KUSKURE Complete Hausa Novel

Abban NAWAL yace ai Bata Gaya Miki b ,wai yaji tayo Nan dake Abin yadawa agari gaba t bashi b baya ba ,daga Aure so take t dawo gida t samu yaro Dan mutunci bakiga yadda yake girmamani ba ,shine takeson watsamin kasa a Ido a gabansa ,yanzu duk n Gane ko gidan tsohon mijinta itace d lefi komai yace tayi hakane n yadda yanzu…
Mama tace ai dama babu ja ,yadda ne bakayi ba , Abban yace yanzu ai n yadda ,y kwashe duk kyaryar d Faruq y gayamai d gaskia y fadama mama ,suka dinga yi Mata fada suna komawa gidan mijinta farillane a wajenta sanan biyaya ma dolene ,meye dangidan su daya d matar sa kowa d sashin sa ,Dan Haka karsu karajin makamancin irin shirmen Nan …
NAWAL Bata d magoyin baya ,kuka t fashe musu dashi mussaman d Faruq yayi sallama y shigo y dinga sunkuyar d kyar shiga surikin kirki ,taci kuka t k’oshi Abba d mama nata Mata fada ,daga karshe mama t ma faruq din nasiha d tsoron ALLAH cikin zaman NAWAL d abokiyar zamanta ,Abba y bashi NAWAL suka juya NAWAL kamar tayi bindiga ……..
Cikin mota ,faruq nata rarashin Amarya NAWAL ko t kulashi ,Haka y hak’ura suka karasa gida Bayan sun Isa sun shiga parlour,tayi saurin wucewa dakinta t Danna key…..yin duniya Taki budemai g bukata na adabar jatabus ……
NAWAL Bata fitoba sai d yunwa t Fara Shirin kaita inda Bata shirya ba ,sanan t fito don kaima d’akin girki ziyarar gagawa Kai t bakunci lahira ….
Yana ganin t fito har yayi bacci y tashi ,y watsa Mata murmushi d yake Wanda yafi kuka ciwo y zata kodan shi t fito ,ganin t nufi d’akin girki ,shima y bita y rungumo ta tabaya ,t kwace ka kyaleni me hada mutum d iyayensa kawai …
Y sake rungumeta yace wlh ban hadaki dasu b ,sonki d kaunar kine y janyo min Haka kimin aikin gafara amaryata mu samu mu shirya tafiyar honeymoon din mu Cikin farin ciki d juna ….tad’an ji sanyi a ranta kadan Amman ta danne ,tace Ni k kyaleni naci Abinci yunwa nakeji ….
Yace sorry me kikeso n tayaki girkawa ? Ta Fara hada girkin t Mai sauki Tana hararar shi Yana tayata har suka Kamala ,wajen CI ma iya nata t zuba t bar sauran a tukunya ko Arziki zubama oga ko t Adana a Abin Adana Abinci be samu Arzikin hakan b ….
Shiko ,sai Bata yakeyi a Baki badan tanaso ba Dan gani takeyi kamar yanga ko jamata Rai yakeyi itako yunwa takeji t barmai cokalin t sa hanun t Fara ci kawai ganin kamar zata hada d hanun t y fuskanci yunwace t korota y kyaleta y dinga b cikin shi tanata bashi alakoron harara ,har suka cinye shi yaje y Karo musu Ashe shima yunwar na cunkushe a cikin shi ,d kamar bazataci b daga baya t Kara kadan t tashi t koma gefe t Fara waya d kawarta daga baya suka koma chart …..
Shiko bukatar maje hajji sallah ,y sidada kamar kwarto y Fara Mata wasu salo d kalamai masu damke zuciyar iya Wanda akayima ,seda y cimma burin shi sanan y rabu d ita ,uwargida nata Kira t Kira y kusan so 8 Amman bemasan tanayi ba ,seda y gama bukatar say faki idon NAWAL yaje tsarata karya d gaskia d tadau fishi Amman Dole t sako ganin yadda yake labarta Mata yadda yayi missing d’inta ….
Haka faruq d NAWAL aka dinga hakuri d junna mussaman ita Dan itace me hakuri dashi sosai aganin ta , ganin Babu sauki cikin lamarin faruq ga hango fantamawa d Jin Dadi d takeyi shiyasa t Fara hakurin Dole Dan t samu ko takerema sa’a Akwai yawan bude ido agabanta g daleliyar mota Dan Haka taketa hakuri d Faruq….
Yau kwanan su goma sha biyu d aure jibi Kuma uwar gida zata dawo su kuma zasu bar kasar washegari shida NAWAL…..
Yau uwar gida zata dawo yaranta Kuma jibi zasu dawo …
Uwar gida t dawo kasar ta t haihuwa lpy ,tare d samun tarban megidanta d yaje Airport y daukota cikin nuna damuwa d lamarinta har y kawota gida ya Mata rakiya har part dinta Yana Mata sannu d hanya g uwar munafukar kulawa d yake Bata t musamman …..
Y Jima a part dinta kafin y CE mata Bari y leka Amarya inta yarda kafin sai y wuce masalaci ,jin anbata girma taji Dadi kanta y kumbura tace b matsala inya dawo Amman y leko ,y ce to sai n dawo y tafi wajen Amaryar ……maza ! Maza!! Mutanen mu….
Yana shiga y samu NAWAL anata cika Ana batsewa Ashe t hango shi lokacin d suka dawo d huzzara Aiko ,t Fara cewa Dan munafurci shine ko y gayamata inda zashi ?
Y talabota y Fara rarashi d Bata Baki Yana ,inbe daukota b y xa’ayi su gaisa kafin subar gari ,tafa sani gobe jirgin su ze daga shida ita Dan Haka t tashi t Fara hada musu duk wani Abun bukata kafin yaje sallah y dawo ,jin y nuna Mata irin ita kadaice agaban shi shine t Mike t tafi hada musu kayan tafiya honeymoon kamar yadda yake cemata …..
Bayan y dawo dg sallah y wuce part din uwar gida ,y dinga tsokanar ta Ina tsarabar sa ,yanata nuna missing d’inta d yaranta d yayi ,sanan take cemai Amman yau kwanan tane ko?
Ya Fara Bata hak’uri Kan t hakura yau daya dai tal ,sbd gobe zasu tafi d Amarya ,shi ba wani son tafiyar yake ba ,amman y Riga y kashe kudi karyayi asara shiyisa ze hakura yaje ,Amman tayi hakuri insun dawo ze tsara komai befi suyi sati bama ,uwargida sarautat Mata ai inatare dake kinfi kowa sani y dinga fasa Mata Kai ,har y samu y Samu kanta ,Amman badan taso b t hakura gobe zasu wuce d Amarya ko Bari yaran shi su dawo m beyi ba ….
Seda y gama lalab’ata y samu y fice Yana Mata zancen t huta kafin y dawo …..
Y dawo wajen Amarya ,kafin tace y Jima t tuhume shi y Fara Mata cakulkuli Yana tmby Ina kayan nasu gone d safe xasu daga fa ,dafatan tayima kowa sallama dai ko har su mama ….
T yamutsa fuska ,au ko zuwa muyi musu sallama ma bazamu samu dama ba? Kodan uwar gidan ka t dawo? Yace aa karta Fadi Haka to meye aciki Dan t dawo b tsalaketa zanyi n tati dake b kike wani shirme ?
Sai t tuna Kuma fa hakane ….
Be koma d’akin uwar gida b sai Bayan isha’i ,sai d y samu y lalab’ata y dinga Mata wasu kalamai n karya d gaskia sanan y samu y fito d kyar y gudu d’akin Amarya . ..
Yana shiga kafin tayi korafi y samu y shawo kanta ,suka kwanta Bayan sun gama duk wani shiri ,itama NAWAL through chart angama mgn d friends zatabar kasa zata honeymoon d oga ,masu gulma d Bata sonshi nayi masu Mata murna n yi ,su mama d Abba m suka Mata Addu’ar tafiya lpy ,Abba nata farin ciki t Fara kwantar d hankalin t ,mama ko Addu’a shiriya take karayi Mata …..
Washe gari d kyar faruq y tursasa NAWAL taje Tama uwargida sannu d dawowa d sallama ,seda taga ranta ze baci tukunna ,suka tafi tare ,huzzara b wani yanayi atare d ita t karbi NAWAL suka gaisa ,NAWAL t Mata sannu d zuwa ,itama t musu fatan tafiya lpy kowa taciki naciki Dan faruq yanata musu mugun gargadi cikin Ido yake aika musu d sakon, har suka mata salama ….
Faruq y sake komawa y dinga nuna ma uwar gida yadda zeyi rashinta y Bata kudade idan yaran shi sun dawo a musu yadda sukeso Yana missing dinsu Amman ze dawo garesu ,ranta n kuna Tana gani y tafi d Amarya …..
Itako NAWAL sai wani feleke akeyi yanasa kafa yabar gidan y zama n NAWAL ……
Sun sauka lpy a kasar Dubai a wani hotel ,NAWAL sai wani wulakanci da Rai akeyi kamar a 9ja ,shiko sai wani like Mata yakeyi …..
Sai can y Kira Aishatu uwargida y sanar Mata sun sauka ,yanata Kara cushe Mata kunne d karya d gaskia ,sanan y Kira iyayen shi sukayi mgn Kan yaran nashi suna hanya sunma kusa Isa gida ….