HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Ba a sallami Aishatu b sai washe gari ,cikin kulawa d kewan juna suka Rabu d nawal tanata musu fatan Ayi suna lpy ,akace zatazo ai ,tace aa Tana musu fatan Rayuwa Mai inganci da fatan shayarwa lpy …….
[6/3, 7:18 AM] Mmn Shaheed: ???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

???? *ROMANTIC WRITER’S ASSOCIATION*????

 

*KUSKURE* ????????‍????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi na saba’en d takwas_

 

*Inama daukacin Al’umar musulmai barka da Gama Ramadan lpy Allah yasa munyi ibada karbabiya*

 

*Sanan Ina Mana barka da Sallah ,Allah ya maimaita Mana Amin summa Amin*
????????????????????????????????

 

Haka su safwan suka tatara d baby sai gida cike d murna samun karuwa…

Aunty zainab d suffaya su suka dinga hidima d Aishatu d babyn ta suka Dora da hirar NAWAL Mai Abin mamaki ,Dan tashayar dasu Ruwan mamaki gaba dayansu ,tausayinta Kuma y kamasu ,dama Haka Rayuwa take ..

Dan halak baya manta Alkhairi komai kankantar shi ,Dan Haka safwan be manta Abin d NAWAL Tama Aishatu matar shi b ,Dan Yana Kara nisanta kanshi d itane d yaje har gida ko asibi ya Mata godiya ,Amman Ina Yana Kara nisanta d ita duk d zuciyar shi n kusanta shi d ita .

Aishatu nata samu ‘yan uwa masu zuwa barka har su tsohuwa Inna tanata yima Yar rawa da Waka ,Haka komai y dinga tafiya cikin lumana d kwanciyan hankali har aka gabatar d shagalin suna ya taci sunan mahaifiyar Indo umaimatu suna kiranta d haneefa ,Inna sai d aka tuna Mata d tilon yarta Mai Rasuwa hakama Aishatu Sai d su aunty zainab sukayita Rarashin su sanan suka fawalama ALLAH lamarin sa Mai tsara komai ayayin d yaso .

Shima Abban Aishatu da yaji sunan d akasa ,sai d aka tunamai abubuwa d dama yaji so d kaunar tsohuwar matar shi y dawo Mai ,ganin Bata Raye Wanda y halitota y bar duniyar da ita sai ya hakura y bita d Addu’a ,Amman y hada ma babyn shatara ta Arziki Dan ya birge kowa .

Su Aishatu nata murna har safwan ma sai d y dinga Mai godiya har sai d Abban y dakatar dashi ,su Ammy ma kayan barkan su Niki Niki ,abindai gwanin birgewa d sha’awa .

Sunyi tunanin ko NAWAL zata leko Amman shiru ,safwan ko yasan dama d kamar wuya Dan y gama yadda d cewa har zuciyar ta take son nisantar su shida iyalinsa ,hakan Kuma yamai Dadi y Kara gaskata tubanta y Kuma yafe Mata har ga ALLAH …..

NAWAL ko sai Al’amarin safwan d iyalin shi y shigo cikin tunanin ta ,sai tayi gagawar kawar dashi ,Dan Kar shedan y Bata damar d zataji wani Abu ko ta aikata wani Abu sabanin Alk’awarin d Tama zuciyarta na nisantar duk wani Abu d zai kusantata d safwan na Dadi ko sabanin Haka ,tsakanin ta dasu kawai zumunci d Alkhairi duk ta shafe komai duk d dai tirsasa zuciyar ta takeyi….

NAWAL t Gama ladabtuwa matuka ,ayanzu Abbanta d mama sune suke damunta d mgn Aure Wanda tun Bataso har t hakura taba ALLAH zabin shi akan y zaba Mata Abin d zefi zama Alkhairi a Rayuwar ta .

Kamar Wasa wani yafito Yana sonta yanada yara3 matarshi Rasuwa tayi shine ze Kara Aure yanzu kuma Babu laifi yanada halin shi Kuma Yana son NAWAL din tun Tana rejecting har ta accepting tare d hadawa d addu’a kodan faranta ran iyayenta ,ta Kuma Gama shahadar zaman Aure dashi n har abada kudinshi ko kyawunshi basa gabanta tasama Ranta kawai tsakani d ALLAH zata Aure shi ta zauna dashi bada wata manufa ba zama na Aure Mai dorewa Kuma tagama yadda d Amincewa ta Rasa safwan Rasawa n har abada ta yadda d Aishatu y Dace ba ita ba ta hakura badan ranta gaba daya yanaso ba ,….

Cikin kankanin lokaci soyayya Mai karfi ta fizgi zukatan masoyan biyu NAWAL Abdallah cikin lokaci kankani aka Fara maganar shirye shiryen Auren Dan acewar Abdallah su ba yara bane d zasu ta zaman kwasan dabgen soyayya a waje kawai ayi Auren su kwasa aciki .

Badan taso ba ta hakura ta yadda aka Gama Shirin komai n biki Babu wani bidi’a sai waleema d ta shirya Ana gobe d’aurin Auren Wanda ta shirya gayatar dunbin Al’uma Dan su tayata murna ciki harda su safwan d Aishatu d su Ammy …

Mama hankalinta kwance tanata murna yarta ta samu Nutsuwa gashi ta canza gaba daya ,shima Abba yaji dadin hakan Dan Haka fatan samun wanzajen zaman lpy d Abdallah d yaran shi kawai suke Mata Dan NAWAL har t Kama yaran Tana hidima dasu dangin mijin har ta gama cinikin su sbd so d kulawar d take nunama yaran ,Haka shima Abdallah ta sake samun gurbi cikin zuciyan shi …

 

Angama Shirin biki komai ,anbuga IV an Rabama masoya ,Abban NAWAL da kanshi yakaima Alhajin su safwan yakuma bashi hakurin duk wasu kurakurai d suka shude ,ya nemi safwan y bashi nashi da kanshi d Kara nemarma NAWAL yafiya ,safwan Abin y bashi kunya ma yace wlh y yafe Mata duniya d lahira ,cike d farin ciki d girmamawa suka Rabu …

Bayan safwan yaje gidan Ammy ,Suka Fara mgn bikin NAWAL d Alh d su Ammy har Ammy take cewa itama zata Dan har gida gayata ta mutunci tazo Mata Dan Haka komai y wuce ita har tausayima NAWAL din take Bata kwanaki har mafarki tayi safwan din yamayar d ita ,kowa nawajen yace ai d munso tuntubar shi safwan din muji ko yanada Ra’ayin hakan? To Amman yanzu komai yazo karshe tunda har ta samu wani inji su Alh d Yaya da ammy …

Safwan dai ko uffan bece ba ,Amman yanajin wani Abu cikin Ranshi …

Alh su da Yaya suka tsara yadda za’aje d’aurin Auren tare zasu tafi gaba dayan su …

Bayan safwan y koma gida y samu ankawo ma Aishatu Abin gayyata na bikin NAWAL din cikin girmamawa ,yace sai su tafi dasu Ammy shima zasu dasu Alh d Yaya , Aishatu tace insha ALLAH zamu ai komai ya zama lbr ,safwan yace hakane ……

 

Yau ne waleema da NAWAL t hada ba lefi ta Tsaru sosai ,su Aishatu d su twins d su suffaya duk sunje sun samu tarba ta musamman ,Ammy dai sai gobe zasu dawo tare dasu ,NAWAL t cikasu d kayan Rabo ta musu tarbar mutunci ,Suma sunji Dadi sunyaba d soyayyar d takema Wanda zata aura sungano hakan atare d masoyan Dan har wajen waleema sai d yazo ,yanata murna d fara’a ga kowa …

Wani Abin d y karasa shi yashiga Ran kowa fara’ar say kwarjini d ya dingama duk Wanda y ganshi a wajen waleemar ,ya birge kowa na wajen badan yaso ba Yama Amaryar sallama yabar wajen cikin raha d fara’a ga kowa …..

Abdallah mutum ne na mutane bashi d matsala d kowa ,kaifi dayane shi Akwai nuna kulawa ga Abin da Ranshi yakeso ,Dan Haka tsakani d ALLAH yakeson NAWAL d duk wani makusan cin ta ..

Bayan An watse daga waleemar cikin Aminci kowa Yana yaba Amaryar d angon nata d hango dacewar su ga kowa ,Abdallah bebar NAWAL ta huta ba y dinga kiranta har Tana tsokanar shi Kiran y Isa Haka ,NAWAL ta Kara tsintar kanta d masifar Jin so d kaunar Wanda yake Shirin zama malakinta …

Bayan komawar su Aishatu ,har labari taba safwan na irin soyayyar d Abdallah yakema NAWAL ,safwan har yaso Jin kishin Abin ,Amman ganin Babu dalili sai ma birgeshi d hakan yayi ,ya musu fatan samu dawamamen zaman lpy tsakanin su ,Amman kasan zuciyan shi Akwai wani Abu ,be Kara tabatar d hakan ba sai d y duba dp din NAWAL din d satatu d’inta yaganta d Abdallah annuri cike a fuskokin su irin n sababin ma’auratan Nan , gaskiya safwan kishi y kawo Mai ziyarar bazata Wanda be shiryama hakan ba Sam Dan bega dalilin kishin ba shikan sa ,yasha veiwing yasha haushin ganin angon kamar ze hadiye Amaryar ,sanan daga baya yaji ango ma kamar taimakon shi zeyi inya auri NAWAL din sbd ze sashi mantawa d ita gaba daya kamar yadda ta mantashi gaba daya itama,sai yaji Angon yadan birgeshi Kuma kadan ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button