haihuwata harse NAWAL tashigo tukunna tayi daya sanan ,intanaso su jera sai su jera …
Jin Haka ,yasa NAWAL Jin sanyi kadan a ranta Tana cewa inama furucin Nan daga bakin safwan suke fitowa? D tayi tsale d murna t samu ‘yanci d dama ,Amman Inna ,can Kuma tace wayace zan sakijiki danaje n Fara zubo yara kamar wata gyada sai Naga kamun ludayin tukunna ….
Yanata Mata Hira ,tanata karemai kalo ,tabass faruq kyakyawa ne ,Amman bekai safwan d’inta ba ,Amman shima y hadu gashi d Arziki ,gashi tun yanzu y Fara Mata Alk’awarin sabuwar mota ,Bari tayi manaji kawai ,suka Dan Fara Hira sama sama ,d ze tafi y Bata kudi masu kauri ba godia b karba sai ajiye Mata yayi Akan cinyarta ,yace sai yaushe ze dawo tace ko yaushe y karbi wayarta y shigar Mata d number shi y Kira wayar shi y d’auki tata number yayi saving atake y Mata vtu ,taji Aleart n credit …..
Yamata salama yanata murna ,itako ko fara’ar babu ,Amman Tana jinjinama Arzikin shi …..
NAWAL ta kasa samun sukuni tun Bayan tafiyan faruq y addabeta d waya ,ga tunanin shi d na safwan sun addabeta Suma …..
“Gidan Faruq ko y Rasa yadda zegayama huzzara mgn Aure d ze Kara yasan bala’in ta ,Dan Haka y dinga rara gefe temakon shi daya d NAWAL Bata Kiran shi sbd girman kanta tafi karfin t kirashi sede y kirata ,shiyisa matar Bata sani ba ,Amman t Fara jiyo warin Abun …
Bikin NAWAL saura sati biyu ,faruq b yadda zeyi Dole y Fara lalab’a huzzara Yana Mata Alkawarori Akan Anbashi Mata , shi da bekarba ba ,seda yaji shahadar d yake cikin Auren sanan Yar abokin n dadyn su ce Dan ALLAH karta daga hankalinta tasan Yana sonta t Fadi duk abinda takeso ze Mata komeye shi ….
Aiko , huzzara tayi kanshi d masifa d ruwan bala’e ,ganin seyayi da gaske Dan sun Saba ita wuta shi ruwa ,wani lokacin Kuma shine wutar itace ruwan ,ganin zata taramai mutane gashi jiyake Auren Nan ko aboyene seyayi babu fashi kawai ya Fara Mata borin kunya d masifar shi d tafi tata Dole t hakura tasan ruwan bala’en shi yafi nata ,Dan Haka Kuka tasa kawai ,ganin tayi ladab Dan tabari Ayi cikin lumana y Fara Mata Alkawarori Yana kwantar Mata d hankali harseda y samo kanta sanan ,Amman f ranta babu Dadi ….
Ya Mata Alk’awarin tafiya Dubai hutawa ,yace setaje ma t dawo sanan ze dauki Amarya Suma suje ….
Zatayi masifa Akan hartare zasu d Amarya …..yace haba ke so nawa muna zuwa tare? Kuma sbd n Baki kima d girma nace sekinje kindawo fa sanan zamu d naso kinsan cewa zanyi Dole ki Bari muje mu dawo kafin ke je,Kuma kin San Babu abinda ze faru ,sanan huzzara taji sasauci kanta y kumbura angirmamata ,Mata bamu da wayo wani kacin ,Amman f wasu matan ….
NAWAL kulin faruq cikin makale Mata yake a waya ganin har yanzu d sauranta gashi y samu y shawo Kan matar shi d kyar ,y Fara labartama NAWAL ai Kora matar zeyi lokacin d zasu tare yaran ma ziyara ze kaisu 2weeks zasuyi suna kwasan amarci sanan ,sati biyu masu zuwa d biki su tafi Dubai yawan bude ido shida ita ,NAWAL Jin za’aje Dubai duk d tasan Akwai kashe d sukafi Dubai ,Kuma tanason zuwa yawon bude Ido aljihuntane Bai Kai b se kawai ta hakura wai Bari tayi maneji d Dubai din ,tayi murna first time in history zata fita waje ,sai tafarajin son Auren faruq din tashi insun dawo ze Bata sabuwar mota ,duniya sabuwa a wajenta zata yaga kowa son ranta ….
Biki saura sati daya ,Abbanta y Fara sakowa ganin Tana farin ciki kadan d Auren ,mama dai Addu’a taketa bin Yar tata dashi …..
Faruq y kawo akwatunan Auren ko budurwa iyakaci Kaya masu tsada d ita sukaje suka siyo komai ,Yan uwa duk sunzo ganin akwatunan masu addu’a nayi masu gulma nayi ……
*Wash*!……….. ????????♀