HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

 

Cikin ikon Allah ta haihu ,zumudi ,rarashi ,da rawar Kai duk sun tatara ga safwan ,ansha shagali sosai na suna , anyi bajinta sosai a hidimar sunan …..

 

‘ya taci sunan Noor , tana ganin riritawa , su twins suna t murna , suna gdn suna rage ma Indo Mai Aiki want aikin .

NAWAL Tana hanasu ,suna cewa ai b komai Aiki baya damun su , cikin kwarewa d tsafta d iya zamantakewar gd , suke tafiar d komai ,Indo taji dadin tayata d suke ,ji take kamar Kar su tafi ,Dan har hutawa takeyi ….

Gashi har t Saba dasu ,suna Hira ,a fahimtar ta NAWAL bason kulata d sukeyi take yi ba bare tayata Aikin d sukeyi …..

Suma su twins suna cewa ,Tana d kirki ,gata d d’an kyau daidai nata …..

 

Kwanci tashi b wuya , ‘ya ta girma tayi wayo ,aka yaye t , Dan Bata ma Isa yayen ba aka yaye ta wai ta gaji d tsotso , Kar Abin d take Bata Tana Sha y rame (KUSKUREN WASU MATAN)Da Tai makon mutane uku ,Dadyn ta safwan d NAWAL d Indo , …….

Dan a gida take barin t wajen Indo , bada son ran SAFWAN ba hakan take faruwa ,Amman yanzu duk y Mata fada akan tsawa d hantarar Indo d takeyi ta Kuma rage …

Duk Abin Nan NAWAL na fama d makaranta ,dan yanzu take 300level amakaranta …..

Wani adababen zazzabi nee y sakota gaba ,Dan yau y hanata zuwa lecture ma duk nacin t d makaranta …

Ganin Abin Yana gaba gaba ,kasala rashin dandanon baki , tashin zuciya yasa ,SAFWAN sun gumarta sai gurin bokan turai (doctor) bayan y gama tasa tasan y sanar musu ciki ne da ita har 3 months………,…..

 

 

*Kuyi hakuri d wanan*

 

*Maman shaheed*????
[12/28, 6:58 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`BY MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)

_shafi na hudu_

 

Aiko Furucin Likita y girgiza NAWAL Dan taji Abin har ranta ,dududu yaushe t haihun d yaye Yar Tata d har wani cikin zai shigeta ?

SAFWAN Tuni y hango razana a tare d ita, y basar shiko yanata murna ,cikin farinciki Yama Likita sallama yaja matar shi suka nufi mota Dan komawa gd ….

 

Cikin mota , SAFWAN y dinga rarashin NAWAL d nasiha Kan wasu haka suke nema ma Amman Allah be Basu ba ba’asan Kuma irin tanadin d ya musu ba ,ke y baki Amman kina fushi d haka ko?

Ta kalle shi t kasan ido , Tana cewa Ni fa b fushi nake ba ,y katseta yace tun lokacin d Likita y Fadi saka makon test din d y Miki ,Naga annurin fuskar ki ya dauke ,nafa sanki Sarai motsi kikayi nasan me kike nufi na gama karantar ki fiye d tunanin kin wlh…

Can t dago d Kai Tana kuka , nifa gani nayi ko 2yrs fa banyi d haihuwa ba ko mahaifina be koma mazaunin shi ba har Ace n sake daukan ciki ……sai hawaye sharshar (raguwa lol)…

Safwan y yi murmushi Mai ciwo ,yace haka Likita yace Miki mahaifinki be koma ba? Koko anaki likitancin ne haka ko jinin ne Kika gaji d hadawa Dani ?Ina nuna Miki gabas kina nausawa kudu…

Ran SAFWAN ya gama b’aci kawai y Mata shiru y d’auke Mata wuta ko rarashin t yakiyi akan kukan d takeyi , tun tanayi har t gaji t saurara ,suka Isa gd ..

Indo n musu sannu d zuwa SAFWAN ne kawai y iya amsawa itako d’aki ta wuce fuuuuu….

 

Shima nashi room d’in y wuce ko bi takanta beyi ba ,Dan takaici …..

NAWAL Bata Kara fitowa ba saida ta fito dinner ,shiru shiru SAFWAN zai fito yaki fitowa ta Aika Indo t kirashi (kuji haukan wasu matan ,wai Yar ‘yaki t kira mijin ki a dakin shi ) akayi sa’a Mai kunyace Kuma Abin y Mata nauyi Dan Bata tab’a shiga dakin shi Yana ciki ba Tana gyara Mai dai in baya Nan ( *WANI KUSKUREN*) Sbd haka a k’ofa ta tsaya tayi nocking yace shigo Mana ,atunanin sa NAWAL ce take shakar shiga dakin ta tsaya Tana nocking , inda watace shiga zatayi , ita ko Indo mika bakinta tayi y hadu d kofan t rad’a Mai cewa Aunty ce tace kazo kaci Abinci Tana jiran ka Yadda zaiji …..

Shi kanshi sai d yaji wani iri ,cikin zuciyar shi yace Allah y shirye ki dear , kice Mata Ina fitowa ,y ba Indo amsa ,sanan t tafi fad’an sak’o …

Bayan fitowan shi , ba Yabo b falasa ,sukaci Abinci ,Indo nata ba Noor a baki taci wani ta zubar d wani ,hakan cin nata yake …….

Bayan sun gama cin Abincin , y koma d’akin shi dake yayi sallan ishan shi ,ganin baida halin kulata yasa ta bishi d’akin shi Dan Abin y dameta sosai .,…..

Tana shiga y d’auke wuta yanata latsa wayar sa , bema nuna alaman ta shigo ba , Abin y Mata ciwo Amman t share Dan sulhu take nema (sulhu Alkhairi ne) ta zauna kusa dashi jikin su na shafan na juna tace my dear wai meye lefi nane d ka d’auke min wuta , nifa b wani Abu yasa nakejin tsoro ba kaga fa yadda Nasha fama d laulayin Noor kai ganau ne Kai ba jiyau ba , haka nazo na dinga fama d tirtsetsen ciki Ina keta Al’umma har Kai da kanka tausaya min kakeyi Banda d’umbin Al’ummah da bansan adadin su ba, sanan haihuwar ma kagafa irin gumarzon d Nasha harfa kuka ka tayani ko ka manta? ko kana so ka nunamin b tausayina ne y saka kuka ba a labour room?

 

Ta fashe d kuka Mai tab’a zuciya , shima y tuno abubuwa d dama , Dan y tausaya Mata matuka , ranar d zata haifi Noor ,atake y manta d b’ancin ran da ta sahi aciki ,y talabo ta y rungume Yana shafa bayanta Yana rarashin ta d kalamai masu sanyaya Rai ,tare d wa’azantar d ita t sigar rarashi , Jin dumin jikin shi ya mantar d ita komai suka fad’a duniyar ………….Sun manta d wata ‘yar su Noor ma hhhh

 

Cikin Nan y tsayawa NAWAL arai musamman idan fanc d’inta na tsokanar ta amakaranta wai ta zama uwar iyali sai taji dama cikin y zube (wa’iyazubillah ) haka dai taketa lalab’awa har cikin ya shiga wata Tara ,su twins insun Zo suna tayata Aiki sosai Dan komai basa Bari tayi n hidimar kanta d Noor sune Dan sun d’auke Noor ma t koma gdn Ammy hankalin NAWAL kwance wai ta huta dama takura Mata take Taita danneta Tana Mata rigima ….

SAFWAN yanata lalabata musamman yadda y san ba wani damuwa tayi d cikin jikin ta ba ,haka dai har watan haihuwar ta yazo , nak’uda ta Kama ta Mai zafi , Dan kasa haihuwa tayi d kanta sai d aka Mata C.S kowa y tausaya Mata mussaman MIJIN ta taga gata Har Ammy lalab’ata takeyi anga narkewa kuwa Wajen NAWAL ko Abinci ma Bata Abaki akeyi , doctor yace baze sallame ta ba sai taji karfi , suko cewa suke a lalab’ata ta ……

Ta Sami d’anta k’ato su twins sai murna sukeyi , SAFWAN ko yafi kowa murna d zumud’in akoma gd , Indo nata gadin gd ….

Bayan An sallameta t dawo gd har su twins aka dawo Dan suna hutun makaranta , Suma makerin budurci ya nata k’erasu sai kyau suke k’arawa anzama ‘yan Mata ,….

Ranar suna yaro yaci sunan Alhn su SAFWAN ake Kiran shi d HANEEF Anyi shagalin suna lpy , an raraba kayan rabo ,su twins an Sha shagali …….

Bayan suna su twins sun koma gd aikin ya dawo Kan Indo agogo sarkin Aiki Dan bataso suka tafi b Dan suna rage Mata wahala aikin gdn ….

Yanzu ko Aiki y dawo kanta hatta Pampers din Haneef ita take care Mai inyayi Kashi t wanke t mayar Mai d wani ,haka wankin shi haka na Noor dake ta dawo tun suna Taki komawa wajen Ammy dasu twins wai Tana wajen baby…..

Haka Indo taketa fama d hidimar gdn , har yakai ta yi shawara d Inna akan zata bar Aiki ,Inna tayi t Bata hak’uri Kan juriya d jajircewa Akan Mai hakuri yanada nasara arayuwar shi , wata Rana take gayama NAWAL zata bar Aiki Aiko hankalin NAWAL ya matuk’ar tashi Dan ta saba d ita tasan sunyi dacen Mai Aiki kafin su Sami kamarta za a Dade baran in tanajin hiran Mata a group d irin gwaramar d suka Sha da Mai Aiki , sai t Kara jinjina ma Indo Amman haka besa t kyautata Mata t jata ajiki t rage Mata wasu hidimomin d be cancanta Ace ‘yar Aiki ce zatayi ba gashi Bata tab’a kamata d lefin t d’aukan Mata k’wayar shinkafa ba bare kud’i kawai Indo itace gdn t fanin hidiman gdn Amman ……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button