HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

D kyar gwuiwa Babu kwari ta shiga gidan ,Ammy d Alh d Yaya d safwan suna zaune a main parlour gidan suna hirar company din su d irin progress din d ake samu cikin nishad’i hankalin su kwance ta musu sallama t shigo cikin Kamala …

Ganin su seda tayi kamar ta juya ta koma ko kasa ta tsage ta shige ,tajikunya matuk’ar kunya sosai …

Safwan tunda y kaleta so 1 y d’auke Kan shi be Kara kalon inda take bama ….

Ammy ce ta sakar Mata fuska Dan taji d wacce tazo ,har ta Mata iso zuwa kusa d ita ,jiki Babu kwari NAWAL taje kusa d ita ta zauna a Kan capet ,Ammy tayi tayi ta tashi ta koma Kan kujera kusa d ita Amman Taki ,tace ta barta a kasan …..

NAWAL cikin ladabi d biyaya take gaishe da Ammy d Alh su har Yaya har safwan shide safwan kin amsawa yayi sai d Alh su yamai mgn sanan y amsa Mata a dakile irin jeki Maya dinan …..

NAWAL Tama kasa furta komai …..can sai g Noor d Janna sun fito dg d’akin Ammy hanun su rike d Teddy kowace…

Noor na ganin momyn ta tasaki Teddy ta Tafi da gudu ta Rungume maman ta ,Tana tmby t yaushe tazo Amman anan zata kwana? Tmby Noor tayita jeroma momyn ta ,kowa seda yayi mamakin shakuwar Noor d momyn ta duk d sun Jima basa tare ,tsakanin d’a da mahaifi sai ALLAH ,me neman kuka anjefeshi d kashin awaki , NAWAL ta Fara shashekar kuka d Raunananiyar murya Tana Basu Ammy d Alh su safwan hakuri Akan duk wani Abu d ta musu a baya wlh bada manufa tayi ba sumata aikin gafara Dan ALLAH har Yaya ….

Kowa yace y yafe Mata ,Banda safwan Jin yayi shiru t sake furta” nasan dama Kai bazaka yafe min ba sede idan gawata ka gani shine zaka yafe min ,Dan girman ALLAH Kayimin Aikin Gafara bansan ko wanan tuban d nakeyi ko shine sanadin haduwar mu ta karshe ba …….hakan da ta furta seda zuciyar safwan ta buga d karfi…..Amman y dake ko kalon ta beyi ba ……

NAWAL ta cigaba d rokon yafiyar safwan ,hade d kalamai masu karya zuciya ko su Ammy seda ta Basu tausayi atunanin su ko wani Abu ne y faru d ita har Tana cewa zata fita a Rayuwar safwan d kowa nashi ,matuk’ar y yafe Mata ….

Jin kalaman bakinta yasa ,Ammi Tama safwan mgn d y furta wani Abu Mana ,Alh su ma ya Kara d yimai magana …..

Seda Yaya y Kara saka musu Baki sanan ,safwan “yace y yafe Mata Dan ALLAH” NAWAL “tace ta gode Masa ALLAH y shiga cikin Al’amarinsa d iyalin sa Sosai tamai Addu’a ,shi Kan shi yaji Dadi ,Dan Haka kowa yaji tausayinta ta musu sallama Akan zata tafi batasan ko wanan shine haduwar su ta karshe ba duk t karyar musu da gwuiwa …..

Noor ce tace zata bita , NAWAL t Bata hak’uri tace tayi hakuri Nan ne dolen ta tazauna t rayu d mahaifinta d ‘yan uwan shi ,Noor ganin momyn ta zata tafi ta barta ta fashe d kuka ….

Ita kanta NAWAL din kukan tasa t Rungume Noor ,Ammy t Gama katantar shakuwace tsakanin uwa d ‘yarta Dan Haka tace NAWAL ta tafi d ita gobe se Azo a dauketa ,NAWAL seda tayi murmushin Jin Dadi tanatayima Ammy godiya ….

Safwan ko cewa yayi Ammy Noor ……kafin y karasa Alh y dakatar dashi …

NAWAL t Kara yi musu godia ta tafi d Noor badon Ran safwan yaso ba …..

 

Har su Noor suka bar gidan ran safwan a bacce Dan Koda Noor tamai bye _bye badan yaso b y d’aga Mata hannu suka tafi ….

Duk sun hango nadama karara a tare d nawal ,Amman Banda safwan ,har suka gama hirar yafewar d suka Mata shidai ko uffan be ce ba ,har suka fice gaba dayan su akabar Ammy d Janna su kadai Ammy nata mamakin sauyin d aka samu dg NAWAL Haka ….

 

NAWAL cikin murna taje hospital din d aka kirata ,t Kamala komai d alamun zasu dauketan t wuce gidan su …

Ganin t d noor mama t tmby t inda t samo ta ,NAWAL ta Mata bayanin komai Bata boye komai ba ,t nuna ma mama ganin take kamar Dan safwan da dangin sa Basu yafe Mata bane Taki samun kwanciyan hankali …… Mama t fahimci nadamar Yar ta sosai Dan Haka tace t Fara hankali , Koda Abban NAWAL y dawo ze Fara fadan dauko Noor ,mama tamai bayani n fahimta har y Gane ….

Ranar Noor d nawal kwanan Farin akayi Dan NAWAL Bata tab’a sanin Tana son Noor ba sai yau ji take kamar Kar arabata d ita Dan Haka kusan kwana sukayi suna Hira d Wasa d nishad’i ita kanta Noor tasan yau momyn ta tafi ji da ita….
[6/3, 7:18 AM] Mmn Shaheed: ???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

???? *ROMANTIC WRITER’S ASSOCIATION*????

 

*KUSKURE* ????????‍????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi N saba’en d bakwai_

 

Wata shakuwace tsakanin Noor d mommy ta a Dan zaman su n yau Dan sai yanzu NAWAL take Kara bambance son d takema tilon ‘yar tata ……

Itama Noor ta ji dadin kulawar d ta samu wajen momyn ta …..

Aishatu d safwan anje asibiti andawo Dan har dashi ake zuwa awon cikin ,Yana makale d Aishatu Dan ba karamin tausaya Mata yakeyi ba ,wani Abun mamaki asibitin d Aishatu take zuwa awo kuma anan zata haihu ,anan NAWAL ta Sami Aiki bangaren haihuwa Kuma next week zata Fara aikin …..

 

SAFWAN Yana sane yaki zuwa dauko Noor ,har sai d Ammy tamai mgn tukunna ,d kyar t lalab’a shi ya tafi d’auko ta ,ko d yaje be shiga gidan b a waje y faka motar shi y aika yaro wai Noor tazo inji dadyn ta su tafi Dan kin Kiran NAWAL yayi a waya ,baya son Abin d ze hada shi d ita kwatakwata ….

Jin Aiken yaron mama t fahimci komai akayi safwan dinne,Dan Haka mama t ma NAWAL mgn Kan t kaimai ‘yar sa ai sun kyauta ma d suka barta haka ….

“NAWAL cewa tayi aa mama barta taje t same shi su tafi ba sai naje b duk wani Abu d zai kusantani d safwan Ina nisantar sa ,so nake namai nisa kodan ya samu sukuni shida iyalin sa mama ta hanyar Hana Ido na d kunuwa na gani d sauraron muryar sa zan samu n manta dashi a Rayuwarta badan bana kaunar shi ba …..

Mama t tausayama NAWAL mussaman lafuzan d suke fita a bakinta t tabar tabbas ‘yarta t Fara hankali duniya t Mata karatu Mai wuyar haddacewa …

D kyar mama tasa NAWAL Raka Noor Dan asan safwan dinne b wani ba yazo daukanta ,Dan Haka t hada Mata su sweet d’inta d kayan d tasai Mata sababi t Bata ta tafi kaima safwan ita …..

Koda NAWAL t hango motar sa ji tayi kamar t tura Noor din ita kadai ita tayi komawarta cikin gida ,Amman Noor t dinga janyo hannun ta Tana cewa g dadyn ta can tazo suje ,Haka t hakura t karasa…

Tana zuwa t gaishe d safwan ,ya amsa d kyar ,y rugume Noor dinsa Yana cemata su tafi …….

Noor CE tace Dady g momy ,yace eh yaganta sai a lokacin y Dan Kali NAWAL shekeke kalon Dole ,Noor ta sake cewa Dady mu tafi d ita Dan Allah ta siyama Haneef Kaya har d n wasa suna cikin ledan hanun ta wlh Tana son Haneef din mu Kuma kace duk Mai son na yaso Haneef muma zamu so shi Tana kalon dadyn nata cikin shagwaba d tuhuma ….

Safwan y lumshe Ido yace hakane ,Haneef y gode sai me Kuma batare d y kalli inda NAWAL take ba…..

Hakan y Sosa Ran NAWAL Amman babu yadda t iya,sai ma mamakin surutun Noor d take kamar wacce aka shirya Mata ……

Cikin rawar Baki d kankan d Kai NAWAL t Miko ma safwan ledar tace gashi dadyn su Haneef agaishe d haneef d maman su Dan Allah ,ace Ina gaishe ta Kuma t yafemin Dan Allah in Allah be kaddara saduwar mu ba Dan bani d tabacin zamu Kara had’uwa ,ace Mata Ni nayafe Mata har cikin Raina ban riketa d komai ba ,kaima Dan girman ALLAH k Kara yafe min wlh nayi nadama Akan *KUSKUREN* d n dinga aikatawa Kuma wlh inason nisantar ku nisanta Mai tazara Kuma zan nisance ku batare rikeku acikin zuciyata ba ,Babu digon laifin kowa araina kamar yadda nake fatan Kuma kumin aikin yafiya badan nni ba Dan ALLAH! musamman Kai gani nakeyi kamar baka yafe min ba ,Dan ALLAH Kar ka manta d wasu Abubuwan d ba sai n tsaya dawo maka d bara bana ba ka duba Alkhairi karka duba tsiya a tsakani na da Kai Dan girman ALLAH ka yafe min yafiya t har Abada….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button