KUSKURE Complete Hausa Novel

Safwan y samu y shawo Kan Aishatu d kyar ,har yace ko office bazeje b ,Amman Aishatu tace Dan ALLAH ya tafi ta Rungumi kaddarar ta komai zai daidaita ,Aiko d taimakon ta y shirya tamai rakiya cike d k’auna ya tafi …
Akan hanyar shi ta tafiya ,Alh su y kirashi Yana tmby jikin NAWAL ,ya Rasa amsar bashi ,sai yayi karya d cewar jiya be samu layin NAWAL ba ,Amman yanzu gashi a hanyar asibitin ,Alh yace to inyaje y sanar Mai d yadda jikin yake.
” yace toh Alh” Dole y juyar d akalar tafiyan shi office to hospital ,Koda y Isa NAWAL nata bacci Yama Abba d mama y mai jiki ? Suka amsa d cewar d sauki ,y musu Addu’a ALLAH y k’aro sauki ,sukace Ameen ,ya basu uzirin zai wuce office anjima zai dawo amata sannu inta farka ,sukamai fatan Isa lpy cike d yabawa d kulawar d nawal ta Fara Sami daga tsohon mijin nata d suka yanke tsamani daga gareshi .
Wuni safwan yayi Yana waya d Aishatu ,itama hakan ya Mata dad’i mace nason kulawa Dan Haka tayi Alk’awarin bashi hadin Kai wajen samun kwanciyan hankali cikin gidan shi Koda NAWAL ta shigo ..
NAWAL wuni t k’arayi cikin asibitin Ana kula d ita har yamman safwan be dawo ba …
D yamma safwan y koma gida yaci Abinci y huta yace t shirya zasuje gidan aunty zainab d gidan Inna ,tace to ta gama shiryawa tsaf…
Bayan sun Fara Isa gidan Inna ,safwan duk y koramata jawabin mayar d Auren shi d nawal ,Jin duk abubuwan d suka faru ,Inna Bataso kanta ba tamishi fatan yin Adalci a tsakanin su d samun zuriya d’ayiba ,yaji dad’i matuka ,Inna tayimusu fad’a na gaskiya shida Aishatu ,sanan ya mata Alkhairi n kud’i suka nufi gdn Abban Aishatu.
Suna Isa ,Haneef y dinga murna yaga iyayen shi yace tare zasu tafi ma ,ganin rigimar Haneef bazata k’are ba ,safwan y fara gayama Abban Aishatu abinda y kawo su ,shima dai nasiha y k’ara yi musu d tinama safwan yin Adalci tsakanin su d samawa gidan sa kwanciyan hankali,sosai y Mai nasiha ,aunty zainab ma t k’ara d nata ,duk sunji dad’i musamman safwan d ALLAH y had’a shi d surukai masu datako mutunci iya mutunci …..
Haneef dai sai d y buying iyayenshi ,suna hanyar komawa gidane sunka tsaya siyan kayan motsa baki , Aishatu take tmby safwan y jikin aunty ta nawal ?
Sai d yaji wani iri aransa ,kafin y Bata amsa d ,to d sauki za’ace Dan wlh naso zuwa n dubata a Daren Nan Amman gashi n gaji Kuma Kinga gida zamu koma d munbiya .
Aishatu tace me ze Hana indai gajiyar taka Bata habaka tuki ba ai har ma lek’a mufito Ina ganin..
“Yace kina ganin mubiya kin amince Babu komai my Ayush? Taji dad’in sunan tace eh’
Sai y juyar d akalar motar suka nufi asibitin ,Koda suka shigo room d’in zaune suka samu NAWAL d mama a kusa d ita Tana cin Abinci mama n Mata nasiha Mai ratsa zuciyar duk Wanda y saurara ….
D fara’a mama t Basu kujera suka zauna ,itako Aishatu a gadon t zauna kusa d nawal Tana Mata y jiki d gaisuwar Abdallah ..
Safwan ma y gaishe d mama y Fara yima NAWAL y jiki cikin ladabi d girmamawa take bashi amsa harda godiya d take Mai Wanda dagashi har Aishatu sun Rasa sanadin godiyar ..
NAWAL t karbi babyn hanun Aishatu ,t kamo Haneef Tana Mai Wasa Haka y faranta ran kowa n wajen,NAWAL t dinga Jan Aishatu d Hira cikin sakin fuska d walwala har mama ma Tana sa musu Baki cikin hirar ,har safwan ba’a barshi bayaba kowa dai na wajen Yana cikin farinciki d hirar d yanayin d yake gudana a wanan lokacin ,baran NAWAL ji tayi kamar su kwana a asibitin …
D sukace zasu tafi safwan y barsu Leda daya ,y masu ALLAH y Kara sauki ,NAWAL t dinga ma Aishatu godiya d fatan Isa gida lpy cikin yabawa d kulawar d suka Bata ….
Mama d’orama NAWAL tayi d nasihar Bata fasa ba ,har sai d nawal tad’an zubar d kwala ,da Gama Gane cewa duniya kasuwanci ce Abin cikinta ko hajace ,Kuma duk nisan gona Akwai kwunyar karshe ,tayi Alk’awarin samar d wanzajen zaman lpy cikin gidan safwan d zama d Aishatu d Amana Kuma zuciya 1.
Bayan isar su Aishatu gida safwan y dinga yaba Mata d kumbura Mata Kai wai tun yanzu ta Fara aikinta na gyara Mai gida ba’asan ma gaba ba ,Bari y zuba Ido ya gani …
Taji dad’i ta k’ara lasan takwabin tabatar d zaman lpy a tsakanin su ….
Washe gari aka sallami NAWAL..
An yanke mgn tarewar NAWAL Nan d sati 1 All d Abba ne suka yanke angama shirya komai , Aishatu n wajen NAWAL nada Dan yafi girma ,ita Kuma NAWAL yanzu t koma wajen safwan din ,kowa y yadda d hakan Kuma …
Safwan dai ko nunawa Yana d’okin tarewar NAWAL d’in bayayi ,Amman ita Aishatu hankalin ta kwance tanata cewa ta kusa samun aunty ta gama sawa ranta ,Noor ma tanata murna d dawowan momynta Amman still tace Aishatu ce babbar mamata ….
Yaune tarewar NAWAL ,ba wani taro akayi b safwan y Hana ,NAWAL t Sami sauki sosai ,lpy ta shigo gidan Babu hayaniya cikin Aminci d mutunta juna ….
Safwan dai yanata Nan Nan d Aishatu kartace wai yana rawar Kan tarewar NAWAL ,Bayan sun had’u a parlour sunyi Addu’a samu saman lot d had’uwar Kai ,sukaci Abincin d Aishatu t shirya musu lafiyayen girki , NAWAL t dinga Santi Tana cewa tayi missing girkin Aishatu indon ta adacan baya ,suka sa dariya , Aishatu tace Indo ‘yar Aikin NAWAL ba ,tasa dariya …
NAWAL t toshe Mata Baki tace Dan ALLAH karta k’ara fad’en Haka Aishatu take yanzu maman su Noor ,subar abinda y wuce ,safwan ma yaji dad’in yanayin d yake gudana tsakanin shi d matan nashi indai haka za’a zauna zai kasance cikin farinciki d annushuwa Mai d’orewa….
Noor a jikin momyn ta d haneef sukayi bacci , Aishatu d safwan ne suka d’auke su suka kaisu d’akin Aishatu Dan suyi bacci ,Bayan safwan y kwantar dasu , Aishatu tamai sai d safe ,y Fara cewa harda korata yau?
Tana dariya tace har d turaka ma in baka tafi ba yaude Kam ,ga aunty na can yau filin nata ne ,yadawo y zauna kusa d Aishatu yace naki tafiyan ,sai nagama hirata , Aishatu tace rufani ka sayani ,Dan ALLAH our one tashi katafi kaji ? Yace Inyeeee har ancanja min suna? Tace eh Mana ka zama b nawa Ni kad’ai ba ai ,Aiko safwan yace kinaso mu Sami sab’ani Ashe ke daban ita daban wlh ki canja maza kafin Rai y b’aci ,ganin da gaske yake tafara bashi hak’uri to my one and only yama ? Yayi murmushin yace eh tace plsss katashi kaje b korar ka nake ba kafi kowa sani wlh banking n kwana n wuni dakai ba cikin jikina ,kawai dai…….Bata karasa ba ,yace kawai dai kin rage Sona?
Tace wani ,wlh inason ka kamar yadda kake adacan Babu canji .
“Yace to ngd ,barin Baki n sallama tunda kin hanani zama .
Ya manna Mata wani …….ta kyar t kwace t sa shi gaba har wajen NAWAL ta musu sai d safe ta juyo zuciyar cike da Abun d ba’a Rasa ba
[6/7, 1:16 PM] Mmn Shaheed: ???? *WRITING*????
BY
“`MAMAN SHAHEED“`
???? *ROMANTIC WRITER’S ASSOCIATION*????
*KUSKURE* ????????_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)
_shafi na tamanin_
(The last page)
*For happy sallah once again*
*ALLAH ya maimaita Mana ya kaimu na bad’in bad’ada muna masu Rai d cikakiyar lpy*
*GODIYA MARA ADADI GA DUBAN MASOYANA MASU BIN NOVELS DINA ,ALLAH YABAR SO ,INA SON KU TSAKANI DA ALLAH NIMA ALLAH YABAR K’AUNA*????????????????
Aishatu ta na komawa d’akinta ta gabatar da safa’i d utiri tayi Addi’o’e samun zaman lpy d Adalci daga mijin su safwan d neman kariya daga mahasada .
Bata tsaya dogon naxarin d shed’e yaketa k’irk’iro Mata ba bare yaci galaba akanta ,ta yi k’ok’ari Tacire komai a Ranta ta kwanta kusa d yaranta Bayan ta tofe su da Addu’a,itama Tama kanta ta kwanta cikin Aminci d kawar d duk wani tunani ko zargi .