HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Sanan t tashi aka farama su huzna ..

Anata kwaliya su hassana d ussaina suna can sunata gaisawa d wasu bak’in Alh su …

Gashi me kwaliyar t gama ma kowa su kawai take jira ,da kyar ussaina tazo aka Mata ,Amman har yanzu ba ama hassana b Ammy t Kara sata Aiki ma ,Dan haka tazo t Kara b Mai kwaliyar hakuri ,ganin kamar ta kosa yasa tace ma Indo tazo amata kwaliya , Zo kuga idon indooo kamar kwalatan biri ,ta zazaro ido tace aa ita base tayi ba Tana sunkuyar da Kai k’asa , Aiko Mai makeup d’in tace kizo Ni na fara yi Miki tunda tace amiki kinaso kina kaiwa kasuwa Dan n kusa tafiya Akwai inda zani yanzu ..

Indo Bata d zabi , hassana CE kamata t mik’ama Mai kwaliyar ita Kuma t tafi Aiken Ammy …

Indo fa an Fara ba da light , ta Fara tashi dg Indo Tana Shirin komawa Aisha “cikin wani lokaci sai g Indo t rikid’e zuwa Aishatu habawa ,su suhaima ,Asmy ,ussaina ,huzna dama t tashi ta tafi way d man d’in ta wai , suka kasa gane Indo ,sai a lokacin ussana t tuna ai ko Kaya indon Bata Saba ake Mata kwaliya ..

Tsaida kwaliyar akayi akace taje t sa Kaya ,Mai wayo wajen zuwa sa kayan taji anata Kiran sallah isha’e Bata fito ba sai da ta gabatar d sallah ishan ta , dama tanada Alwala itama sanan t dawo d’an kwalin t ahannu…

Haka aka cigaba d yi Mata kwaliya har ta gama Mata t Mata d’auri Mai steps, hmmmm hohoho Indo dai t koma Aishatu Bamai ganeta sai an Gaya Mai , sun yaba tsarin t d kyan kayan d tasa , Ashe dama tanada kyau sai kankantar shekaru kawai….

Ana gama Mata ,hassana ta dawooo ,itama sai d tayi d gaske sanan t gane Indo .

Itako Indo sai kunya takeci , sai rarabewa takeyi , ta kasa sakin jikin ta ,

Bayan an gama ma hassana tata kwaliyar , har d’auri d komai d komai itama t yi sallah ta har su ussaina sun zame sunje sunyi sallah su time yayi na tifiya dinner ,motoci sun Fara zuwa ..

Noor d Haneef ,suna tare d Indo t canja musu Kaya ,tace suje su nunama momyn su kartace ba su za’asa musu ba t kunyata ta acikin mutane , Dan bataso su had’u ma ji take kamar zatace tacire kayan jikin ta Dan tasan halin ta …

Aiko akaci sa ‘a ta yaba kwaliyar d indon ta musu tace t rikesu atare d ita suje su shoga mota ,su Fara gaba akaisu wajen dinner , memakon t rik’e ‘ya’yan ta (wasu matan ma dai toh) Indo Mai neman kiris tace toh ta d’auko gyalen ta dama shine mahadin kayan d tasa d takalmin ta d fos d’inta ta Kama hannun su suka wuce zasu fita wajen d motoci suka Fara jeruwa ,sai ga kawarta yarinyar Mai Aikin gdn su Ammy , itama su hassana ne suka siya Mata kayanta , Amman ita ba a Mata kwaliya ba ,Indo tasan itace daidai ajin ta talaka ‘yar Mai Aiki shiyisa suke kawancen su tun Fara bikin Kuma itama tanada hankali …

Dan haka tare suka tafi suka shiga motar wani driver suna jira afara tafiya atafi dasu su Haneef n hannun su ..
[12/28, 7:01 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`BY MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)

_shafi na shabiyu_

“Cikin takun isa irin na Amarya d Ango tare da rakiyar d’umbin Al’ummah suka rako ango d Amarya har wajen da aka tanada na musamman Dan su..

Suna zama waje y d’auki tafi da sowa ,can aka saki kid’a d wak’an Ahmad shanawa ta Ashe gaskia Tana da dad’i …..

Haka aka dinga kwasan rawa , ga Abin yayi tsari dan save ur self akeyi awajen kowa Abin d yakeso yake d’iba y koma domin ci …

Noor ceta tashi d gudu t tafi wajen dadyn ta yayin d ta hango shi ,ita Kuma Indo Sam Bata hango shi ba gashi itace me kula d su , Dan haka cikin himma d sauri ta tafi domin kamota , lokacin shi dadyn nasu y juya baya Tana zuwa t rik’e Mai hannu lokacin d yayi daidai da k’arasowan Indo itama t kamo hannun Noor d’in d niyar t dakatar d ita ,…

Shi Kuma Jin an kamkame Mai hannu y juyo d niyar ganin waye?

Idon sa Bai sauka Kan ita Noor d’in ba sai da ya fara tozali d Indo house girl d ta d’au wankan sikari , cikin Jin wani bak’on yanayi atare da shi na ganin wanan fuskar d kamar y Santa Amman Yana shaku ..

Daga bisani y Lura d wacce ta cakumeshi Tana fad’in Dady kayi kyau, surar ta yayi y Bata kiss yace thank you my luv , Ashe Kuna Nan ,kema kinyi kyau my Noor ,ina brother ki tace Yana wajen can t nuna Mai da yatsa ,yayin d yake Satan kallon Indo yanaso Yama Noor tambaya…

Itama Indo saroro tayi d niyar komawa tunda taga Ashe dadyn su t hango , d kyar t iya firta sannu dadyn su Noor …..sai d yaji muryar ta ya fita daga kokwanto ko y Santa ,wai dama Indo Ce ?

“Abin y matuk’ar bashi mamaki , uwa uba tmby inda t samu Kaya ga d’aukan wanka gaba d’aya in one time ta canja haka ?

Can Kuma y fara tambayan kansa toh ,meyema aciki in ta canja ,ai d sallah d biki mace komai munin ta d kazantar ta canjawa takeyi ,toh danme zan damu kaina ma y kawar d zancen yace ma indon kije kawai zan kula d ita har ta tafi…

Ya kwala Mata Kira t juyo cikin wata siga ,saida idon shi y bada wani light d y had’a ido d ita indon asan da t juyo ,sanan ya gajarta maganar yace ki d’auko min Haneef ki kawo min shi can ya wuce ba tare d y jira amsawar ta ba …

Itako bin ummarni tayi , ta tafi ta d’auko Haneef ta je kaimai , kafin t k’arasa ta ganshi d huzna suna kwasan pix ,Dan haka t d’an jinkirta ta d’an tsaya Tana kallon su ,Ashe NAWAL na hango su a hanzarce ta nufo su Tana huci ….

Ko da tazo ,janye mijin tayi Tana gallama huzna wata muguwar harara ,Tana ce ma huzna Abi wani sarkin b wanan ba Tana k’ara jifanta d mugun kallo …

” Ran huzna y matuk’ar baci Dan haka t buga tsaki tace naki wasane yarinya bakisan huzna ba ….

Shiko Ashe tun d’azu y hango indo kin karasowa dai tayi , sai a lokacin d NAWAL take kokarin janyeshi a wajen kwatakwata Yama Indo magana ..

Yace Mata t kawo Mai Haneef d’in Mana ,shima Haneef d’in dama tun d’azu yake zillo Yana son kwacewa a hannun ta yanason zuwa ga dadyn shi ,…

Indo badan taso ba tayi saranda ta karasa cike da zilimin Dan harda ganin momyn su Noor yasa ta dakata da Kai Haneef d’in ..

Ko da indon t k’araso daf d su ,ido momyn su Noor d’in ta zaro , cikin kin kid’ima da mamaki Mai tsanani a fuskarta ,tace Indo ?

Cikin rawar murya tace ,naam Aunty!

Ganin halamun zata tozarta ta cikin taron jama’a yasan aikin matar tasa , yasa yace Kinga Zo mu tafi anata neman mu ,zata Kara magana ya dakatar da ita yace t wuce su tafi ……

Awajen suka bar Indo ,jiki na d’an kyarma ,itako momyn su Noor badan taso ba ta hadiye maganar da takeson firtawa ,Amman abubuwa nacin ta aranta ,Dan tanada tarin tambayoyi da zata ma Indo ,Amman y hanata ….

Indo fita tayi daga Hall d’in gaba daya ,Dan har gumine y fara tsatsafo Mata Dan ta tsani tozarci arayuwar ta Dan haka ta fita Dan Shan iskar waje badan ciki ba iska ba ….

Tana fita ,ta Sami rakiyar wanan gayen d y dinga kalon ta kamar y Sami tv dazu …..itama huzna bin ta tayi taji inda ta aro kayan jikin ta d uban d y Mata kwaliya haka irin tasu ….

Itako duk batasan sunayi bama …

Gayen nee ya Riga huzna tare Indo ,cikin salama d kyakyawan lafazi y tareta , sanin mahimmancin sallama yasa ta amsa Amman Bata tsaya ba ,

Haka y cigaba da binta suna taku, in ka gansu kazaci shekararun masoyane ..

Ganin zata wuce shi ,ya rok’i Alfarmar sanin sunan ta d ta bashi Kuma aron lokacin ta …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button