HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Itama indon ajiyar zuciya tayi Mai nauyi , ahankali ta samu ‘yar Nutsuwa bayan ta zauna a kujera ,Tana tunani kala2 …

Daga zuwan ta gidan ,masifa har ta bud’e Indo agidan daga dawowar ta ?

Noor ko d Haneef suna jikin ta sunyi lif tanata shafa bayansu kamar ta samu kuliya …

Momyn su Noor shiri ma takamayi ,wato anma Bata Mata Rai a gidan Bari ta tafi aikin ta tabar musu gidan..

Bayan ta gama ta fito lokacin dadyn su Noor shima y fito zuwa masalaci ,suka had’u a parlour Indo t basu ayyar da ta taho musu dashi sunata ci suna Santi d k’aramin bakin su ..

Koda Noor taga dadyn ta ,cewa tayi Dady bisimillah zakaci ayya ? Cikin kulawa yace Ina Kika samu Aya? Tace aunty indo ce ta kawo Mana Kuma da dad’i ci kaji yace yi hak’uri ci kayan ki sallah zani ,sai tayi fushi (kunsan yaro ba ko yaushe yakeson inyama tayin abinsa kaki karba ba ,sai yaji haushi ,zaman lpy kawai ka karba kaci ko bakaso ko da dabara ne ka nuna Mai kaci ka gode kawai)…

Ganin tayi fushi yasa yace sorry Noor d’ita ki ajiye min Inna dawo sallah zanci kinji ,sanan ta saki ranta tace toh Dady ,shima Haneef yace Nima zan ragema gyad’a ta Dady ,yace to my Haneef Kai gyada! Noor Kuma Aya! a ajiye min sai na dawo, batare d y Kali inda Indo take ba bare NAWAL.

Itako momyn su bayan ta gama yafa gyalen ta da ta gama sa Tom’s d’in ta a k’afan ta ,tace ma Indo kekuma ki kiyayeni wlh ku Kuma zanyi maganin kune tayi kwafa tana Shirin fita ……. Dadyn su Noor ne yace kokuma Ni nayi maganin ki ba kafin kiyi maganin su …..

da har zata tanka Mai ganin Kar y Cigaba da dizga ta a gaban yaranta d Indo , Dan bacin ranta be wuce fad’an da ya Mata agaban Indo ba shi yafi bak’anta ranta …..fuuuu ta fice a gidan ranta a bace da gayya ma Dan yayi magana ta fetse shi ..

Shima ,takalmi ya sa yayi waje da niyar tafia sallah masallaci, ko takanta be bi ba ….

Indo suka Bari da lissafi ,ta sak’a ta kwance ,haka dai tunani fal ranta ,ga tunanin me momyn su Noor zata Mata …..

Ranar ji tayi dama ba’a gidan zata kwana ba gashi tafi tunanin dare , gashi jiya Abin d y faru na shigowar dadyn su Noor duk d tasan arashin sani hakan ta faru ,Aiko yau Haneef be Isa ta barshi yaje d’akin shi ba bare yayi bacci azo kawo shi(kujimin Indo da k’ok’ari) ..

Noor ce tace zataci Abinci , bayan indon taje tayi sallah ta dawo ta kunna musu kallo mb3 …

A sanan Indo ta tafi duba kitchen ko momyn su tayi girki Amman bataga Alamar tayi ba ,Dan haka Indo ta dinga Al’ajabi Tana cewa Anya momyn su Noor mace ce kuwa? Tama iya dafa ruwan zafi kuwa ? Bare indomei zuwa girki cikake???…

_Hhhhh Indo kunada yawa masu tambayar , harda wasu readers d’in_

“Cikin lokaci k’an k’ani ta d’ora musu julof d’in taliya d kifi ta manja dama Akwai ragowan lemun abarba data Bari a fridge …

Tana kitchen ,dadyn su Noor y dawo ,su Noor suka Mai oyoyo sunata shak’ar kamshin girkin Indo ..

Cikin Nutsuwa dake d zafi Abincin ta rik’o shi a plate tazo kawo ma su Haneef …

Ganin dadyn su yana cin Aya d gyada yanata Santi Yana tsokanar su Noor yasa tayi turusss …

Ji tayi kamar ta koma , Amman ba Hali Dan y d’ago d kansa sun had’a ido ,jiki ba kwari ta k’araso tace Noor ga Abincin naku Amman d zafi ku bari ya huce karkuci Abinci d zafi Dan ba kyau ….

Haneef yace to ,Ina na Dady Ni da Dady zanci ,

Haneef y k’ular da Indo ,kamar ta dukeshi ,can dai ganin dadyn nasu bece komai ba Kuma Yana binta d Indo ,tayi karfin halin ce mai in kawo ma yanzu dadyn su Noor ?

Da Kai y Bata amsa ,be samu bakin magana ba..

Bayan taje ta zubo Mai ta zubo lemun abarba a jug ta kawo Mai ya karba yana ci Yana ba Haneef ,inda sabo ya mugun sabawa d girkin Indo Dan shi yakeci a Koda yaushe,tun Yana kin ci harya Saba yabi jikin shi Kuma dadin shi yakeji sbd ya yarda da tsaftar ta …..

Itako Indo ita d Noor suka rabe a gefe inda dadyn su baya ganin su sosai , sukaci , bayan sun gama Indo t kwashe komai ta gyara wajen ..

Ta zauna t Fara kalo taga bazata iya ba , ji tayi duk ta takura Dan haka ta tashi ta tafi d’akin ta ta kwanta Tana ta tunanin rayuwa ….

Jin shiru Bata fito ba ,ya fahimci nauyin sa takeji , Dan haka yace baze takurata ba Bari y barsu d su Noor shi y shiga daki Dan ayanzu itace farin cikin yaransa tunda uwar su ta zabi aikinta akansu ..

Sawa yayi Noor ta kirata ,

Bayan ta kirata tazo ya ke tambayar ta har ta kwanta ne?

Tama rasa amsar da zata bashi dan Jin nauyin maganar tasa , ta kyar tace aa gyara d’akin nakeyi …

Murmushi yayi yasan fad’a kawai tayi Dan haka yace barinje kizo ki zauna dasu kafin ku kwanta ,sanan tazo ta d’an d’ofana a Kan kujera kamar za Ace ket ta keta da gudu …

Koda ta zauna ganin yanata Hira d yaran shi yaki tafiya ,ita Kuma Taki sakin jiki ,

“yasa tace dadyn su Noor Dan Allah in su twins sun Sami hutu suzo su dinga tayamu kwana ,Naga an kusa jarabawa …

Shiru yayi na wani sakanni ,Yana nazarin inda maganar ta dosa …

Can ya nisa yace zan duba na gani ,ya tashi Yana ma su Noor sai da safe …

Haneef ne yace zai bishi ,Aiko Indo t gwalalo Ido Tana jira taga yadda zata Kaya ..

Dadyn su Noor ne yace kayi hak’uri ka kwanta anan ko akaika daki ka kwanta ,Amman ka tabata kayi fitsari d Addu’a kafin kwanciya kaji my good boy?

Sanan Indo ta samu sasauci ,Haneef yace to Dady nice sleep bye ..

Dadyn su shima yace sleep more my kuratul ayn….

Y wuce d’akin shi Abin shi …..

 

*Maman shaheed*????
[12/28, 7:04 PM] First Lady????: ???? *WRITING* ????

 

“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi na Ashirin_

“`Godia Mara adadi ga masoyan indodo da na NAWAL din ma Kai har huznan ma“`????????????

“`ina son ku irin sosai d’inan muna tare iya wuya , Allah y bar so da k’aunar juna“`????????????

 

“Zangani Inna Isa agare ki……….ya fice zuwa wajen Dan Bala y bashi sak’o Kan y je y dubo in angama Mai gyaran mota y karbo Mai….

 

“Takaici bacin Rai y turnike NAWAL cikin matsanaicin baccin Rai t koma d’akin ta zuciyar ta kamar ta fito fili Dan tafasa d takeyi ……

Tanata zagaye d’akin Tana neman mafita …..da ta tuna Abin d y faru ga maruka d Tasha Akan Indo ,sai zuciya ta yunk’uro ta kamar taje ta kashe Indo da duka , takaicin ta daya Akan safwan”sai yace fa zai sake Marin ta Akan Indo ko? Tana tambayar kanta ,zuciyar ta tace Mata eh Mana dukanki maze iyayi akan wata banza Kuma house girl d’in ki wacce acikin mutane ma ita ba kowa bace ……

NAWAL dai duniya ta Mata zafi , ta rasa mafita ,kawai ta Kira doccas abokiyar aikin ta a waya ta Fara Gaya Mata sirrin gidan ta ,don shashancin irin na NAWAL …..,

Docas cewa tayi wanna b maganan waya bane ki Bari night idan mun had’u ,,,,,,,Amman fa Kar ki Bari ko mijin ki ne ya Bata Miki “future” d’inki Dan dis work d kike gani is ur future , y Kama ki zama mace tsayayiya jajirtaciya duk rintsi duk wuya kimar ki ‘yan cin ki macce Bata zama yanzu sai da madogara….. NAWAL tace toh sai mun hadu Aiki ai ba fashi wlh …..

 

Can Kuma ta Kira wata aunty ta k’anwar maman ta ,da suna shiri daga baya mamanta tayi d gaske wajen rabasu sbd ,Bata d kirki aunty haule Dan sai yadda tayi d mijin ta Kuma ta Raina shi kowa ma Bata ganin shi d kima har yayar tata maman NAWAL din zaman zumunci kawai sukeyi ,Dan taga tanada Abin hanun ta Kuma ma’aikaciyace ga kasuwanci tanayi tama NAWAL d’in Abin d yasa Bata harka d ita tun d taga Bata girmamata mahaifiya sai ta fita a lamarin ta toh shine yanzu d take neman mafita saboda toshewar basira shine t nemeta …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button