KUSKURE Complete Hausa Novel

Safwan dai ji yayi wani iri wai yau shine d nawal amtsayin miji d Mata ? Yayi k’ok’arin K’aryata kanshi Amman inaa! Gaskiya ta Kori k’arya ,gani ma y Kori ji , tabbas Haka Abin yake ….
Itama NAWAL ji takeyi kamar a mafarki ,wai itace d safwan? Tana cikin tunanin taji muryar safwan n Bata ummarnin d kwanta shi sai y watsa ruwa ,ta amsa d to ,Bayan t rage kayan jikinta ta yi Addu’a ta kwanta .
Bayan safwan y watsa ruwa y dawo ji yake kamar ba daidai yake ba ,duk guje gujen shi d kame Kamen shi dai d’akin NAWAL dai shine wajen kwanan shi yau ,ganin Babu sarki sai ALLAH kawai y Samu gefe y d’ofana ..
NAWAL ma kusan hakan dad’i yamata ,ganin bece Mata komai ba ,hakan y Bata damar tsundumawa kogin tunanin Abdallah ! Abu yaso y dawo Mata sabo tayi nisa cikin tunanin shi ,ga wani kuka Mai sauti da y Fara fita daga gareta Wanda batasan Yana fitowa ba ,safwan tun Yana ganin zai iya daurewa yaga Ina Dole y magantu .
Koda y Kira sunanta kusan so 3 sai Ana 4 t amsa cikin muryar kuka ,ya tmby ba’asin kukan ,Amman ta kasa furta uffan ,ganin kukan na gaske ne yace ko shi yamata lefi?
“Tace aa ,Babu komai” ganin Bata d niyar fad’en matsalar ta yasa y d’an fuskanci ko mijinta ta tuna ,sai yaji wani gajeren kishi y taso Mai ,besan lokacin d y Fara rarashinta ba har Yana janyo ta jikinshi batare d neman shawarar zuciyarshi ba ,y Fara Mata mgn akan indai ba mijinta me Rasuwa ta tuno ba to tayi shiru ,in Kuma shi take tunawa tacigaba d kukan Amman tasan Abin d take aikatawa be halata ba……
Ganin ya doshi gano matsalata sai ta tsaida kukan cak ,ta bashi hakuri ta nuna Mai ba mijinta t tuna ba ,Jin furucin t y umarci d to tayi bacci ,Haka bacci Mai cike d sark’akiya y kwashe su …..
Washe gari Koda suka tashi , safwan shi y Fara tashi yaje y tashi Aishatu domin ta gabatar d sallah asuba ,Bayan Nan y wuce masalaci …..
Kafin safwan yayi wanka ,NAWAL ta tashi a bacci , Aishatu ta gama Kamala komai na break d’in su ta jera shi su kawai take jira..
Koda safwan y gama shiryawa y tashi NAWAL ,sanan y wuce d’akin Aishatu y samu su Noor anata bacci Aishatu kuma Tana wanka sai y tsaya jiranta .
Bayan ta fito ,ta gaishe shi cikin girmamawa d biyaya sanan tace insun Gama “breakfast is ready “ya bude Baki Yana mamaki ,yace bazaki Bari NAWAL tazo kuyi tare ba ?
Nan y Fara nuna Mata ,shifa b irin safwan din dacan bane d nawal take barinta d Aiki ,Dole ne ta dinga shiga kitchen kamar yadda kike shiga kema Bata Isa ta barmin ke Aiki ba kulin ,in ba hakaba sai dai anemo Mai Aiki ..
Aishatu tace badai a gidan ba ,ayanzu dai sbd aikin mu be Mana yawan d zamu nemi taimakon wata ba ,sai dai idan aunty nace tace ka Nemo ta ,yace wa! Ita yanzu har zata iya kalo na tace n Nemo Mata me Aiki?
Aishatu tace meze Hana in tanada ra’ayin Haka!
Safwan yace to , ALLAH yasa tanada Ra’ayin hakan kiga yada karshen films d’in ze kare ….
Aishatu tayi murmushi tace dadyn Noor ban sanga d Rigima ba pls karka canja ,to me Kar kace Mata ta dinga shiga kitchen don tayani Aiki Dan ALLAH badan Ni ba ,ka barta ka gani ,inta shiga d kanta yauwa kaga cewa tabbas ta Kara canjawa kenan tunda Babu wani Abun boyewa tsakanin Ni da Kai d Kuma farin sani d muka Mata ,Amman bana zargin ta na tabbatar maka ta canja daga sanin d muka Mata adacan ba ,jikina y bani ,wasu abubuwa d na gani nake k’ara hangowa atare d ita ya tabatar min d hakan insha ALLAH kaji dadyn Noor kamin Alkawari?
Yayi ajiyar zuciya yace shi kenan ,Dan Haka nake son ki my Ayush ,y rungumeta ta kwace ,yace ze zuba Ido na wani lokaci ,tace to tagode …..
Parlour suka fita gaba d’ayan su Bayan sun zauna ,NAWAL t fito cikin shiri cikin girmamawa d son zaman lpy ta Fara gaishe d Aishatu .
Aishatu t amsa cikin girmamawa itama ,suka nufi wajen break acan NAWAL take cewa bataga yaranta ba ?
Aishatu tace suna can kinsan su d dogon bacci ,so nake su tashi na musu wanka su karya ,kafin Nan nagama nawa Karin …
Ganin Aishatu ta Kamala komai d sasafe n break ,NAWAL t Fara cewa , Aishatu yanzu fa ba da bane ,da ya wuce mu manta dashi plsss mu fuskanci gaba cikin Amana d Aminci d taimakon juna d son zaman lpy a cikin gidan mu d zuciyar mijin mu Abin Alfaharin mu ,Dan Haka ban yadda ki dinga shiga kitchen ke kad’ai ba plsss ki Bari mu dinga gudanar d komai tare ,Dan ALLAH Ina neman wanan Alfarmar a gunki ta had’e hannu biyu Alamar Rok’o ..
Aishatu ta Kama hannu nata ta saukar Mata tace ,angama raki shi dad’e ,naji dad’in kalaman ki ,Baki d matsala daga gareni insha ALLAH.
NAWAL tayi murmushi tace ngd.
Aishatu tace nice d godiya .
Shi ko safwan dad’i ne ya cika birnin zuciyar shi ,Jin anzo mgn Aishatu d tuni yayi gajan hak’uri d be cimma manufa ba ,Dan Haka y sake musu wasiya d zaman lpy d hakuri d juna d zaman Amana ,duk suka Mai Alk’awarin bashi d matsala insha ALLAH .
Koda su Noor suka tashi ,tare d nawal aka musu wanka suka shiryasu ,safwan n ta farin ciki d hakan Abin d be Saba gani ba ga NAWAL ..
Har ya tafi office y dawo y sane su a kitchen tare suna gudanar d girkin dare suna Hira cikin Raha d fara’a su Noor sunata wasan su Suma …
Haka yanai dad’i Dan Haka tare sukaci Abincin ma ranar …
Bayan sati 2 gidan safwan Abin gwanin ban sha’awa Yana sauke halin dake kanshi ,Kuma yaran shi suna samun kulawa matuka daga iyayen su gaba d’aya ,Noor tare suke zuwa school d haneef an sashi shima ,wani lokacin NAWAL ta shiryasu wani lokacin Aishatu ta shirya su ,girki ko tare sukeyi kulin sunki yadda araba kowacce taba k’ok’arinta akan mijinta ,so yanzu safwan y Sami happy family…..
Ranar safwan ya d’ebe su sukaje gidan Ammy suka gaishe ta cike d tsaraba d nuna kulawa irin n surukai d surika ,sanan suka wuce gidan Inna itama d tata tsarabar tanata shimusu Albarka Tana yavawa d zaman nasu ,sanan suka wuce gidan aunty zainab itama d hidimar d suka Mata ,Nan ma ta musu nasiha d Jan hankali ,ta Basu abubuwa na gyaran Aure gaba d’ayan su Babu nuna banbanci ,sunata godiya suka nufi gidan maman su NAWAL ,itama tayi farin ciki ganin su d tata tsarabar ,har Abban NAWAL dake Yana gida yaji dad’i y dinga shima safwan Albarka d Addu’a Yana nuna farinciki shi afili sanan suka nufi wajen Shan ice cream suka Sha suka danyi siyaya d ummarnin mijin su sanan suka dawo gida cike d farinciki d ziyarar d mujin ya kaisu
Haka Rayuwar Gidan safwan ta dinga kasancewa Babu hayaniya bare tashin hankali ,NAWAL ta bala’en ladabtuwa duniya ta koyar d ita darasi me wuyar mantuwa Dan Haka Babu fada ko kishi fili tsakanin ta d Aishatu ,gashi suna Jan yaransu ajikin su , Aishatu tanata kasuwancin ta ,NAWAL ma ta koma wajen ai d kyar d sa bakin Aishatu Dan da tace ta Dena kwata kwata duba d irin taimakon d Al’umma suke samu t hanun ta shine t koma d amincewar safwan ,Amman kulin Bata barin gidan sai tayi wani Abu na Aiki ko shiga kitchen ko yima yara wanka ta shiryasu ta wuce dasu school Haka dai kulin take cikin hidima d gida inta dawo ma ta karbi duk Abin da taga Aishatu ta karasa ,sosai takeyin hidima Babu kyashi ko son jiki d lalaci irin na can baya ,real NAWAL ce yanzu .
Kowa yanzu bashi d matsala d nawal ,ta mugun canjawa ita kanta tafijin dad’in Rayuwar ta tayanzu ta dawo ga mijinta ta Kuma tuba daga KUSKURE d ta tafka tun kafin shud’ewar Rayuwar ta , ALLAH ma muna Masa laifi y yafe Mana d Babu yafiya a duniya d jama’a da dama Basu shaa ba .