KUSKURE Complete Hausa Novel

Aunty ce tafara zargin mgn harisu sai tatafi ta Kira maman NAWAL d’aki Dan Jin ko tasan wani Abu ,tace Mata aa Kuma Abban NAWAL ma be kirata ba ,Amman Bari t kirashi Dan taji dalilin sawa a karb’e wayar NAWAL d’in….
Da yaki fad’a Mata Amman ganin sunji komai daga harisu Babu amfanin b’oyewar kawai y Gaya musu ………
Itako NAWAL t kasa hakura d son Jin muryar angonta Dan Haka ta sake biyo aunty inda kunuwanta suka Mata mugun ji …….
Ji tayi mamanta nacewa *Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un* Abdallah! Rasuwa? Amman akamana shiru?………….
Basu Ankara ba sukaji NAWAL ta kwala wani uban k’ara shi kanshi Abban nata yaji k’ararn atake ta zube sumamiya awajen,mama tayar d waya suka nufi Kan NAWAL d gudu suna ambatan sunan ta …..
Jin shiru yanata mgn Babu amsa ,yasa Abban yasan Babu lpy yayo gida cikin tashin hankali Bayan ya sanar ma da Alh su safwan gida Babu lpy ,Suma hankali atashe suka rufo Mai baya ……..
*Maman shaheed*????
[6/3, 7:19 AM] Mmn Shaheed: ???? *WRITING*????
BY
“`MAMAN SHAHEED“`
???? *ROMANTIC WRITER’S ASSOCIATION*????
*KUSKURE* ????????_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)
_shafi n saba’en da Tara_(second to d last)…..
Ko Da su Abban NAWAL suka karaso ,Kan NAWAL cike yake da mutane ,kowa n tausayama NAWAL d yaji abinda y faru harsu Ammy d Aishatu tamatukar Basu tausayi gata a sume …..
Anyi iya kokari a gida ganin ta farfad’o Amman Abu yaci tura Dole aka dangana d asibiti d ita Dan ba karamin tausayi taba Yan taron bikin ba ….
Shima gidan su Abdallah ,hankali y dugunzuma ankawo gawar shi ,Nan kowa sai kuka d kuka ,anata Mai kyakyawar Addu’a….
NAWAL dai taimakon gagawa aketa faman Bata ,yayin d gidan biki y koma n makoki d zaman jingun _jingun ,Dole tasa Alh su safwan Yama su Ammy mgn su Zo su tafi gida ,haka Ammy Tama ‘yan gidan sallama tunda mama n wajen NAWAL ,su Aishatu gaba dayansu gidan Ammy d matsanaicin NAWAL far zuciyar su …..
Bayan komawar su gida ,Alh su safwan y Tara su gaba dayansu ya Fara musu nasiha d nuna musu duniya b gidan zama bace Abin d y faru Kan Abdallah zai faru Kan kowanen su ,sanan Haka Wanda y faru Kan NAWAL zai iya faruwa d kowanen su dg cikin matan ,yadai musu wa’azi d nuni akan Rayuwa d karsu d’auki wani Abu su dasawa Ransu akan Abin da zasuji dg gareshi yanzu ,su d’auka Abun d sukayi shida safwan d Yaya kamar jahadine tunda NAWAL macece Yar uwarsu ,karsu dubi *KUSKURE* ta n baya kawai su fuskanci gaba ,suyima Abin kyakyawan zato.
y Kira sunan Aishatu y dinga Mata Addu’a d nasiha d samata Albarka ,y nuna Mata Yana Alfahari d ita Kuma y dauketa yane b surika b ,Dan bai d matsala d ita baya fatan ko Nan gaba y samu ,y gama kashe Mata jiki d zuciya d dad’a kalaman say nasiha d bata kimar sirkanta …..
Ya cigaba d bayani akan ,mayar d Auren safwan d nawal ,amemakon na Abdallah marigayi d nawal .
Kowa y firgita d mamakin Abin da sukaji dg bakin Alh su ,sabanin Aishatu d ko motsi t kasayi sai tausan zuciyarta d take tayi ,safwan ko duk idanun shi d nutsuwar shi yanaga Aishatu ,ji yaje kamar yaje y rungumeta y lalasheta duk d y kasa gano irin yanayin d take ciki ….
Nan dai Alh yayita ma safwan nasiha d riko d Adalci ,Yama Aishatu fatan Alkhairi d samu dawamamen zaman lpy cikin gidan safwan d zaman d zasuyi d nawal y nuna Mata duk t manta baya t d’auka tarihini Wanda y gabata …
Ammy ma tama safwan fada sosai d nasiha ,sanan Tama Aishatu nasiha d Addi’o’e masu sanyaya zuciya d ragema mutum zafin kishi ,tajata jikinta Tana nuna mata ‘ya ta d’auketa b surika ba , Aishatu taji dad’in kulawar d kowa y Bata ,Amman sakamakon Raunin d muryar ta tayi takasa furta uffan ,sai gyada Kai alamun taji tayi naaam ,kowa y dinga musu fatan samun saman lpy d yalwartan Arziki …
Alh d Ammy sun bar parlour ,ganin dagasu sai su yara a parlour sai safwan y bukaci ganin Aishatu ,Koda suka kebe ,Taki had’a Ido dashi Sam ….
Sai d y rungumeta y dago habarta y manna Mata wani zazzafan kiss Mai cike d k’auna d rarashi ,sanan suka had’a Ido ,sunjima a Haka kafin y zaunar d ita Kan kafafun shi ,Yana Mata tausasan kalamai d sigar rarashi d ban Baki d Bata hak’uri Akan yadda d dawo d nawal d yayi ,gani yake kamar zatace be kyauta ba ….
Bayan y gama duk wani salon sa ,y nemi yaji ta bakin ta ,cikin tatausan lafazi tace Alh y gama magana , ALLAH y Basu zaman lpy dawamame ALLAH y kad’e fitina y bashi ikon yimusu Adalci ,duk k’ok’arinta na ganin hawaye be zubo ba ,Amman muryarta tayi Rau’ni sosai ,Dan daga bayama kasa mgn tayi ,cigaba d rarashin ta yayi harda Alkawura ya dinga Mata Akan Yana tare d ita har karshen Rayuwar tasa Haka a Ranta ,Kuma Akan NAWAL beze taba tozartata ba ko rage wani Abu daga cikin so d k’aunar d yake Mata Mai tushe ,Kuma kartace ma su Abbanta komai shi zaije d ita sumai bayani na fahimta har yanzu Inna ma ,duk dai y gama kalalameta ….
NAWAL dai d kyar t samu t farfad’o burinta tayi tozali ko da da gawar Abdallah ce ,hak’uri mama d Abban ta suka dinga Bata , tace ita Sam Addu’a kawai zata Mai b wani Abu ba Dan ALLAH karsu hanata yimai Addu’a abinda zai shiga tsakanin su dashi nefa n k’arshe sumata wanan Alfarmar ,Haka d saka bakin Dr aka nufi gidan su Abdallah d ita lokacin d yayi daidai d angama salatan Abdallah za’a tafi dashi makwancin shi …
‘yan uwan Abdallah suna hango Abban NAWAL d su NAWAL d’in sai sukazo ,Nan Abba y musu bayanin su taimaka NAWAL Tama Abdallah Addu’a karshe d ze shiga tsakanin ta d gawar sa ,Aiko aka Bata izini aka Dan bude Mata shi hawaye n sharara ta k’uramai Ido kirrrrr….
Su duk ji suke ta gama tawakali t hak’ura ,Addu’a take Mai ,itako ita kad’ai tasan Abun d take tunowa d Abdallah Yana Raye ,tasake bude Mai fuska d hanun ta ,sai taga kamar Yana motsi ,afirgice tace Abba y motsa fa ku bincika sosai …..
Ganin kamar kizo yake Mata ko Kuma gawar n neman zautar d ita ,Abban y umarci d su kaishi makwancin shi n gaskiya ,Aiko NAWAL t Fara cewa ,Abba Dan ALLAH ku bincika ko ku kaishi asibiti Ni na bincika d kaina Abdallah be Mutu ba ,ganin anufi mota dashi har sun tafi ,ita Kuma anata k’ok’arin sata cikin mota ,t sulale t zube sumamiya a wajen Dole Abba suka karasa sata a mota suka koma asibiti….
Assume aka karbeta ,d taimakon ALLAH d na Dr ta farfad’o tanata sambatu ,sai d aka Mata wata Allura sanan t samu bacci Wanda y kaita har anan zata kwana …
Suma safwan d su Yaya d twins duk sunbar gidan Ammy kasancewar dare yayi ,safwan ko numfashi Aishatu ta fitar sai y Bata kulawa ,Koda suka Isa gida ma Nan Nan y dingayi d ita d babyn ta ,Yana Mai Bata wata irin kulawa ta musamman ,ganin kamar hankalin ta be kwanta ba ,ya sake dawo d mgn Akan kartasa komai cikin Ranta beyi d wata manufa ba t d’auka jahadin ne kamar yadda Alh su yafada Mata ,Aiko y tsinkar Mata d zuciya sai kuka y kwace Mata ….
Hankalin maza a tashe ya nufo ta y Rungume murya cikin Rau’ni d salon rarashi y dinga aikin rarashi d zafafan kalaman lobayya ….
Kwana yayi Yana aikin rarashi y manta Alh y bashi umarnin tuntubar halin d nawal take ciki ma kafin gobe Dan tanada haki Akan shi Dan matar shice,Inna Aishatu ce kawai a gaban shi y manta karatun Alh ….
Washe gari ma dai jikin NAWAL sai addu’a….