KUSKURE Complete Hausa Novel

Safwan duk y Gama sauraran t y ja dogon numfashi yace Allah ya yafe mu Baki daya,Ni na yafe Miki sai Atari gaba Kuma ……
Wani ajiyar zuciya NAWAL tayi Jin furucin safwan ,Noor tace ka yafemata Dady ? Duk sukayi dif,t sake maimaita tmby zuwa g momyn ta Tana cewa momy me kikama Dady y yafe Miki laifi? D sauri t jd’aga Kai Alamar eh ,”tace Noor laifi namai na rokeshi Kuma yace y yafe min kinji ?
Noor tace wai Haka Dady? Y daga Kai Alamar eh ,y Kara d cewa n yafe Mata my Noor …..
Noor tace ta gode Dady ,to mu tafi d ita ,yace aa ,ganin Noor na Shirin yimai Rigima y Mata karyar Dole Akan zamuzo dai mu dauketa wataran ,Noor ta dinga murna ,safwan yaja mota Bayan NAWAL t Miko Mai kayan y karba y ajiye kusa d Noor ……
NAWAL Haka t koma gida tanata Raya wasu abubuwa acikin ranta …..
Shima safwan Haka ,gidan Ammy y mayar d Noor y Bata ledar d nawal t bashi ,Noor t dinga murna t Fara yima Ammy bayanin hadda kayan Haneef ,t karba t fito d kayan wasan Haneef d momyn ta tasiyo masa t Fara Shan sweet din d tafito dashi su Ammy nata tsokanar ta ,Noor t Fara b Ammy lbr ai momyn su watarana zatazo Nan su zauna ,Ammy Tasha jinin jikinta akan ko safwan n son dawo d itane Amman Babu lbr Kuma bataga alamun hakan atare d ita b ,sai kawai t basar ,Koda safwan zai tafi sai d Noor t hadashi d kayan kanin ta Haneef wai akai Mai ,Dole y karba y tafi dashi ……
Akwai wani furuci cikin kalaman NAWAL d yayi tasiri cikin zuciyar safwan sosai y Jima Yana dogon nazari akai Kuma ,har sai d Aishatu t fahimci nazarin nasa nashirin shiga hakinta Dan y rage Hira yadda suka Saba ,Koda t Mai tmby yace Babu komai yayi kokarin jingine tunanin y bama Aishatu nutsuwar sa kamar yadda suka Saba har zuwa kwanciyar bacci ,Bayan tayi bacci y Dora d tunanin shi ,y ji ajikin shi matuka NAWAL ta ladabtu duniya t Mata bulala Kuma t canja dabi’u duk d bashi d tabas ,Amman yanaji ajikin shi ayanzu NAWAL t Fara ko Tana Shirin amsa sunan ta ,Yana kaunar NAWAL matuka badon komai ma sai Dan itace fisrt luv din shi ,Kuma yamata son d betaba yima wata ‘ya mace ba kafin Auren Aishatu ,duk d kaunar d yakema NAWAL be Bari tafi karfin shi t zama miji y zama matar ba ,Haka zalika har aka Kai ga rabuwa tsakanin su y daurema rashinta a kusa dashi matuka Wanda Babu Wanda yasan hakan sai zuciyar shi ,asakamakon hakan ALLAH y turo Aishatu cikin Rayuwar shi har tazama wata gin shiki na Rayuwar shi har y kasa tantance irin son d yakemata d Wanda Yama NAWAL ,dg baya y auna a mizanin hankali yaga son d yakema Aishatu y rinjayi son d yakema NAWAL sakamakon wasu Abubuwa d Aishatu ta Dara NAWAL dasu Wanda ita NAWAL Bata dasu ko Bata Amfani dasu wanan shine y sake daga darajar Aishatu sama d ta NAWAL a farfajiyar zuciyar safwan d ilahirin jikin shi har y zamto Babu wata a gaban shi sai Aishatu ita kadai ,Wanda har takai idan yanason Dora matsayin NAWAL Kan na Aishatu Abin baya bada ma’ana Wanda y gama yadda d Kuma Amincewa lalai Yana matuk’ar k’auna d son Aishatu fiye d kowacce macce a yanzu ,Amman f har yanzu kamar Akwai didigar son NAWAL a zuciyar shi ,Amman Babu Wanda y Isa y gano hakan …..
Bayan kwana biyu ,safwan yaje gidan Ammy ,Ammy t Fara Mai mgn NAWAL sai yaji kamar Tana Mai Susa cikin zuciyar shi Amman yaki Bari t Gane sai ma watsar d zancen d yayi b,atunanin shi Yana so Yama Aishatu halacci indai zuciyar shi zata bashi goyon baya …..
Wata Rana safwan d Aishatu sunje awo asibitin d take awon ciki inda anan yanzu NAWAL take Aiki , Koda suka shigo likitan d ze duba Aishatu y Sami Kiran gagawa zuwa wani asibitin Dan Haka y fice ,safwan y kirashi be daga ba ,suka hakura suka Fara jiran shi ,kusan awa biyu d Rabi be samu dawowa b dg baya ma yakira asibitin y sanar d baze samu dawowa ba Dan operation zeyi yanzu Kuma b mutum 1 ba Dan Haka NAWAL ta duba Mata masu awo …..
Aka sanar ma d su saFwan cewa suje su jira g d’akin d za’a duba masu ciki can ,sukaje suka zauna ,basu Jima d zama b NAWAL t fito taje taga wata mara lpy Tana dawowa idon ta y hango Mata su safwan d Aishatu Bata Bari sun ganta ba ta koma cikin office dinta tadai fahimci awo sukazo ko suna cikin wadanda Dr ummar y turo Mata su ne Dan Haka ta bada umarnin afara turo Mata Ido t kwatanta ta …..
Jin ankirata afarko wasu matan har sun Fara mita ,wacce t Kira tace itama umarni aka Bata ,safwan ko Dadi yaji za’a sallame su su tafi Dan yafi tausayama Aishatu ma d zama …..
Aishatu n shiga tayi tozali d nawal tad’an bude Ido ,NAWAL tamata nuni d ta zauna cikin hikima d Nutsuwa d rarashi NAWAL t dinga yima Aishatu bayani akan kartasa komai a Ranta t dauketa matsayin ‘yar uwa wlh Babu cutarwa ko mugun Abu a tsakanin su a yanzu tajima d Gane *KUSKURE* ta ayanzu duk su yafe Mata zaman Amana d lpy ne ateakanin su me wanzuwa a yanzu Babu cuta Babu cutarwa tsakanin su ,sosai hankalin Aishatu y kwanta d nawal sbd bata tabajin irin lafizan abakinta ba tun tsahon zamansu Kuma zuciyar ta takwanta d ita ,Dan Haka har t saki jiki ta dubata t Mata awo Mai kyau t Mata tmby ta Bata magani tamata fatan sauka lpy ,cike d mamakin canjawar NAWAL farat daya Haka cike d zumudin bama safwan lbr ta nufi safwan din ……
Tun amota t Fara bama safwan lbr d dumi dumin shi d irin karbar d nawal ta Mata d irin dubata har su hakurin d ta dinga Bata sosai ta yaba d canjin d tagani dg NAWAL din ,shima safwan Abin ya bashi mamaki ya Kuma kara yadda d cewa tabbas duniya tayima NAWAL attishawar tsaki takuma ladabtu ga dukan Alamu ,cike d mamaki suka Isa gida ……..
Ahankali aka Fara sabawa d Aishatu d nawal intaje awo har NAWAL nacema Dr ummar ai Aishatu kanwarta ce ,safwan ko tsakanin shi d ita Gaisuwa kawai hakan Yana bashi mamaki Yana Kara gaskata hankali d nutsuwar NAWAL d Dane d seta nuna Mai alamun so ko yayane ……
Yau Aishatu t tashi d matsanaicin ciwon baya g Mara na dadaurewa ,d sauri t Kira safwan t sanar Mai babu shiri y taho y dauketa sai asibiti akayi Dace NAWAL aka samu d wata d gagawa d axama suka karbeta akayi labour room d ita anata fama dai Bata haihuwa b akace asamata ruwan nakuda ko d aka duba asibitin Babu y kare ,cikin jakar ta ta Ciro kudi ta Aiki wani yaje y siyo safwan n tsaye Yama Rasa abinyi sai kwantar Mai d hankali d nawal din takeyi sai wani kishi y yunkuro Mata yadda taga Yana rawar jiki d shiga tashin hankali Akan Aishatu sai tayi kokarin danne shi tacigaba d aikin Lada ………..
Can safwan y Kira aunty zainab y sanar Mata d sauri ta d’auko hanyar zuwa …….
Anata fama ,ba lefi tadanyi doguwar nakuda ,daga baya ALLAH y sauketa lpy ta samu ‘yarta macce lafiyayiya katuwa lokacin d yayi dadai d isowar aunty zainab d aunty suffaya ,sai murna d suka Sami NAWAL tanama safwan Albishir d haihuwar ,duk mamaki ya matuk’ar cikasu sosai ganin NAWAL tayi uwa tayi makarbiya d haihuwar Aishatu Abun y Basu mamaki sosai …..
Aishatu t Sami kulawa sosai ta wajen NAWAL t zama Yar gata a asibitin komai cikin gata d kulawa aka samata ruwa tayi wanka aka Bata Abinci taci Tasha magani ta kwanta tayi bacci Dan taji dadin jikinta sosai ……
Kowa n mamakin canjawar NAWAL ,Kuma ko bakason gaskiya sai tad’an birgeka yadda take kula d Aishatu tsakani d ALLAH …..