HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Aiko da kanta ta tafi kiranta ,sukazo har gaban dadyn su Noor d’in

Cikin Isa d gadara ,NAWAL takema Indo magana….

“Indo”

“Cikin sanyin murya tace naam”

“Uban wa ya baki kayan jikin ki da Kika sa ranar dinner?

“Cikin kid’ima d rawar murya “tace Su hassana da hussaina ne suka siyamin suka dinkamin Kuma suka bani sukace nasa ranar kamu d dinner”

NAWAL tace Kan uban Nan ,au bama kala d’aya bane? Munafuka …..dadyn Noor ne y dakatar da NAWAL din..

Bari in Kira su twins d’in naji ,tace kirasu mu kure munafuka !

“Y dailing number hassana ringing 1,2 aka d’aga ,ya fara magana yaji muryar Ammy nacewa wayar Tana hannu na su Kuma suna d’aki kasan k’anwar taka d ajiye waya duk inda ta samu..

Safwan y k’osa da bayanin Ammy , yace hassana fa Tana kusa , Ammy tace duk suna can …Bata rufe baki ba sai g ussaina ta shigo d’akin …..sanan Ammy tace toh ga ussaina Nan ma t shigo t Mika Mata waya …

Usaina n karba tace , Yaya y kikaje gd? Yace lpy kawai ,yace ke waya siyama indo kayan anko ?

Duk sunajin hiran nasu har NAWAL d’in ,ussaina tace eh mu muka siya Mata Kuma d izinin Ammy…

Yayi ajiyar zuciya ,yace kin tabata Kuma kala nawa kuka Mata ?

Ussaina tace kala biyu ne , mu muka Mata duka har d’inki Yaya indon CE ai Bata d matsala tanada kirki wlh kodan hidima d take dasu Noor ai ma Mata Abin da yafi haka ma …

Ya ce eh , kin tabata dai ko? Tace eh Yaya g Ammy ma ka ji daga bakin ta t sakama Ammy waya a kunne..

Yana Mata magana Ina Ammy har ta Amshi magana ,safwan wani abune Dan sunma Indo d’inki lefi sukayi naji Kanata tuhuma ?

Cikin inda inda yace aa Ammy dama ,bamu San Wanda y Mata bane dagani har momyn su Noor shine muke tambaya ..

Ammy tace hakane ,inace sun Gaya muku ai ,hakan nada kyau , Nima d Amincewa ta hakan ta faru Dan sun tambayeni nace suyi Mata ai ta cancanta ,Mai hidima ga iyalanka ,

Yace hakane Ammy Allah ya Kara girma ,sai da safe ,Ammy tace Allah ya tashe mu lpy Allah y hutar da gajiya ….kafin y kashe waya NAWAL t tashi fuuuu ta nufi daki ta barshi awajen amsar Bata gamsheta ba gashi Ammy ta Mata katsalandan tashiga maganar …

A wajen tabar shi da indon ta tafi Abun ,ta shima y juyo y zubama Indo ido , ita Kuma ta sunkuyar da kanta k’asa ,yace ta tashi taje ta kwanta Abin ta ….cikin himma ta mik’e ta nufi d’akin ta ….

Shiko be bi NAWAL ba seda y shiga d’akin yaran shi ya musu Addu’a sanan ya bita d’akin ta Dan Mata tambayoyi
[11/15, 5:43 PM] Maman Shaheed: Daga baya y shiga d’akin ta y sameta Tana kad’e shinfid’a ranan a jagule ..

Y zauna Kan wata kujera 1seater a cikin d’akin yace Zo muyi magana NAWAL,seda gabanta y fad’i Amman ta dake taje ta zauna kusa dashi..

“Yace NAWAL baki gamsu da bayanin Ammy bane mahaifiyar gareni ko me kike nufi d har Kika d’auki zafi akan ‘yar maganar Nan?

Cikin Jin kunya tace ,laa nifa ba manufata kenan ba!

Ya katse ta yace” bayana min manufarki Ina Jin ki?

Ta ce aa wlh Abin NE y d’aure min Kai ,Kuma kaga su Hassana ma ai Basu kyauta min ba sun munafirce Ni ….

Yace da suka Miki me?

Tace y zasu saima Indo anko irin namu ,Kuma batare d sun bani na Bata ba , me yayi zafi haka d zasu min haka ? Y Dace hakan d suka min?

Yayi murmushi ,yace be dace ba , zan musu maga Kuma ,saura me Kuma?

Tace har kwaliya fa sukasa aka Mata irin tamu,Bata karasa ba y katseta Yana dariya ,yace Banda Abin momyn su Noor meye acikin kwaliya Kuma ?

Tace kasan kud’in kwaliyan kuwa?

Yace ko nawa ne yakai 100 thousand ? Tace a haba saikace ….

Ya sake katseta ,yace to meye Dan anmata kwaliya irin taku , ta haskane na lokaci d’aya ,NAWAL t d’ago d sauri ta kalle shi tace kaima ta haska ka kenan?

Yace ,aa ki Bari in gama maganata Mana ,yace Kuma ma yanzu Ina kwaliyar take? Tun aranar fa duk kukayi asarar kudin d kuka biya kuka wanke ta ,yada tata ta goge haka ma ta kowa ta goge ,ko Akwai a fuskar ta har yau?

Kai kawai t girgiza Mai Alamar babu ..

Yace toh ,duk fa abinan ke Kika d’auka d tsanani yarinyar Nan Tana Miki biyaya ga hidima d take Miki d yaranki , kwanaki fa bakiji dad’in cewa da tayi zata bar Aiki a gdn nan ba d yanzu fa Bata Nan ,in Kika ci gaba d takurata ta tafi shikenan …

Kayan d kike magana akai ,kinji dai Mai Ammy tace Kuma ,su twins nace zan yi musu maga ,shikenan?

Badan taso ba sai dai Kar yace ta Raina maganar Ammy yasa ta hakura tabar zancen suka kwanta ,cike d faranta ran junan su.

 

*Maman shaheed*????
[12/28, 7:03 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`BY MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)

_shafi na shahud’u_

 

“Haka zama yaci gaba d gudana tsakanin momyn su Noor d Indo , aikin ta dai Yana Nan kamar yadda yake na hidiman gidan ta hak’ura tabar maganar badan Tana so ba ..

Su twins Kuma Tana Nan ta hak’esu aranta ,wato d t hanasu siyama Indo Kaya saida suka siya Mata ,har d dinka Mata harda Mata kwaliya Dan kuturun wulakanci suna had’a level d’in ta da Mai Aikin ta ,zata had’u dasu ne zata yanka musu warning Mai yaji kuwa..

 

Indon ma badan tasan in ta rasa ta ,zata Jima kafin t Sami kamarta ba ai d ta k’ara Mata wuta …

Ango d Amarya anacan anata gurzar amarci ,Yaya Ahmad suna waya d k’anin shi SAFWAN yanata cewa yaushe zasu Zo ,shiko safwan kunya yakeji Yana cewa zasu Zo ne.

Yace su twins fa sunzo har su huzna ,safwan yace dama Wa’yan Nan ai ‘yan tamore ne ‘yan sai gara takare zamu rabu kenan ,suka dinga dariya , har suka gama wayar.

Su huzna Ana gari ,anata faman zirga zirga Ana zazu a cikin garin.

, har takardun NAWAL sun fito na kammala karatun ta ,ta dukufa neman Aiki haik’an dama can Tana nema …

Yau Bata Nan ,gobe Bata can , shima safwan yanzu y zage Yana neman Mata aikin a wajen d hankalin shi zai kwanta , Dan da aikin ne bayaso yasa ya k’i dagewa ya Nemo Mata aikin , Amman gani tak’i Nutsuwa yasa y fara nema Mata shima …

Cikin ikon Allah ta Sami , Aiki a wani private hospital ,tayi murna kuwa , safwan nema y samo Mata ba lefi hankalin sa ya d’an kwanta d hospital d’in ,saidai yanayin aikin kamar tafiso a government hospital kawai dai ta Raina sallary d za ‘a Bata .

Bayan wani lokaci ta Fara fita Aiki ,hidiman gidan y sake samun matsuguni da kyau a hannun Indo ,hatta break d hidiman safwan Indo Ce Mai Yi ,saidai in ya shirya da wuri sai su fita tare dashi Dan ita Tana rigashi fita ….

“Huzna kuwa ta Sami Kiran gagawa daga gdn su haka ta tatara ta koma batare da ta gama cika burin ta ba ,amman ta k’udiri aniyar dawowa Nan kusa”

Su Noor ko dama sun Kara zama yaran Indo , tun tashin su d safe ita take zama dasu har sai momyn su ta dawo ko ta dawo ma Indo Ce koman su …

 

Indo hak’uri kawai takeyi ,Dan ma Inna na rarashin ta ,sanan hadiya ma n Bata hak’uri Kan ta cigaba da hak’uri wata Rana sai labari har ta samu ta cika burikan ta guda biyu…..

************
*WACE CE INDO*❓
“Aishatu wacce aka fi sani da Indo ‘ya ce ga Hafiz mamman ,ita kad’ai Allah yaba su shida matar shi Umaima ,

K’auna ce mai tsafta da inganci tsakanin sa da umaima , suna nunama junan su kulawa sosai Hafiz beyi nisa a karatun shi n Boko ba daga sakandiri be Kara ko Ina ba shima d kyar y samu y Kamala ,saka makon tasowa da yayi a hannun kishiya maman SA “Amman ya Sami na addini har matakin sauke Al’Qur’ani da wasu litattafan, ya azabtu a wajen ta iya azabtuwa gashi baban shi bashi d kata bus sai Abin da tace Mai ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button