HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Yace yeess kece , ko kinada Abin yi ko karya nayi NAWAL!?

rass! rass! Taji kirjin ta y amsa ,rabon d y ambaci sunan t har t manta tun tanada ciki y canja Mata suna zuwa mommyn unborn Amman yau Abin yasha bam_bam..

Cikin bacin Rai d hucci y fice y bar Mata room d’in y koma nashi dama y biyotane , maybe yanaso y d’an kare yawa saboda tsaro badan tsoro ba ,kunde gane ,toh t Bata Mai Rai y hadiye abinsa y koma nashi daki Yana shiga yasa key.

 

Haka aka barta d lissafi , cikin mutuwar jiki t tashi ,ta d’auki Noor takaishi d’akin su , sanan ta d’au Haneef taje t kwantar dashi kusa d Noor ,sbd bacin Rai Tama manta ko addu’a Bata musu ba (sakaci d shirme ,kiyayewa ai yafi Allah na Nan)

Yara under 5 yrs a d’aki su kadai …

Ranar kwanan bacin Rai tayi , gashi tanason Jin dumin mijin ta matuka ,ga girman Kai Yana addabarta , bare taje t nemi sulhu , Abin takaicin Taki yadda tayi *KUSKURE* haka t kwana cikin zullimi d tunani dakyar bacci y Dan dauketa harda mafarkai ta dingayi …

Da safe , Indo d su twins suka tashi suka shirya komai na break , cikin kwarewa d birgewa , dake d wuri zasu fita zuwa gdn Ammy Dan yau acan zasu kwana ma ,Dan yau d’aurin AURE da dadare Kuma za Ayi dinner wacce ta gaji d had’uwa …

Safwan d NAWAL dai sama _sama ake ,Amman sunki Bari jama’ar gdn su gane hakan .. .

Sunyi break lpy , Dady su Noor y koma bedroom d’inshi ya fesa wanka yaci wata d’anyar galila Mai ruwan Zuma tanata kyali Riga d malummalun adon malum malun din iri d’aya d hular kanta takalmi d agogon sa masu tsada ne ga wani zoben azurfan sa sheki yakeyi ayatsan sa ya feshe jikin sa d turaruka sunkai 4 Yana Shirin fita Dan barin gidan ..

Momyn su Noor ta shigo d’akin , har y gotta ta ze wuce ta Sha gaban shi , ya tsaya , cikin narkarkiyar murya ,tace dadyn Noor wai meye haka?

Y kalleta ,yace d akayi me?

Ta ce , Abin d kakemin Mana? Yace me nayi Miki ?
Cikin shagwaba tace Kanata wani shareni hakama jiya kaki kwana…….sai kuka y kwace Mata t fad’a jikin shi Tana shashekar kuka..

Abin ka d masoya ,tuni yaji kukan har cikin ranshi ,gashi y tsani kuka arayuwar shi , Dan haka besan San da y matseta a cikin jikin shi Yana Dan dukan kafadun ta d shafa Bayan ta ba Alamar rarashi …

Jin taci gaba d narkewa kamar zata kule kirjin shi ,yasa y talabo ta Yana cemata tayi shiru , t Mai bayani …

ta yadda tayi lefi ,haka t d’ago da kyar ta Fara bashi hakuri , cikin lokacin kankani , yace y wuce ta dinga kula d kanta d hidiman iyalin ta ta gyara Rayuwar Auren su Dan Allah , tace insha Allah dadyn su Noor …

Shikenan komai y canja ,ganin zata Bata Mai kwaliya y dagota y Bata tissue yace t goge dg baya ma y karba y goge Mata hawayen , gudun Kar t shagalar dashi gashi y gama shiri ,ya lalab’ata , yace zasuje gun d’aurin AURE Kar t makarar dashi ,se sun had’u gdn Ammy ,cikin birgewa da matsanaicin kewar juna suka rabu tamai rakiya har bakin mota, ji tayi kamar ta bishi haka t dawo bedroom dinta dan ta gama nata Shirin ..

Su ko su Noor d Haneef tuni Indo t gama musu wanka t gyara su tasan aikin tane , ussaina Kuma t sa musu Kaya t gyara su …

Huzna,suhaima,Asmy,hassana,usaina,duk sun gama shiri sun tsantsara kwaliya t agani ayaba , kafin suje gdn Ammy me kwaliya t sake tatso musu kyan su in zasu canja Kaya ..

Indo ma tayi wanka ta saka material d’inta d’inkin rariya Mai Shan 0 dinan tayi kyau b lefi kayan d su twins suka Dinka Mata Ankon dinner shiko ta sashi a Leda se a gdn Ammy zatasa ….

Koda suka fito gaba dayan su Dan tafia , momyn Noor d huzna d suka ga Indo seda sukayi mamaki ,suka San Ashe kwaliya d kowace mace dacewa yakeyi Amman Basu yaba ba …….

Suka nufi inda driver yake , suka shiga y jasu sai gdn Ammy uwar ango kakar su Noor……

 

*Maman shaheed*????
[12/28, 7:01 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`BY MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)

_shafi na shad’aya_

 

*KIYAYEWA AI YAFI ALLAH NA NAN*…
“`means“`
_ka Fara kiyayewa akan komai yafi kace Allah Yana nan_

_ka Fara taimakon kanka kafin ka nemi taimakon Allah_

“`duk Mai tsokaci ko tmby akan novel Dina k’ofa a bude take“`????

 

“Isar su gdn Ammy , lokacin gd y d’inke d jama’a ‘yan uwa da abokanen Arziki anata Shirin tafiya d’aurin AURE”

 

“Bayan sun gama gaisawa d baki maza d sukazo daga garuruwa har ma na cikin garin ,sai suka wuce ciki.

“Nan ma gaisuwa suka shiga yi, anata raha kowa ka kani cikin farin ciki yake fuskar sa cike d annuri ”

“Suna gama gagaisawa ,suka Kama shirye _shiryen abubuwan d ‘yan d’aurin AURE zasu buk’ata Kama d su Abinci , snacks , drinks, duk d oder wasu aka bayar ,wasu ankawo wasu Kuma ba su karaso ba …

Gida y cika yayi taf , a haraban gdn ansa canopy chairs ..

“Bayan An d’aura Aure , Ango bakinsa har kunne, shida abokanen sa suka dungumo zuwa gd , kusa d gdn su Ammy y shiga d jama’ar sa dake Akwai abokin sa gdn Kuma sun Saba sosai ,gdn Ammy sai ya barma baki d su Abba d ….

Ango yayi kyau y ci d’anyar galila shi shima kusan irin d’inkin su d’aya d k’anin shi SAFWAN.

“Tun shigar su gdn , momyn su noor take sa Indo Aiki , ko Abu taga an zubar ko Ana neman Wanda ze gyara wani Abu duk d Akwai masu tayasu Aiki amman sai tace g Indo , har wani uban wanke wanke tace wai taje tayi sai d akace aa ta Bari Akwai masuyi sanan t hak’ura badan ranta yaso ba …

Gashi t turo su Noor wai t dinga kula d shige d ficen su t sakar Mata komai har kayan d zasu canja indon taba bag clothes din nasu wai d sun Bata t cire t canja musu , Indo ba yadda ta iya haka t karba take t fama.

 

“Anata faman yawo d snacks , drinks, swan, ga girki anata kwasa ‘yan d’aurin AURE sun dawo , anata wulakanta kaza d Naman rago harma na saa ranar nama sun gane kuren su …

Hidima yayi hidima , indo ta bace ma ganin momyn su Noor Dan inba haka ba bazata barta takai ko lomar Abinci bakin ta ba ,Amman Tana kula d movement d’in su Haneef ,amnan ko da wasa Taki yadda su zauna inuwa d’aya d momyn su , gashi su hassana Basu Sami zama ba bare su dinga tare Mata wani wahalan idan momyn su Noor t jefo Mata Dan haka Indo t shiga wasan buya d ita Dan t samu t huta itama ..

Wuni akayi Ana ciye-ciye da shaye-shaye Amman n drinks fa , har yamma ta gabato aka Fara mayanar dinner d za a gabatar da daddare .

Indo ta canjama Noor d Haneef Kaya kusan 4× sha’anin su kawai suke yi ,abinka d yaro …

Su hassana,ussaina,Asmy,suhaima,huzna sun Sha makeup sun canja Kaya Suma kusan kala 3 3 ,sun Sha kyau sosai ..

Magriba tayi ,wasu sunyi sallah wasu ko bansan yaushe zasuyi ba (Dan kunsan Akwai masu kara’in sallah abiki “wa’iyazubillah”Kar kwaliya t goge Allah yasa mugane ) Dan haka su hassana anyi sallah Dan basa wasa d sallah Sam Ammy Bata musu d wasa kwatakwata training din d t musu Kuma yabi jikin su ..

Bayan idar d sallah magriba duhu y fara shiga , alokacin me kwaliya t sake baje makeup kit d’in ta Dan tsantsara musu wata sabuwar kwaliyar Dan Shirin tafiya dinner ko isha’i ba Ayi ba ,wasu dai sunce d alwalar su atare dasu sallah kawai zasuyi su tafi ..

Momyn su ita aka farama kwaliya inda taci wani uban codelece d’inta Mai tsada d matukar kyau ,head d’inta ma yayi kyau jaka d takarmi masu tsada Suma d’ankune d Abin hanu g zobina masu kyau t cika Jakarta d kudin liki sababi fil ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button