KUSKURE Complete Hausa Novel

NAWAL Bata aikin komai sai na kukan nadama Mara Amfani ,itako mama nata rarashin gyatumin NAWAL din ……
Ba Abban NAWAL ba hatta mama zubamata Ido sukayi tare d tsatsauran mataki Dan ,Abbanta kuntata Mata yakeson yi Dan y hanata Aiki ,yace gwanda t dinga zama a gida Tana Taya mama Aiki tunda zaman gidan takeso ,NAWAL hakan yasata cikin matsanaicin tashin hankali d firgici d hukuncin Abban ,Amman ganin yanzu Bata da zabi ko damar bada hakuri sai kawai ta hakura ta bi umarnin d ya Bata badan taso ba …..
Bayan komawar faruq gida huzzara ma ba karamin haurawa sukayi d Faruq ba Dan Dan seda yace itama taje gida seya nemeta Amman tace yayi kadan wlh gida taci gida sede shi ya fita yabar musu gidan ita d yaranta Dan wlh inbesan ta ba a iya zaman su d ita yanzu ze Santa Dan ya gama kaita karshe ,Aiko suka dinga gabzawa fir tace wlh Babu inda zata ,karshe dai sai iyayene suka musu sulhu aka gyara Auren sukaci gaba d zaman doya d manja ahakan ,ran huzzara fess tunda NAWAL tabar gidan da sannu zata shawo Kan mijinta uban ganin dama ….
Duniya Tama NAWAL kunci anhana kawayenta zuwa ,ga Aiki an hanata zuwa ga aikin gida mama ta sakar komai har girki ga mota ga makulin mota a hanun ta Amman babu Wajen zuwa
Abbanta har faruq y tuntuba ko ze iya mayar d nawal Amman y nuna Mai Sam baze iya ba batasan darajar nagaba d itaba ,shi Azo a kwashe kayanta ma ze gyara part dinsa y fuskanci zama part daya d mace bacin Rai ne ,Aiko shine fitar ta ta farko tun Bayan fitowarta dg gidan Faruq din ,akazo kwashe kayanta ,Nan ma Saida suka raba Abin fada d huzzara ALLAH yasa faruq baya Nan ,d kyar aka rabasu ……
NAWAL tayi bakar nadama sosai ta takura iya takura ,ga damuwa ga nadamar *KUSKURE* da ta aikata tun farko ,Dan ayanzu harda nadamar barin gidan Faruq da tasan duniya zata sauya Mata haka har mahaifiyar ta d mahaifinta su juya Mata baya Haka d batayi yunkurin fitowa daga gidan Faruq ba ,Dan ko faruq y nuna Mata so y sakar Mata aljihun shi y kilace ta ,itace t bijire Mai ,hatta iyayenta sun so t zauna t rungumi aurenta d Faruq Amman Taki ,ayanzu tayi nadamar duk Abinda t aikata ,musamman d safwan yaso mayar d ita Taki komawa sbd Indo d tuni Bata fuskanci wanan Abun ba ,gashi yanzu safwan y Mata nisa ,ita wlh tayi nadamar rayuwarta ta baya , babban burinta be wuce iyayenta su sasauta Mata su Dena fushi d ita ba ,sanan Abbanta y dawo d kulawar d yake Bata ada ,wlh ta shirya karban kowane hukunci tare d gyara halinta wlh ko ayanzu t horu d zaman gida d Aiki d shiga kitchen ta Gane duk wani Abu d me Aiki yake fuskanta musamman lokacin d sukayi zama d Indo ,Ashe dacan yadda t rayu a gaban mama zaman asara d sangarta tayi? Dan ko da Wasa Abban ta baya Bari awahalar d ita bare abarta t shiga kitchen akanta ansha korar Mai Aiki ,gaskia ALLAH baya zalunci wlh ta aikata *Kuskure* Amman tayi nadama sosai fiye d tunanin Mai sauraro …….
_To Fanc NAWAL Na Tsaka Mai wuya Agajin Gagawa Daga Masoyanta Hilisssss_????????♀????????♀????????♀
*Maman shaheed*????
[6/3, 7:17 AM] Mmn Shaheed: ???? *WRITING*????
“`BY“`
“`MAMAN SHAHED“`
???? *ROMANTIC WRITER’S ASSOCIATION*????
*KUSKURE* ????????_????????
( _yar Aiki Ko Matar Gida_)
_shafi N saba’en d shida_
NAWAL na cikin matsanaicin Damuwa sakamakon toshe Mata kofofin jindadi d watayawa da Abban ta me share Mata hawaye d mamanta sukayi ayansu ,ga horar d ita ayukan gida d mama takeyi masu tsauri Tana cigaba d shigar Mata d darasin Rayuwa cikin maganar d take jefa Mata lokaci zuwa lokaci ….
NAWAL tayi nadama matuk’ar nadama Dan Ayanzu bataki ta nemi yafiyar Faruq ba indai zai mayar da ita d’akin shi ta shirya zaman Amana d iyalan shi …..
Safwan sun Kamala Gina company dinsu n hadin gwuiwa dasu Ahj su ,har anyi walima d Addu’a na fatan Alkhairi ,har y Fara Aiki ….
Safwan n kula d Aishatu tanata renon cikinta lokaci zuwa lokaci Tana kaima Noor d haneef ziyara Dan kaunarsu na Mata zollo cikin ranta ….
Huzzara anacan Ana fama d Faruq ,yanzu t kankane mijinta azaton ta Kar ya komawa NAWAL shiyisa take ta faman kankane shi ….
Huzna ma anacan anata zaman da bashi akaso ba d wanin safwan ,hakurin zaman takeyi sosai ,shiko ango kulin cikin lalab’ata yakeyi dayi Mata ‘yan dabaru ,Haka dai suke Rayuwar gidan nasu …..
Abban Aishatu d aunty zainab ,Suma suna bama junan su kulawa uwa uba yanzu d suka d’auko Haneef sun tatara so duk sun jibga Mai tatali kulawa bashi suke ko Dan d suka Haifa iyakaci amatsayin jika Mai gata suke rikon shi Daman …..
Twins sun haihu ansha shagali tsakanin su wata 3 asha budiri kowacce Tana gidanta Tana wankan jego cikin kulawa mijinta d dangin sa ,ita hassana dama tana bangaren su aunty zainab kodan mutunci Mai karfi dake tsakanin sirikin hassana d Abban Aishatu…..
Aishatu cikinta y Isa haihuwa gab take d haihuwa ,ga nauyin ciki ga kokarin zuwa shagon ta ,Tana yawan zuwa gidan Inna Kuma kodan ta dinga debe Mata kewa su Sha hirar su Abun su …..
NAWAL na matuk’ar son Kiran safwan ko ganin shi ko turamai d sakon karta kwana akan ya yafe Mata *KUSKURE* da tayi abaya ko ta Sami salama cikin zaman gidan su da mahaifanta suka juya Mata baya ,kannenta ne kawai takejin dadin su ,Dan Haka take jinta cikin ukubar rayuwa a yanzu Dan ta takura ,Babu Aiki Babu shiga cikin kawaye ,Babu hutu ,ga hanun ta Babu ‘yan canji ,ga zaman takura ba’a barinta fita ko Ina ,gashi t Applying wani aiki a hospital Mai kyau d tsada sabon hospital ne ta Kuma samu annemi ganinta ,shine taketa fama d Abba d mama Akan su Mata hakuri taje tagani ko za’a Dace ……
Yin duniya Abbanta yace ta gama Aiki sede zaman Aure inta shirya , NAWAL tayi magiya Amman ko ajikin Abban ta ,ganin Babu sauki sai ALLAH kawai tasa Mai kuka tanata Mai magana Tana karanto Mai karatun tuban d tayi Akan kurakuran d ta dinga jerawa ,da Alk’awarin bazata sake bashi kunya ba tayi Alkawari …..
Tausayin ta duk y d’arsu a zuciyar iyayen nata ,suka Mata gargadi d cewa zasu barta taje Amman Nan kusa t fito d miji tayi Aure ,Kuma dawamamen Aure Wanda zata zauna tsakani d ALLAH ,ta d’aukan musu Alkawari…..
Itako babban burinta ayanzu shine ,safwan y yafe Mata ,ita ta fitar d Rai d sake zama dashi ma ,zata hakura t zauna d duk mijin da kaddara ta zabar Mata ayanzu kodan faranta ran iyayenta d cika musu burinsu ,bawai Dan safwan y mayar d ita ba ,ayanzu tasan ya Mata nisa ta d’au darasin Rayuwa ,ta gane cewa Wanda ka Raina yakan Zo yafika d komai d komai ,ta amince komai y faru d ita sakacinta ne ayacce ta gani da idon ta ,Dan Haka kulin cikin nadama take…..
First Abinda ta Fara tunanin yi shine zuwa gidan su ammyn su safwan Dan Rokon su gafara d yafiyar duk wani sabani d y shiga tsakanin su ,to Amman Tana kunyar ace Dan Tana son komawa gidan safwan ne tazo neman yafiya ,Dan Haka tace ta hakura ,wata zuciyar tace indai tsakanin ki d ALLAH zakiyi to kije, kije kuma da tsarkakakiyar Niya Dan Haka t yanke shawara zuwa kawai …..
Bayan mama d Abban t sun yarje Mata zuwa hospital din d ake nemanta ,zuka Mata izinin taje ta Kuma kula d kanta ,ta musu godiya tayi shigar Kamala ta fita zuciyar ta fesss Dan har ta samu ta shaki iskar d tajima Bata Shaka ba ,gidan Ammy t Fara zarcewa ….