HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Aiko ,d aunty haule ta daga Kiran NAWAL d’in ta gane me kiran ta Sarai ,Amman sai take tmby ta wacece? Irin batasan Mai magana ba dinan , tmby ta ba NAWAL haushi Amman tunda nema take ta fizge tace aunty NAWAL dinki ce ina son zuwa gidan ki in kina gida anjima ?

.cikin wata murya ,tace yau Kuma NAWAL? Batan Kai kikayi ne?

NAWAL tace nidai ba wanan ba kawai sai nazo din ,tace toh sai kin Zo ,Tana dariyar keta.

 

Indo dai Saida taci kukanta ta k’oshi sanan tayi shiru ta Lula duniyar tunani …

Ita ba wani Abu bane y sata kuka ,Kar ta zama sanadiyar shiga tsakanin ma’aurata gashi suna tsananin son junan su ,saidai shakuu d take Kan soyayar d ita NAWAL d’in takema mijin nata ,Dan ta dadyn su Noor ta tabata so ne yakema NAWAL Mara Algus so ne zallah tare da k’auna ,Amman ita ayukanta y Isa y saka ka kokwanto akan son da takema mijin nata …..

Indo dai tanata deciding barin gidan Dan aikin ta yazo karshe alokacin da shak’uwa Mai k’arfin ta shiga tsakanin ta d yaran Suma hakan take a wajen su ……

Indo ta ma kasa aikata komai yau agidan ,jikin ta duk yayi sanyi Bata jin kwari kwatakwata ..

 

Itako NAWAL tanata tubka da warwara har Group d’in su na *WARWARE MATSALOLIN MU* _takai sirrin gidan nata , dake Admin din Mai hankali ce ta Bata shawara akan ta bi ahankali ta samo wuyan gidan ta kafin taci gaba d Aiki_……

_sanan Kar ta sake t ketare umarnin mijin ta saboda nadama Mara amfani,har ta Mata nuni Kan cewa Kar ta tsaya kalon ruwa kwado ya Mata kafa , Kar tayi mamaki reshe ze iya juyewa da mujiya ta dinga Mata gugar zana dai (kukan kurciya jawabine)_

Aiko NAWAL tace haba! Allah y sawake ,duk yadda kuke tunani Abin b haka bane ,Sam ku ma bar wanan zancen ita fa har yanzu basu warware Mata matsalar ta ba Admin d’in da members …..

_sudai shawarwari suka Kara Bata na gaskia d gaskia suka dinga Mata hanunka Mai sanda har Dara Dara an nuna Mata matsalan Abin d take Shirin yi d Wanda tayi a baya ,Amman Inna Wanda yayi nisa baya Jin Kira NAWAL ta Lula duniyar marasa Jin kira_

“Daga baya ma da taga basu da mafita ,ta musu tsaki tayi left a group d’in….

Aiko wasu suka dinga biyo ta pc suna Bata shawarar Arziki ,duk tayi watsi ,sai wata zinaru da ta Bata ta tsiya Aiko suka jone ta dinga Mata hud’uba itako NAWAL tana nadewa Nan dai sirrin ta ba Abin d zinaru yanzu Bata sani ba ,yau kad’ai suka Fara magana ko d can a cikin group d’in ma basa magana ,Amman har ta Bata yadda har t sanar d ita tsakanin ta d mijin ta ,ta Bata shawara taji Kuma ta d’auka ,ku sani fa masu karatu itafa zinarun bazawara ce Auren ta 3 Tana fitowa ,Amman Bata gayama NAWAL din Bata d Aure ba ta boye Mata ,Amman ita ba wani Abu d ta boye Mata *hatara matan mu na Aure d zawarawa har ‘yan matan ma mu noticing mutum kafin bashi amanna*…….

Bayan dadyn su Noor y gama Shirin shi jira yake su Noor su dawo y d’ebe su zuwa gidan Ammy daga can suje masalaci shida Haneef d Yaya Ahmad d k’anen sa ..Dan sunyi way d Yaya Ahmad d’in shima zai Kai Amarya Mai laulayi inji readers ba injini ba …,lol

Gidan dai zaman doya d manja aka dinga yi tsakanin safwan d NAWAL da NAWAL d Indo Dan ko had’uwa basu k’ara yi ba har yanzu ….

Su Noor na dawo wa, kuwa ganin basuga kowa a parlour ba d’akin Indo suka Fara shiga d murnar su ,suka zube a jikin ta ,Indo ta seta nutsuwar ta ta musu oyoyo ta musu sannu d dawowa y karatu? Suna Bata amsa cikin nishad’i d sakin fuska Abin su ..

Haneef ne y fara tambayar dadyn su,Indo tace Yana d’aki ,Noor ma tace wlh murna nake zamuje gdn su aunty twins ko aunty Indo kema kina murna ko?

Kai kawai Indo t d’aga Mata ,da tunani fal cikin ranta Tana Kara son yaran ,da gudu suka tashi suka nufi bedroom din dadyn su…..

D sallama suka shiga , cikin sakin fuska y amsa y musu oyoyo kamar yadda Indo ta musu , Haneef y fara maganar zuwa gdn Ammy ,Dadyn su yace kuje aunty Indo ta shirya ki”

” su fice ,da gudu suna murna suka sanar ma Indo sak’on dadyn su ….

Jiki b kwari ta musu wanka t shiryasu cikin wata shada d aka musu anko Taji Aiki Mai kyau d tsada aka sama Noor gyale Indo ta Mata rolling dashi d takalmin ta Mai k’asan kwalba tayi kyau Masha Allah har Haneef harda agogon su d glass sukace wai dashi zasu dole Indo t musu yadda suke so ,suka tafi nunama dadyn su kwaliyar su ….

Shi kanshi yaran sun birge shi ,sun gusar Mai d takaicin bacin ran d uwarsu ta turnika mishi ,na wani lokaci (wasu readers sunce to ai da taimakon Indo kayi farin cikin Dan ita ta gyara su) Dan haka har a hoto y d’auke su y kuna datan sa y turasu zuwa status d’in sa readers Banda viewing d’in statun d’in dadyn su Noor fa Dan ganin su Noor ………wlh NAWAL ta shirya fito na fito da kowaye “ba ruwan fateemah ‘yar gidan Abubakar ..,…lol.,..

 

Shima shiryawa yayi ,yace suje su cema Indo t gama shiryawa y fito su tafi ?

Noor ce taje t Gaya Mata ,dama tayi wanka Kaya kawai ta canja ta shafa powder kawai sai man baki ta d’au gyalenta d zai shiga d kayan t tayafa Abin ta tanata Jin wani iri kamar tace su tafi kawai ,can Kuma tace tab tafiyata can d’in shine hututa yau in aka barta d momyn su Noor a gidan Nan sai ta kashema Inna ita Dan bak’ar zuciyace d ita g rashin imani ,gwamma na tafi …..

Dadyn su Noor d su Haneef ne d Indo a parlour suna shirin fita haraban gidan sai Indo tacema su Noor kun je kun gaishe da momyn ku kun Mata sallama?

Wani mugun kallo dadyn su Noor y jefo ma Indo ,atake jikin ta y karbi gargad’in d y Mata har d rawar jiki ta sunkuyar da Kai ,ta k’ara Satan kalon sa ,idon shi Yana kanta dau , d kamar bazeyi magana ba ,Amman ya cije yace bazasuje ba Yana Mata wani kalon Kar ta k’ara cewa komai .,….

Haneef ko cewa yayi sai sun dawo zasuje shi gdn Ammy ze je ,Noor ma cewa tayi Nima wlh Allah Allah nake naje Naga Aunty twins dasu Ammy gani ga aunty Indon mu ko Dady? Tare ma zamu dawo ko?

Wani murmushin karfin Hali yayi y cemata eh tawan, Indo sai d ta yabi annurin fuskar shi ,sanda y Mata kalon gargad’in nan “Karo na farko d taga kyansa d cikar haibar shi ,t sunkuyar d Kai k’asa saka makon bak’on wani yanayi da taji …..

Shi ko gaba yayi hanun sa n rik’e Dana Haneef , Noor ko na tare d indon ta …..

Suka Isa wajen mota ,Mai gadi nata gaisuwar bangirma ga dadyn su Noor,cikin sakin fuska safwan y amsa Mai,

Haneef kusa dadyn sa ya sauna wajen Mai zaman banza (gaban mota) Noor d Indo a bayan mota ,Noor nata Mata Hira Tana sako dadyn su ,haka yake ansawar dole har Indo ansawar dole takeyi tanata sasu nishad’i……
Time to time idon safwan d na Indo n had’uwa a mirron motar.,.

 

Hakimar Tana gida duk Abin d akeyi ,har dawowan su Noor taji ,Amman tace indai Basu Zo ba suje su ta zama a wajen uban nasu …..

Bata Samu fitowa daga d’aki ba sai da cikin ta y fara wuridin yunwa tun Tana daurewa har taji zatama kanta illa shine t fito Dan neman Abin kaiwa baki….

Taji duk hayaniyar su ,Amman Bata San sanda suka bar gidan ba …..

Ko d ta fito parlour bataga kowa ba ,bata damu ba ta nufi kitchen ta gama laluben ta ba ko Abincin d bera zeci , taga ma tukwanen duk Indo ta wanke har su plate d’in food flacks ko ,bama alamun Abinci a cikin su ,amman sai da ta duba Dan ta tabatar …….wani dogon tsaki taja na takaici d bacin Rai t wuce fridge Dan neman ko meatpie ne da d’an drink ,ta samo want guntun shawarma d juice…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button