KUSKURE Complete Hausa Novel

Wata Rana SAFWAN sun taba fada d NAWAL shine fadan su na farko atarihin soyayyar , Inna dije ta dakama tsawa har da Alakoron tsaki dare d gyaran harara ,wanan Abu shi y fusata ran safwan Dan wanan shine karo na 5 da takema Inna jide abinda ran SAFWAN Bai so ba Dan matar Tana mutun tashi in ta kawo Mai ruwa ko aka aiketa wajen shi ,shima Yana girmamata amatsayin ta na Mai shekaru ,akan dai Ina dije aka Sami matsala tsakanin 2lovers Dan haka ranar baran baran akayi ,Abin d y sashi tafiya kuwa Taki karban *KUSKUREN TA* Gani take meye lefi Dan ta hantari Mai yi musu bauta wato Aiki,haka y barta y tafi gd ko sallama babu …..
Zuciyoyin masoyan sun kwana kunci ranar Dan ko irin musayar kalaman luv din d suka Saba suke wa junan su kullin ranar be samu ba ,dukan su sunji dacin Abun ga kowane naji d kanshi akan baze nemi wani ba …..
Haka soyayyar su ta fuskanci tazgado (fushi) har na tsawon sati guda kowannen su ya jigata hakuri kawai sukeyi kowa nason gane wa yafi damuwa d wani ,akarshe dai NAWAL CE ta bada Kai bori ya hau…..
Ta fara turamai d text ,da kamar baze responding ba daga baya yakasa jurewa shima y Mata reply , Nan komai y wuce suka re_new din soyayyar su ….
*WANE NE SAFWAN*
*SAFWAN* d’ane ga Alhaji Bukar ,shi Kuma mijine ga Hajiya Aslamiya ,SAFWAN Su biyar nee gdn su shine na 2 Yanada Yaya 1 Ibraheem sai SAFWAN sai Twins dukansu matane sai Autar su jannah …..
SAFWAN sun taso cikin kulawa ,gata ,yalwan Arziki ,hakan besa sun sangarce ba Dan gdn su Sam ba wata Mai akin d take kwana wata datijuwace kawai d take zuwa d yarta matashiya take ma Ammy shara d wanke wanke Tana gamawa take tafiya in anada bukatar ta kiranta ake a waya dake Ammyn ta sai Mata ,Dan haka Ammy t goge d Aikin ta har su twins ma suna hidiman gdn sosai , hatta su SAFWAN insun so suna shiga kitchen shida Yaya su dafa indomei ko shayin coffee ko soya kwai Ammy tayi t tsokanar su A Alhajin su suna cewa matan su sun huta ,suna cewa wazema mace girki ashema b AUREN mukayi ba ,
duk atajirancin irin na Alhaji Bukar , Yana wadata iyalin sa Dan motar yaransa daban take tun suna kanana kaisu school ,islamiya ,kaisu gdn zoo yawon shakatawa ,kaisu super market siyaya ,wajen wasanin yara ,Yana nuna musu gata d sangarta ,amman sakamakon nuna musu daidai d akeyi d sunyi ba daidai ba za’a tsawatar musu ta sigar rarashi d iya sarafa tunanin su Dan haka suka zama Abin Alfaharin iyayen su …..
Bayan sun Malaki hankalin kansu Yaya d SAFWAN Alhajin su y malaka musu mota zabin ransu , bayan sun kamala karatu Kuma y sama musu Aiki shi Yaya Yana Aiki a asiti shi Kuma SAFWAN Yana Aiki a Karkashin Alhajin su y bude Mai company Yana Aiki a wajen ……
Cikin nutsuwa d nuna sha’awar AURE,SAFWAN y bayanama mahaifan sa y samu matar Aure , ganin baida matsala t kowannen fani
Nutsuwa ,Aikin yi, Kuma zai iya rike mace basa haufi yasa suka barshi sai ma mara masa baya d sukayi ,har aka dinga tsokanan Yaya wai y zama Yaya na zaure ,shidai yace b yanzu ba ,Nan su twins suka dinga murna za’ayi biki a gdn su ……
,,,,,,,,,,,,,,,,,
Cikin lokaci kankani aka yanke bikin SAFWAN D NAWAL ,Batare d ta kamala hada dgree d’in ta ba Dan haka taci Alwashin karasawa ko agdn mijin tane , Koda sukayi shawara d SAFWAN yace Mata b matsala yasan dadin karatu d amfanin sa baze hanata ba ,Dan haka bikin su wata 3 akasa kacal …
Kwanci tashi asarar Mai Rai komai akasa masa lokaci Mai zuwa ne indai d Rai da lpy ,Dan ayanzu bikin su y gabato , angama shirya komai na biki ,biki na nunama sa’a ango yayi hidima d Amarya , iyayen ango sun nuna bajinta Suma na Amaryar haka Abu dai cikin girma d Arziki aka samu aka Kamala biki Dan dunbin jama’ar da bikin ya samu Abin ba’acewa komai Dan Kaf ‘Yan *MAMAN SHAHEED FANC* Sun halaci bikin sunci sunyi guzirin musamman masu cikin group din ,da ‘yan matan cikin iyayen karban takeaway har matan AUREN ma anci antafi dashi gd (su Oo har d neman Kari) ,biki y tashi lpy ankai Amarya gdn Ango nata zumudi d farin ciki mara misaltuwa ,Amaryar ma fa Tana cikin wani yanayi na farin ciki …… …
_MAMAN SHAHEED_????
[12/28, 6:58 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????
“`BY MAMAN SHAHEED“`
*KUSKURE* ????????♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)
_shafi na uku_
Ango SAFWAN D Amarya NAWAL ,Sun gurji Amarcin su son ransu , sun tafiyar d Al’amuransu yadda musulunci y tanadar ,tare d jagorancin SAFWAN Dan Akwai ibada , …
NAWAL Tasha tarairaiya yada y kamata g angonta SAFWAN , taga kulawa Nan t Kara gane banbanci tsakanin Aure d ‘yan matanci , takuma ji dadin irin kulawa d Angon ta y Bata ji take tafi kowace ‘yamace dace ,minus maman shaheed d Waleed lol.,…
Bayan watani biyu kacal ,NAWAL ta fara bojiro ma SAFWAN d maganar ‘yar Aiki wai ta fara gajiya d Aikin gdn ,Nan SAFWAN y nuna Mata bafa su gama cin Amarcin su ba ,bare wani yazo y musu Karan tsaye , yadai Mata bayani na fahimta , badan ranta y so ba suka k’ara wata uku adadafe ,gashi Tana zuwa makaranta ga hidiman gd …..
Nan t nuna Mai gaskia anemo Mai Aiki Adinga biyanta ,ya Mata mgn akan t Kara hakuri t nuna Mai ta fara gajiya f d Aikin gdn wlh ..
Abin baima SAFWAN Dadi ba Dan beji dadin kalamin t Kan ta gaji ba ,to d Auren t gaji ko me , yayi niyan tsawatar Mata d daidai t Mata kalaman t ,sanin cewa zuciyar t kamar akusa take wani lokacin ,kuma baya so Ace daga Auren su ko shekara ba’ayi ba har an Fara samun sabani acikin Auren su Dan haka y Bata hakuri akan cewa zai sai yadda za’ayi …..
Sai da taji y fada haka sanan ta Dan ji sanyi sanyi aranta ….
Cikin wata na 5 d bikin su ,suna bama juna kulawa yadda y kamata ,..
Kwatsam laulayi y kawo ma NAWAL ziyara ,laulayi sosai Dan tun Bai cika wata 2 ba take t fama d laulayi ….
Ganin irin wuyar d take Sha yasa ,SAFWAN Nemo Mai Aiki ba shiri Dan Yana tausayin ta in y fita kullin hankalin sa na kanta …
Ai ko Ammy bataji dadin d’auko Mai Aikin d SAFWAN yayi ba ,Dan cewa tayi g su twins d se su dinga Mata komai Basu d matsala d Aiki Dan yara Mata sai d kokarin gyara Nan tsaftace can ,Dan wani lokacin ko wani Yama Abu indai ba da kanka kayi ba ji zakayi kamar ba a ma ba saidai kayi Kara k yaba kokarin mutum…
Aiko SAFWAN yace ,Aikin gama y gama Dan yarinyar har t fara tayata hidimomin gd ,Ammy d Yaya Ahmad suka samai dariya , Ammy bacewa sai kace gdn iyali irin yarane agdn wai hidimomin gd ,shi dariyar yayi Yana Sosa keya , azuciyar shi Yana cewa su Yaya sun gano Ni na gama Aiki ,sai asanan yaji kunya yayi sum sum y ma Ammy sallama y gdu d Yar junyar shi .,…..
Amarya NAWAL anata faman bada umarni g Indo ‘yar Aiki , tanata Shan tsawa d hantara ,SAFWAN nason Mata mgn akan Abin d takema indon Amnan ji yake kamar in y Mata fada kamar ze shafi cikin jikin ta Dan Yana ji d cikin kamar akanshi aka Fara haihuwa yake ji …
Haka dai Indo sarkin hakuri , injin sarkin Aiki taketa hakuri d uwar dakin nata , Dan inn ta koma gd Tana b Inna lbr sai tace ta Kara hakuri wata Rana sai lbr ,ta Mata uziri ba ita kadai bace …
Haka tafiya taketa turawa , SAFWAN na fama d siyo wanan ,bar wacan irin n masu juna biyu ,Indo ma n nata hidimar ,Dan ko girki take wani lokacin sai an Mata kashedin Kar ta bar kofan kitchen din abude ,in ba haka ba Abin d ta dafa zai zama haramiyar t Dan baza ta iya ci ba ,haka indo take bin doka Dan Azauna lpy …..