HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Kamar ankira faruq sai gashi y shigo harabar gidan a sukwane d mota ,Yana fitowa y Fara tmby ba’asi Babu Wanda ya samu damar tsaida fadan y bashi amsa ,shiko Abin y kular dashi y kakafta musu Mari kowace so biyu a kuncin ta d hanzari suka shiga hankalin su ,y Fara musu ruwan masifa ,ran NAWAL y gama bacci yamareta gaban huzzara ,itako huzzaran tad’an shiga hankalinta shine har ta iya sanar Mai da abinda y faru ,shine ya Gane NAWAL ce Mai laifi ,y dawo kanta y dinga zazaga Mata bala’e akan danmme zata aikanmai yara waje? Meye baya ajiyewa a gidan shi ? Atsarin shi baya Aiken yaranshi ko mazan bare ‘ya macce karta Kara yimai Haka inba hakaba zata fuskanci mumunan hukunci ,

NAWAL taji zafin kalaman shi ,ta zazaga Mai tata rashin kunyar ta wuce part dinta ,ya mata kwafa y sa Kai y wuce part din huzzara dake acan yake …..

 

********
Huzna anacan gidan angonta ,lokacin d safwan y Sami lbr gudun d tayi yaci dariya sosai ,ayanzu shijan shi yasan ya rabu d kwalon mangwaro y huta d kuda d bacin huzna ,itako tabacan ranta ba Haka taso ba duniya safwan taso y zama miji agareta ,Amman ya zatayi ,angonta shiko sai lalab’a abarsa yake Dan yacimma manufarsa ……

Tun Tana fushi kuka ,bacin Rai ,har t Dan Fara sakin rainta kadan tayi girki taci t k’oshi ,Amman fa ango b wata kulawa yake samu daga gareta ba …..

 

*********
NAWAL burinta y za’ayi t kuntatama huzzara ,Dan Haka t hada birthday party ta Akan mijin ne ya Bata kudin party Dan ran huzzara y sosu ,tabata shirye shiryen ta batare d ta sanar ma shi kanshi mijin ba sbd t Raina shi gani take d Auren shi d Babu duk daya….

Sai d t Gama Shirin komai sanan t sanar ma faruq din ,faruq wani irin mutum ne Dan Haka yaki Amincewa d abinda ta kudiri aniyar shiryawan duk d cewa d kudinta zatayi, Amman Sam yaki Amincewa ,itako ta kafe be Isa ya hanata rawar gaban hantsi ba Dole ta cikata ladanta t Gama kashe kudinta……

Ranar ba NAWAL bace d girki t Kira kawayenta ta Kuna musu kida suka Fara cashewa Ana cin snacks Ana korawa d drink, huzzara tazo wucewa suka hadu d nawal ,ganin alamun tmby a fuska huzzara ,NAWAL t Fara ce mata ,ya Mata Kinga Abu gwanin birgewa ko ? Wanan aikin faruq ne y sakar min ‘yan daloli nayi murnar cikar sherata ta haihuwata harda ragowar canji kafin savuwar mota tabiyo baya …..

Jin kunuwan huzzara bazasu iya sauraron kalaman NAWAL ba ,huzzara t tafi t barta a wajen ranta n Mata Kuna har NAWAL din t gano hakan ,Dan Haka t bushe d dariya t koma cikin kawayenta akacigaba d cashewa …..

Itako huzzara babu abinda y fi Bata Mata Rai ila kudin d ya sake y bar katuwa baliga kamar NAWAL yin shagalin birthday ,tun yaron su n fari take ma faruq naci Akan sumai birthday n cikar shekaru biyu a duniya yaki Sam waishi baya son bidi’a Haka t dinga Mai naci Akan sauran yaran Sam yaki tun Tana d’aukan Abun a zalinci ko bayason sakin kudine t Gane cewa bakin ra’ayin sane a Haka Dan be Rasa kudin hidimar ba ,hatta manyan yaranta d sukayi sauka su biyu Hana su shagalin saukar yayi ,wai bidi’a ne babu Aya bare hadisi saidai y yanka musu rago y siyo musu abinda ba’a Rasa ba suci a gida su kadai Wanda yayi yawa aba makota ,Amman be yadda d taro kamar shagalin biki ba Sam ,tun tanajin bacin Rai d takaici ko d kudinta ma ya hanata ,Dan azauna lpy t hakura d irin tsarin sa take zaune dashi ahaka ,Amman yanzu Dan wata Yar gwal mace Amaryar SA sai y karya dokar y fijin tsoronta kenan,shine abun d Yama huzzara ciwo aranta har ranta y bacci NAWAL t gano hakan ….

Bayan faruq y dawo y samu lbr ,sa’anan huzzara t dinga zazagamai gori harda cemai mijin tace ne shi ai ayanzu magana harda Wanda bata taba furta Mai ba ,Dan Haka ranshi y bacci y dinga Gaya Mata mgn itana huzzara bebar part dinta ba seda y tabatar y bakanta Mata sosai ,sanan y nufi wajen uwar taurin Kai …..

Koda y shiga y Sami ragowar cake dinta n birthday d ta yanka tabaci Tana nishad’i Bayan kowa y watse sai ita sai halinta ,Aiko d ruwan masifa y Fara Mata sallama ,fahimtar inda masifar shi t dosa Akan Birthday d tayine ,gashi ze Bata Mata farin ciki ta Haka kawai ,itama ta shiga mayar Mai d kalamai marasa dadin sauraro Wanda be kamata mace ta dinga mayarma d mijinta ba ,Yana fada Tana fada har y mareta Yana cewa Bata d tarbiya y d’aga hannu ze sake marinta t tare Tana yunkurin ramawa Aiko faruq yace Bata Isa ba ,Dan be auri maccen d ze dinga fada Tana mayar Mai b har y mareta tayi yunkurin ramawa ba Dan Haka tatafi gida y saketa ,NAWAL tayi shewa t buga tsaki tace aikin banza taimakona kayi ,dakai d banza duk daya ,Dan Haka nama kaina tsari Babu wani dikon jinin ka atare dani banshigo gidanka ba sai d na shirya wace hada zuriya d Kai ,d Wanda akeso ake hada jini ba irinka ba ,maganganun NAWAL sunmai ciwo Dan Haka y dinga zaginta Yana tir d tarbiyarta ,itama tana ramawa ,y yunkura zai daketa Dan Abin duka y dauko d gudu t shige bedroom d’inta t sa key ,Aiko y dinga tazo t barmai gida wlh sai tabarmai gida tunda Babu gadon ta ko na ubanta a ciki duk abinta yake fada Tana bashi amsa ,har n Kara cewa NAWAL dama Haka take kodai faruq ne y kaita bango?

 

NAWAL Bata samu fitowa ba seda t hada ‘yan suturun ta ,seda t tabatar yabar part dinta sanan ta d’au makulin motar ta tadau hanyar gidan su…….

Bata San me ta aikata ba seda tayi parking a harabar gidan su fitowa ta shiga gidan ya gagareta Dan Bata d bakin yima mama d Abbanta bayani ,Nan ta shiga tashin hankali Wanda ba’a samasa Rana ……

 

******
Aishatu yanzu b sosai take zuwa shop ba sbd jiki d jini Amman Tana lekawa Kuma suna Mata abinda y Dace sun rike amanarta ,safwan ma Yana taimaka Mata d wani Abun ,shima yanata samun budi har y Fara Gina wani company na gadin gwuiwa shida Alhajin su d Yaya su uku Amman safwan yafi hannu aciki ….

 

Ba’a dawo d Noor d haneef ba Dan a hutar d Aishatu ,suna can Ana kula dasu sosai ,itama taji da kanta d hidimar gida Dan Taki yadda a kawo Mata Mai Aiki ko wacce zata taimaka Mata indai b heedaya d take zuwa ba wani lokacin ……..

 

NAWAL da kyar ta samu t shiga gida jiki babu kwari ,Tama mama sallama ,mama ta amsa t Mata masauki ….

Ganin yanayin d yarta take ciki kawai y sanar Mata d komai ,Babu Wanda yacema wani ufan ,sai mama tace yanzu Kuma wacce tsiyar Kika kuntugo?

NAWAL t bude Baki zatayi mgn ,sukaji salamar faruq ya shigo Yama mama salama Gaisuwa sama sama y Bata takaddar NAWAL Yana gagayama mama magana Akan tarbiya d halayen NAWAL y gama Mata rashin kunya y fita ,Yana hanyar fita sukaci Karo d Abban NAWAL ,lokacin Kuma NAWAL t biyo shi Tana zagin shi Akan kalaman d y gayama mamanta ,Koda Abbanta y tmby faruq ba’asin zagin d nawal take Mai Yana mayar Mata ,sai faruq y Fara Mai rashin kunya shima ,Aiko NAWAL tacigaba d Rama ma iyayenta ganin rashin hankalin zeyi yawa ,Abban ta ya jata suka koma ciki ,faruq y fice daga gidan ransa a matuk’ar bacce ….

NAWAL n komawa ta fad’a jikin mama Tana kuka Mai ban tausayi ,ba kukan komai takeyi ba sai na irin fadan d zata Sha a wajen Abbanta d mama ,ayanzu ta katayin nadamar duk ayuka d kurakuran d ta aikata ,Bayan mama t Gama korama Abban NAWAL abinda y rabata d Faruq ,ta mikamai takardar sakin ,sai Abban nawal y Fara zazagama NAWAL ruwan masifa har seda y Mata lafiyayun Mari masu gigitarwa ,da kyar mama ta kaishi dakinsa da magiya d ban hakuri Dan komai ze iya faruwa ranshi y matuk’ar bacci fiye d yadda na maman y baci ,d kyar y samu y rage kayan jikin shi t bashi ruwa yasha t dinga bashi Baki Akan karyana yarsa Baki Dan Allah …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button