KUSKURE Complete Hausa Novel

Nowk ta sakeyi har so 3 har ta Fara k’osawa ,can Taji an bud’e ..
2eyes sukayi d dadyn su Noor , cikin kirsa ta tafi gareshi d murmushi d alamun gajiya atare d ita ta d’an fad’a jikin shi , Tana wash! Dear ..
Janyeta yayi daga jikin shi ,y wuce y barta a wajen , Tana tunanin me ze biyo Bayan hakan.
Jiki a sanyaye t wuce bedroom d’inta don wanka, “dama duk warin asibiti takeyi inji meelat ,ba injini ba lol”
Bayan ta gama wanka , cike d zullimi ta Isa ga yaranta ta rungumesu ,Indo t gaisheta ta Mata sannu d dawowa ,Tana Mai Mata kaico acikin zuciyar ta “daga Nan t k’arasa wajen dadyn su Noor Yana zaune a parlour Kan kujera ..
Ta zauna kusa dashi ,ta kwantar da kanta Kan ciyar shi Tana Mai wani irin kallo na salon rok’o da magiya ….
Shiko ko kalon ta beyi ba , saima d’aukan kanta d yayi y ajiye Kan kushin d’in kujera ,shi Kuma y tashi y bar wajen batare d y cemata komai ba , wajen breakfast y nufa y zuzuba komai dama Indo ta Kamala komai ..
Su Noor ma sun gama breakfast d’in su t musu wanka t saka musu uniform ta gama had’a musu lunch box d’in su t Basu school bag d’in su sun goya ta,sun fito very clean “ta kaisu suka gaishe d dadyn su Dan taga basu gaisa ba ..
Anan Ne Mommy su Noor tana can nesa dasu inda y barta taga dariyar mijin nata , y saki jiki sosai y gusar da duk wani fushin fuskar shi y musu kiss y musu Addu’a y samusu Albarka y musu Adawo lpy ..
Sanan indon t kaisu g momyn su ,itama t musu kiss sai Adawo lpy d ta musu ba Addu’a ,sanan Indo ta kaima baba Mai gadi y mikama school bus dinsu su Dan tafiya school ….
Daga Indo sai dadyn su Noor sai momyn su Noor , tanason rokon shi ,Tana tinanin tijarar d ze Mata gaban Indo ,gashi yaki Bata dama d zata rokeshi , da Alama yayi fushin d be tabayi ba gaskia Dan haka a shashancin ta Bari ta Bari in y sauka sai ta rokeshi ai ze yafe Mata ….
Haka y gama break d’in shi y nufi bedroom din shi y yi wanka y gama Shirin tafiya office yazo ze fice Abin Shi ..
NAWAL ta rakashi bakin k’ofa ,Indo ko cewa tayi dadyn su Noor Adawo lpy, yace Allah yasa batare d y kaleta bama ,itako momyn su Noor Tana Shirin fita waje Dan yimai rakiya ,hannu y d’aga Mata Alamar ta barshi ,ta tsareshi d ido , ya gyad’a Mata Kai yace yeess nace ki barshi na gode !
Y yayi gaba Abin shi , jiki ba kwari ta dawo ta wuce bedroom d’inta ta kwanta tanata lisafin dokin rano , kwakwalwarta cike d tunani ,Bata Samu sasauci ba seda ta tuno wasu hiraraki d sukayi da doccas sanan ta Sami Nutsuwa har Tana cewa yayita fushin zema sako ne ,Dan tasan baze iya ba indai ba ita arayuwar shi (nidai nace wato Karin maganan ku dayane ko shima haka yake cewa ) Dan haka ma bacci Mai nauyi ya d’auke ta …..
Bayan Indo ta gama komai ,ta koma d’akin ta Tana sauraran redio wata ‘yar raga d’ud’a da ta karba awajen Inna …
Tana sauraran wani shiri a gdn redio na zamantakewan Aure ….
Tayi nisa cikin Jin redio , har bacci y d’auke ta Dan jiya kwana tayi su Haneef n tashin t Shan ruwa d fitsari Dan haka take Rama bashin baccin..
Cikin baccin ta taji Ana tashin ta wai taje ta gyara ma dadyn su Noor d’aki ,haka ta tashi idon ta duk bacci ta mitsike idon ta tafi yin gyaran badan tanaso ba in Akwai inda ta tsani shiga a Kaf gidan to bedroom d’in dadyn su Noor ne ,Amman momyn su Noor bazata gane hakan ba Sam …
Koda t shiga ,sasayan turaren d y feshe jikin shi da shi ne, ya fara Mata oyoyo , Saida wani Abu y ziyarci illahirin ganobinta da ta rasa gane komeye shi…
Gashi yau har shortnikers d’inshi y Bari d singlets d’in shi akan kado , ta rasa yadda zatayi ta d’auke su t gyara gadon ( so suke su expanding brain din Indo ne ? Inji readers) ta d’auko sandan morpper ta d’uke d su (tun Tana yarinya Inna take Mata nasiha akan duk wani abu d ya danganci wani namiji koma waye karta je wajen ko kiranta yayi Kar ta taba wani Abu ajikin shi itama ta dinga kula d kanta ,tace har Abin d mutum y Ciro na jikin shi Kar t taba) Dan haka wanan karatun Yana cikin brain d’in Indo Yana moving yadda ya Kamata hakan ne yasa Taki taba kayan d hannun ta ..
Bayan t d’auke t rasa inda zata ajiye Mai gudun Kar momyn su Noor ta gani ta sata ta wanke Mai yasa t turasu Karkashin gadon sa , can Kuma tace tab se tasani na wanke ,tab! Aida bazan wanke ba d na shiga uku na ,na tsalake maganan Inna ta ….
Haka dai t gama gyara komai na d’akin damma ba gwanin barin Kaya Baja Baja bane Yana k’ok’arin kammale kayan sa y ajiye a clotheset d’in shi ….
Bayan t gama t fito t fad’a kitchen Dan girkin Rana , ta zuba tagumi Tana cewa ooh mairai bashi da hutu ,tana Addu’ar Allah y kawo Musu mafita cikin Rayuwar su ita d Inna …..
Bayan ta gama girkin ta Adana a warmers ta tafi Jin redion ta kafin ‘yan makaranta su dawo..
Itako momyn su Noor ,tanata bacci in ta tashi tayi d’an chart d’inta t gama latse latsen ta shi take tayi har su Noor suka dawo dg school har Indo ta shiryasu suka wuce islamiya….
Yauma dadyn su Noor be dawo gd d wuri ba ,Dan haka suka Kuma sabani ..
Ta tafi Aiki “night” shi Kuma y dawo, yauma ko bi ta kanta beyi ba y wuce bedroom dinshi Bayan y gama amsa sannu d zuwan Indo …
Indo Ce take gayama su Haneef dadyn su y dawo Yana d’aki ,Aiko d gudu suka tafi har suna fad’a a hanyar tafia..
Koda suka shiga ,da gudu suka fad’a kansa suna Mai oyoyo ,rungumo su yayi gaba dayan su Yana ,musu kiss Yana tambayan su karatu d gdn ..
Noor t dinga zubo Mai suruto har da Wanda ba a tambayeta ba , har Tana biya Mai karatu d addu’o’en da Indo take koya musu Daren jiya “ya dinga musu dariya Yana nuna Jin dad’in shi, yace Kai Haneef banji naka karatun ba ,ko baka iya ba , yace na iya shima y karanto Mai Wanda y iya bakin baya fita tar kamar na Noor y dinga tafa musu Yana sa musu Albarka …
Haka suka kasance cikin nishad’i “yau har sun mantar dashi bacin ran momyn su ma ,can Noor tace Dady wlh inason lndo Tana d kirki Tana son mu Tana koya Mana abubuwa ko Dady?
“Yace eh ,Yana wani dogon nazari ,sanan yace me sunan ta?
Haneef d Noor suka had’a baki sukace indoo ,yace aunty Indo zaku dinga ce Mata kunji Dan ta girme ku..
Sukace toh, dama ance mu dinga girmamawa Wanda y girme mu a islamiyar mu inji Noor..
Dadyn su yace eh hakane…
Can Haneef yace Dady aunty Indo itama ai momyn mu ce ko? Kai ka haife ta ko?……
Noor ta sa dariya ,tunda tad’an fishi wayo” shima yasa dariya sunata Mai dariya ,Aiko Haneef y yi fushi yaji haushi ,da kyar dadyn su y rarashe shi …
Itako Noor d tafi Haneef cewa tayi Dady toh Aunty Indo ai matar kace Koh?
Wani irin firgici d mumunan fad’uwan gabane ya kawo Mai ziyara ,Yama rasa me ze ce mata ,gaban shi Saida ya fad’i , yace Noor karna sake Jin wanan maganan a bakin ki kinji yarinyar kirki ?
Tace toh Dady …
Yace ,Indo ba mamar ku bace , momyn ku itace mamarku Kuma matata ita kad’ai kinji?
Ta ce eh!
Yace Indo k’anwa tace ,Kinga su aunty hassana d hussaina Kinga Suma ai k’anne nane ko?
Tace eh , itama Ammy ce ta haife ta kamar yadda ta haife ka?
Ji yayi kamar y korasu wajen Indo ,Dan tambayoyin sun Fara galaban sa ,Amman Kuma sai ya tuna ai barin yara a irin haka ba’a Basu amsar tambayar su ba yakan sanyansu cikin shaku duk tambayar da yaro Yama ka bashi amsa daidai fahimtar sa Abin Yana wuce musu ba kamar kaki basu amsa ba ..