HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

NAWAL kwana sukayi suna waya da Abdallah har mutane na musu tsiya wai ai gobene final day Amman suna damunsu dake Akwai Yan biki d suka Fara zuwa ,NAWAL tace abarsu su merewa Daren Shirin shiga amarcin su dake abokanen Wasa suke ,suka dinga Mata dariya har Abdallah y nemi abashi wasu suka gaisa , Abdallah mutunci iya mutunci …..

Washe gari da safe ,anata hada hada gidan su NAWAL na Shirin d’aura Mata Aure d sahibinta Abdallah…

Wajen y samu halartan dubin Al’umma da dama dake me mutane ne Angon ,su safwan d Alh su d yayama har anzo ,dake d’aurin Auren Ranar Friday ne After juma’at kowa y halarci wajen ,Sai Ango d Abokanen shi d Basu Karaso ba .

Su Ammy , twins, Aishatu,suffaya duk sun halaci bikin har Inna tazo ,sun Sami tarba ta Arziki daga mama har NAWAL d in ….

_Remaind 15mnts_ a D’aura Auren Ango na Hanya ,Babban wansu y kirashi yaji me sukeyi har yanzu Basu Karaso ba? Abdallah y dinga bashi hakuri Yana cewa suna hanya insha ALLAH Ayi hakuri ,Yana ajiye wayar y Kira NAWAL Yana cewa Kinga babban Yaya yanata fada nakusa makara a d’aurin Aure Mai cike d zumudin masoya ,tasa dariya tace to badan babban yayabane d nace kadan Kara jinkirtawa Dan jinake gabana Yana faduwa kamar wani Auren fari wlh ,Abdallah yace Kai Amaryar haka ma zakice to kin karamin himma ma Kuma ki yawaita Addu’a indai kikaji Faduwar gaban Nima ta kawai min ziyara d sanyin Safiya d na tashi d Karfin Addu’a na koreta tabarni naketa farin ciki na yanzu …

NAWAL tace hmmmm to ,Amman wlh …..Abdallah ya katseta yace Dan ALLAH kiyi kyakyawar magana mubar wanna maganar Ni in angama d’aurin Auren ma sai nazo naganki kafin Anjima akawo min ke ,Dan nafiki zumudi wlh …

“NAWAL tace hmmmm Nima inayi wlh Amman kafini din Kam ,Dan ALLAH ka kashe wayar kuyi sauri Kar babban Yaya y sake kiranka .

“Abdallah yace korata ma kike? Tace Ni na Isa? “Yace au n tuna so kike nayi sauri Dan Adaura Auren agaba Nagano ki,tasa dariya tace aa Ni karkamin fassara ,suka dinga nishadantar d junan su ,da kyar suka kashe wayar ….

 

Kowa ya halar Babu ango ,babban Yaya su Abdallah yabara umarnin a D’aura Auren tunda waliyai sun halarta ,Anfara gabartar da d’aurin Auren Kenan ………

Kiran Waya ya shigo cikin Wayar babban wansu Abdallah Wanda hakan yaja hankalin kowa na wajen dake annutsu kowa na sauraron madaura Auren.

Sai ji akayi babban wan nasu yace *Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un*.………
Be Karasa magana ba ya yanke jiki ya fad’i awajen batare d yasanar mada kowa komai ba ,kowa hankalin sa dawo kanshi ganin shi asume ga wayar tanatayi ,ganin Babu Mai Niyar D’aukan wayar sai Abban NAWAL y d’auki wayar y Kara akunnen shi ,yaji Ana sanar Mai Abdallah sunyi mumunan had’ari yanzun Nan duk sun Rasu Ana jiran magabatan su d gagawa ……. *Inalillahi wa’inna ilaihiraji’un* ne yasake futowa daga bakin Abban NAWAL d sauri wani kanin Abdallah y fizgi wayar shima yaji ,shine ma y iya tmby inda su Abdallah suke a Halin yanzu aka sanar Mai …

Abban NAWAL ne y sanar mada kowa Al’amarin d yake faruwa…

Kowa na Gurin ya kid’ima dajin Abin da ya Faru ,hatta safwan kasa motsi yayi har Alh su ,Abban NAWAL ko cewa yake shikenan ya Rasa Abdallah ya Rasa NAWAL da wacce fuska zai kaleta y sanar Mata?

Alh su safwan ne y umarci da yayi gagawan sanarwa gida a karb’e wayar Hanun NAWAL d’in Kafin Wani yasanar Mata ,Hakan Abban NAWAL yayi cikin hikima y ummarci wata k’anwar shi ta Aikata haka cikin hikima d dabaran zasuyi hoto ne d mutane ,jiki Babu kwari t Bata wayar …..

 

Shiko Kanin Abdallah harya Isa wajen d wasu ‘yan uwan Abdallah wasu Kuma sun D’auki babban yayan su sunyi Asibiti dashi jini y hau ,…

 

Shiko Abban NAWAL Alfarma y Fara nema Ga All su safwan d safwan Kan Amayar da D’aurin Auren Kan Safwan badan cimma wani burin Shiba ko nuna halin ko inkula d Rasuwar Abdallah ba !

Sai Dan k’ok’arin kwantar ma da NAWAL Wani ciwo da ze iya tasowa Dan kwanaki tayi Rashin lpy d aka dubata aka tabbatar musu hawan jinine yake barazanar kamata ,Dan Haka yayi imani d tabbas sai tafi kowa shiga tashin hankalin Rasuwar Abdallah …

Magiya d Roko Abban NAWAL yashigayi har Yana Shirin yima Alh su kuka har yasa wasu datawa shiga maganar suka dinga nunamai fa’idar Hakan indai Babu matsala ,Safwan ji yayi zai iya komai akan samuwar NAWAL d farin cikin ta yau dai Rana daya Tak tun Bayan Rabuwar su ….

Aka sake Kiran su aka sheda musu tabbas Abdallah ya Rasu yabar duniya hankalin mad’aura Auren y k’ara dugunzuma ,Atake All su Abdallah y Aminta d mayar d Auren ga Safwan har Yaya ma Yaso Haka ,shiko safwan tausayin NAWAL d marigayi mijin natane yayi mugun tasiri akan shi har yaji bazai iya jayaya ba ya zuba musu idanu ….

 

Nan da Nan Aka mayar d Auren Ga safwan Yaya yazama Waliyin Safwan ,Aka biya sadaki Aka d’aura Auren atake cikin gagawa ,Anata ma safwan fatan Alkhairi d samun lada Mai yawa akan wanan jahadin da yayi Dan wasu Basu San Mijinta bane adacan ….

Sanan aka dunguma family house din su Abdallah domin yimai jana’iza ,har su safwan din ,Abdallah y samu dunbin mutane gidan y canja daga farin ciki zuwa akasin shi kowa kuka d Al’ajabin Rasuwar Abdallah ,jikin kowa yayi sanyi …..

 

Suko gidan su NAWAL anata shagali anata cin Abinci Ana kwasan drink’s ,…

NAWAL ko tanata Jin jikinta Babu Dadi kawai dai kawar wa takeyi ..

Shiko Abban ta Yana Rasa yadda ze sanar ma mama ta fahimce shi uwa uba NAWAL d’in Gashi Dole tasani ayau dinan Dan so yake yace Mata and’aga tarewar ta ,to Amman ya zeyi d Rashin Jin Abdallah a waya d balallai taji muryar sa ba bare ya sanar Mata da kanshi ? Duk Yama Rasa Abin yi duk wanan shawar yanayine d Alh su safwan kowa kansa y kulle gasu safwan din awajen kowa y Rasa mafita ….

 

Wani saurayine yanada matsalan brain d’an yayar maman NAWAL ne yaji Ana maganar ango y Rasu awajen d’aurin Auren be tsaya an d’aura Auren safwan d nawal dashiba y sabo kafafun shi ze kawo ma Amarya jawabi Mai firgitarwa har sauri yake ,y samu tsaikone sakamakon tafiyar kafa d ya kirkiranma kansa dg inda za’a d’aura Auren zuwa gidan su NAWAL,sai yanzu yasamu ya karaso yanata neman Amarya wai yanada lbr siyarwa sai tabiya kudi ,kowa yanata gwale shi sun zata shirmen nashine y tashi ,Aiko y dinga yima NAWAL rantsuwa lbr ne me dad’i Kuma sai tabiya ,wata ‘yar uwar su ta d’auko 200 ta bashi tace munsani and’aura Aure tafi kabamu waje ….

Yace shi bayason nata sai na hanun NAWAL ,Kuma wlh bashine lbr daze bayar ba,ganin yaki tafiya yanata naci NAWAL t d’auko 500 tabashi tace y tafi t yafe Jin lbr ,Aiko yace Bata Isa ba wlh tunda ta biya kudin sai ya Bata …..

Yace _Angon Kine Dama Yayi Hadarin Mota Ya Rasu Tun Dazu_ Gaban NAWAL yayi mumunan fad’uwa tace na shiga uku fatan d zakamin kenan? Aiko yace _kwarankwasa tanatsa in karya yakeyi ta Fado mai_ d sauri cikin Jin haushin shirmen shi aka koreshi awajen y tafi Yana mita …

Anata nunama NAWAL shirmen harisu ne tamanta d zancen Amman Inna laluben wayarta ma tashiga yi Dan tabo Angon ta …

Ta aika Akarbo Mata wayarta yafi so nawa Amman aunty ta hanata har tatafi da kanta ,tayi tayi abata wayar wai sai akace ba’a Gama hotunan ba ,har aka dinga hoton da ita wai Dan adauke Mata hankali …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button