HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

“Huzna kuwa ta Sami Kiran gagawa daga gdn su haka ta tatara ta koma batare da ta gama cika burin ta ba ,amman ta k’udiri aniyar dawowa Nan kusa”

Su Noor ko dama sun Kara zama yaran Indo , tun tashin su d safe ita take zama dasu har sai momyn su ta dawo ko ta dawo ma Indo Ce koman su …

 

Indo hak’uri kawai takeyi ,Dan ma Inna na rarashin ta ,sanan hadiya ma n Bata hak’uri Kan ta cigaba da hak’uri wata Rana sai labari har ta samu ta cika burikan ta guda biyu…..

************
*WACE CE INDO*❓
“Aishatu wacce aka fi sani da Indo ‘ya ce ga Hafiz mamman ,ita kad’ai Allah yaba su shida matar shi Umaima ,

K’auna ce mai tsafta da inganci tsakanin sa da umaima , suna nunama junan su kulawa sosai Hafiz beyi nisa a karatun shi n Boko ba daga sakandiri be Kara ko Ina ba shima d kyar y samu y Kamala ,saka makon tasowa da yayi a hannun kishiya maman SA “Amman ya Sami na addini har matakin sauke Al’Qur’ani da wasu litattafan, ya azabtu a wajen ta iya azabtuwa gashi baban shi bashi d kata bus sai Abin da tace Mai ..

A haka da Dadi ba Dadi har ya samu y auri umaima har Allah y azurtasu da samun Aishatu , mahaifin sa na son sa Amman baya nunawa agaban kishiyar uwar sa saidai abayan idon ta ..

Haka rayuwa Taita musu tsanani dama b wata sana’ace dashi ba jiran shago na provision yake, gashi ba wani sallamar kirki ake Mai ba ,hakuri kawai yakeyi Dan ma aihuwa t tsaya musu tun haihuwar Aishatu …

bame temaka Masa a garin ,Inna mahaifiyar umaima itace kawai take temakon su dame Tana saida kayan kule kule irin na Mata acikin gida ..

 

Shekarar Aishatu biyar aduniya ,umaima ko Bari Bata sakeyi ba ,

A cikin shekarar ne , Allah y Aiko ma da umaima jinya wacce aka rasa kanta ,Dan daga baya ma tun Ana zuwa asibiti har hakura akayi aka dawo da ita gidan Inna ta Dan jinya ,hankalin Hafiz mamman in yayi dubu ya tashi , magani yakeyi daidai karfin sa Amman Ina Saida cutar Nan takai umaima kushewar ta Allah y karbi Rayuwar ta ….

tashin hankali da kid’ima d shiga rud’u Inna da Hafiz mamman sun shiga Dan su akama mutuwa , yaci kuka kamar ransa ze fita .

Inama taci kuka kamar me Dan itama ita kad’ai Allah y Bata sai Aishatu da Allah y Bata a matsayin jika ..

Ana cikin wanan tashin hankalin Bayan sati biyu da rasuwar umaima ,barayi Wanda ake tunanin turo su akayi suka fasa shagon da Hafiz yake jira sukayi sata …

Da gari ya waye kuwa gari ya d’auka ,wai talauci yasa Hafiz ya fasa shagon Dan Maliki ya kwashe Mai kaya , wasu d dama sun San k’age akemai wasu ko sun yadda ..

Da safe Dan Maliki yazo y dinga surfama Hafiz masifa wai ko y fitomai da kayan shagon sa ko yayi prison ,Kuma ansan shi fagen rashin MUTUNCI tasa zai aikata ..

Ganin y tafi ,yasa Hafiz yaje gdn Inna yanata Bata hak’uri Kan ta rike Aisha ya barmata har abada shi tashi t kare baida kudin biyan kayan ,Kuma duk garin Bamai biya Mai kud’in ,ko yayi zaman gidan yarin ko ya gudu ya bar garin ,acikin biyu dai za’ayi d’aya …..cikin kuka suka rabu shida Inna d ‘yar shi tilo Aishatu.

Ana haka ,mahaifin hafiz hawan jinin shi y tashi sakamakon sharin da akama d’ansa Hafiz ,Aiko tuni shima Rai yayi halin sa ,sanadin sharin.

Hafiz Yama rasa yadda zeyi Banda kuka ba Abin da yakeyi ..

Anata zaman makoki , ranar sadakan uku Dan Maliki ya kwaso tawagar ‘yan sanda har su 5 anzo tafiya da Hafiz …

Aiko abokin Hafiz nuhu ya Zo y Gaya Mai a kunne batare d kowa yaji ko ya gani ba ..

Atake aka nemi Hafiz aka rasa ya gudu guduwar da shima besan inda zashi ba gudun ceton Rai …

 

Ko da sukazo ,haka aka dinga neman shi babu shi babu lbr Hafiz ,har gdn Inna sukaje suka d’aga Mata hankali ta dinga kuka ,manyan garine suka ba Dan Maliki hakuri da kyar y hakura Amman yace idon shi idon Hafiz wlh sai ya ziyarci gdn maza (prison)

Haka Inna tashiga tashin hankali ,itako Aishatu nada shekara 5 Bata ma San rayuwa ba, Amman ta San baban ta Dan ko lokacin d mahaifiyar ta ta rasu taci kuka Amman daga baya ta ma manta tun Tana tambayar ina take har t daina ..

Yanzuma haka kulin cikin tmby Inna Ina baban ta yake ,Inna na cemata yayi tafia ,haka dai kulin sukeyi har ta Fara mantawa d shi ..

Wasa_wasa har shekaru suka shud’e ba Hafiz mamman ba lbr sa har Aishatu t Dena tambayar Inna shi,Dan Maliki ya baza makamai na neman Hafiz a duk inda aka ganshi Dan be hak’ura ba ..

Ayanzu b Wanda ta sani sama da Inna , Bayan wasu shekaru ma akazo aka sanar ma d Inna wai anganshi mota ta kad’e shi , taci kukan ta ta k’oshi tabisu da addu’a har umaima da mahaifin Hafiz din mamman Dan mutumin kwarai ne se mata da Allah ya jarabe shi d ita ba ta kirki ,yanzu ko ai tafara Raina kanta …

Bayan wasu shekaru Aisha nata girma inda Inna take CE Mata Indo shine Indo y bita daga wasa …

Inna tayi kokari wajen temakama Indo wajen karatun ta adadafe ta gama makarantar firamari,tanayi Tana had’awa da islamiya da makarantar dare har ta wuce karamar sakandiri inda tayi aji uku da kyar a makarantar gwamnati …

Daga hakane Bata ci gaba ba ga Inna karfi na karewa shine fa , akazo akace ta bada Indo tayi aikatau lokacin indon na tausayama Inna ganin yadda take hidima da ita shine taci buri biyu a Rayuwar ta ..

Na farko taci burin neman nakanta Dan ta taimaki kanta ta taimaki Inna ta ..

Na biyu sai tayi karatu insha Allah arayuwar ta na Arabic d boko…

Wanan sune burikan Indo,arayuwar t ayanzu.

Ba lefi Indo tayi karatun addini ta ,tare take hadawa d bokon ta har t gama

Wanan shine lbr Aisha Indo

Har ta Fara Aiki a gidan su NAWAL ta hanyar wata mak’ociyar su Inna ..

 

*CIGABAN LABARI*

“`kubiyo Ni Dan cigaba da lbarin mu“`

*Maman shaheed*????
[12/28, 7:04 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`BY MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)

 

_shafi na shida_

*Wanan shafin nawa nakune kawaye na masu kirki d Auntyna*

“`AUNTY ZULAIHAT AMSHI

_Mrubuciyar AMINATU BAIWAR ALLAH_

*UMMI HAMBALI
(WATA K’ADARAR)

*FATY AFREEN
(KAWATA matar mijina)

 

Anata Shirin biki ,komai y Kamala angama tsara event d’in d za a gabatar ……

Akon twins Yana hannun su Dan tuni angama musu d’ukunan su ,fitet gown d Riga d skit masu shelf ,har na Indo ma sun karb’o Mata …..

Ranar suka Isa ,gdn Aunty NAWAL , bayan sun Bata nata Ankon dake duk guri d’aya aka musu Kuma duk SAFWAN ne y biya musu kud’in d’inkin , haka suka b Indo nata bayan NAWAL Ta tafi gabatar d Alwala itama Dan t zama Mata dole ne d cewa zatayi Indo t Mata har wanka ma “tirkashi d Indo Tasha kallo ” …

Dan haka d’akin t suka shiga suka mik’a Mata ,Aiko tanata murna Dan Bata tab’a sa kaya masu tsada d kyau d tsari irin haka ba a tarihin Rayuwar t ,Dan farin ciki har kwala tayi sukace ba komai karta damu ,t d’iba zata fita Dan nunawa uwar d’akin ta ,Aiko su twins suka hanata sukace karta nuna Mata sai ranar bikin kawai intaga Ana hidima kowa nasa nashi itama t sa ,suka Gaya Mata duk ranakun d za asa kayan t haddace a brain d’in ta cike d murna d nufin zataje d nunama inna Abin Arzikin d kannen dadyn Noor suka Mata ….

 

Bayan sun gama Abin d y kawo su suka ma Aunty NAWAL sallama suka tafi ….

Bayan sun koma gdn suka labarta ma Ammy sunba Indo nata Ankon harda Aunty NAWAL d’in ma , Ammy t ce sun kyauta ,Allah ysa mu Fara cikin nasara ayi agama lpy ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button