KUSKURE Complete Hausa Novel

SAFWAN ya dawo da Indo duniyar sa yayi da ya fito d ita daga duniyar tunani wacce suke waya.
Yace y za Ayi dasu Noor Naga Haneef nason bacci ,Indo jiki ba kwari tace eh dama tare zamu kwanta dasu ,
Yace toh hakan yayi , ki dinga musu addu’a Dan Allah!
Inayi musu dama ,Kuma zan dinga musu insha Allah, yaji dadin kalaman nata duk d kamar a tsorace takeyi ma .
Can tace Abincin ka is ready tun d’azu na gama ,da kamar yace y k’oshi Dan takaicin NAWAL d huzna itama d t tabo shi yanzu ,Amman ganin yarinyar ta wuni Tana hidima d iyalan sa yanzu ma tamai hidima be kamata yaki ci ba Dan haka yace toh y tafi Dan ci d gudu Noor t tafi gareshi Tana Mai surutu.
Haka y zuba gwaten dankalin turawa yaji kayan lambu na manja Yana ci Yana kurban chafman drink ,turawa yakeyi kawai badan Yana so ba …
Bayan y gama ma tunani y tsaya yi, duk Abin d yake, indo na Lura dashi ,tasan be wuce damuwar momyn su Noor ce ta sako shi gaba ba ,Dan kyautawa Bata kyauta ba ,to Amman ai yanada yadda zeyi inhar y Isa da gidan sa ,inko be Isa ba ai sai yayi hak’urin dole ..
Dan Indo zaman ta a gidan su Noor yasa ta k’ara fahimtar rayuwa Mai tsari d Mara tsari tayi karatun duniya da dama gata d Jin shirye shiryen gidajen radio dama Tana k’ara fahimtar rayuwa Tana banbance Abu Mai kyau d Mara kyau d can duk Bata sansu ba …
Ganin yaki tashi zuwa kwanciya , gashi Noor nata zubamai surutu Kuma bajinta yakeyi ba ,gashi ita tanaso suje su kwanta yasa Indo Mai magana …
Taje d’auke kayan d ya gama cin Abincin,tace Noor zomuje kiyi fitsari in canja Miki Kaya in koya Miki Addu’ar kwanciyar bacci kiyi ki kwanta ,duk Yana jin su ransa y sake sosuwa ..
Yana cewa wanan fa duk aikin momyn noor ne , bana Mai Aiki ba ,ita bantaba Jin ta firta hakan ba gasu Noor d’in ,Dan haka yace eh Noor ki nutsu ki iya Addu’ar kwanciya ki dingayi aduk lokacin d Zaki kwanta kinji ko?
Tace toh Dady , ai aunty tanada kirki ko?
Besan sanda y ce eh ba Yana kalon Noor d’in..
Ganin ya cigaba d zama Yana tunanin yasa Indo yimai magana , jikinta a sanyaye ,
Tace dadyn su Noor Dan Allah kabar tunanin Nan ,kaje ka kwanta ,komai yayi zafi maganin sa Allah kabar ma Allah komai ,amman fa Bayan kayi iya iyawar ka baka Sami mafuta ba ……
Kayi hak’uri na ma kutse cikin sha’anin Rayuwar ka , Dan Allah!
Yaji dadin kalaman ,Kuma gaskia ta fad’a Kuma sako ta bashi a dunkule ,Kuma hakan be taba shiga tsakanin su ba ,daga eh sai aa tsakanin sa da ita amman yau harda shawara ,Kuma dunkulalen sako warware shi sai mutum ya Sami Nutsuwa,
Dan haka mik’ewa yayi kawai ya tafi ,izuwa wajen Mai gadi y sheda Mai y rufe gida yayi Addu’a ..
Sanan y dawo y ma Noor Saida safe ,y sumbaci Haneef a rungume a kafad’ar Indo zataje kwantar dashi , Saida wani spark y ziyarci safwan ayayin da y kusanto Indo d Haneef d’in itama Indo saida ta d’auke wuta na wucin gadi , Dan taji Abin d Bata dab’aji atarihin Rayuwar ta ba , ta kasa fassara hakan Kuma Dan Bata d fassarar a cikin kwanyar ta adai yanzu Kam..
Shiko safwan tafiya bedroom yayi Yana Addu’ar neman tsari ga mahalicin sa Dan tabas yasan a daidai lokacin shaid’an ya gifta…
Abin yaba SAFWAN mamaki ,ba NAWAL ba wayar NAWAL ,ita y kamata ta kirashi ko shine y kamata ya kirata ? (Nidai nace kowannen su ze iya Kiran d’an uwansa masoyinsa) shiko cewa yayi ita ce zata kirashi tunda ita tamai lefi , sanan nace Kuma fa hakane !
Itama kanta tasan Bata kyauta ba ,amman ba yadda ta iya tanason aikin ta Dan ta fito duniya tasan ta ,gashi Tana kewan mijin ta me yaye Mata damuwa maganin jin sanyin ta, ga Aiki a asibitin ga bacci y fara ziyartan idon ta gashi bataga alamun zata samu baccin ba , sakamakon wasu tagwayen abubuwa da suke Mata Zillow , aikin asibitin da tunanin SAFWAN d’in ta , gashi Tana Jin tsoron Kiran sa batasan me ze faru ba in ta kirashi ……
Shiko dunkulalen sak’on Indo yajeta warwarewa ,Yana hango hikima d dabara cikin sakon nata ,Yana Dada gamsuwa da hankali d tunanin ta.
*Maman shaheed*????
[12/28, 7:04 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????
“`BY MAMAN SHAHEED“`
*KUSKURE* ????????♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)
_shafi na shabakwai_
“Indo d Noor sunata kallon su hankali su kwance ,har idanun su suka Fara buk’atar bacci ,
“Ganin baccin na k’ok’arin cin k’arfin su ,yasa Indo tambayan Noor tanajin bacci ?
Tace eh !
Indo tace to tashi muje na rage Miki kayan jikin ki sai kiyi fitsari muyi Addu’a mu kwanta ,Noor t tashi suka nufi bedroom din s……
Har ta kwantar d Noor bayan tayi fitsari Tana Shirin ce mata tayi Addu’a ,sai t tuna d Haneef a wajen dadyn sa …
Da sauri Indo ta tashi Noor tace taje tace Haneef yazo su kwanta sbd school gobe ,d gudu t tafi zuwa bedroom din dadyn su..
Da sallama ta Isa ,ta sameshi yanata latsa wayar sa ga TV akunne Amman hankalin shi baya ga TV …
Yana Jin sallama ,y amsa y dawo d kalon shi ga Noor ,yace Noor d’in dadyn ta baki bacci ba ?
Ta mutsika ido tace ,Dady har mun kwanta aunty Indo tace nazo na Kira Haneef mu kwanta ,
“Yace ai mutumin nawa har yayi baccin sa ,barin d’auke shi na kaishi.
Ya d’auko Haneef yace ,muje na mik’a Mata shi Dan ke ba iya d’aukan shi zakiyi ba ,tasa dariya Tana cewa wlh Dady Haneef nauyi ne dashi suna tafiya Yana Mata dariya …
Ganin dadyn su ya nufi parlour ,Noor tace Dady ai Tana d’aki aunty indon …
Kawai y canja takun shi zuwa bedroom din da indon take ,yayi nowking..
Atunanin indon Noor ce ,kawai tace shigo ……shikansa yasan Indo batasan tare suke d Noor ba Amman ganin Haneef zai kwantar ko y mik’a Mata kawai yasa shi bude k’ofan y shiga ….
Ido ce tayi mutuwar tsaye na wuci gadi , ganin dadyn su Noor d Haneef a hannun sa , idon sune y gyauraya ,sanan wani Abu Mara fassaruwa ya kaimusu ziyarar dole , atake gabobin jikin su y karbi wani sak’on d basu shirya ba …
Indo kasa zuwa tayi karban Haneef ,shima kasa mik’a Mata shi yayi ,ganin tayi nesa dashi sai gado a kusa dashi kawai sai y nufi gadon Dan kwantar da Haneef ,
indo ko ji tayi dama k’asa ta tsage ta shige ciki yafi Mata ganin da dadyn su Noor ya Mata da nighty ajikin ta gashi kanta ba d’ankwali ,har Tana ajiye hijab a kusa d ita Dan ko zece tazo t karbi Haneef d’in sai gashi y shigo ,kuma ita tabada izini” atunanin ta Noor ce *lefin waye*? *Lefi nane* nashiga uku na yau Ni……
“Dadyn su Noor ne y Mata magana ,muryar SA har karkarwa takeyi shikad’ai yasan irin karatun da shaid’an la’anannen Allah yake Mai ….
Cemata yayi tunda shi yayi bacci ,sai kimai Addu’a kinji Indo ?
“Jin shiru Bata amsa ba ,yasa y d’ago Dan ganin abin d y hanata amsawa….
Murya na rawa tace toh ,kunya duk ta gama rufe ta.
Ganin idanuwan sa na Shirin rikitata da tsoro ko tashin hankali ita kanta Bata San wanne ne aciki ba ..
Ganin yanayin ta ,yasa shi d’auke ido daga kanta y juya zai fita ,Noor t kamo hannun sa ,Tana cewa Dady kazo mu kwanta anan Mana ….
Indo Ce ta zaroo idanu Tana k’are musu kalo …
Shikan shi y firgita da maganar Noor Amman dake maza gumbar dutse ne , y d’aure ya sunkiya daidai tsayin Noor yace aa Kinga ai Nima inada nawa d’akin ko?
Ta eh Dady ..
Ya sake cewa Kinga momyn ku ma ai tanada nata ko?
Tace eh ..
Muma Nan ne namu ko?
Yace eh Mana.
Indo ma wancan d’akin shine nata ko?
“Cikin karfin Hali Dan shi kad’ai yasan yadda yakeji acikin jikin shi , yace yauwa my Noor kinada fahimta ….