HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

SAFWAN ! SAFWAN!! Akan wanan kazama talaka wawiya Mara amfani ga Al’ummar ka mareni?

Yace eh ,Kuma kece wawiya ,butulu duk hidima d takeyi d yaranki d gidan ki Amman d Abin d Zaki saka Mata kenan sokuwa kawai wlh kinyi ya isheki ayanzu ko ki seta Rayuwar ki d tsarin Auren ki ko na seta Miki Dan na gama d’aukan duk wani shirmen ki ,Ni nake Auren ki ko ke kike Aure na ? Ba sakaran namiji bane Ni soyayya d k’auna yasa naketa kau Miki d Kai ,Amman Naga Alama ke bakisan inayi ba so kike na zama mijin tace?

Cikin kuka tace to da meye?

Yace wlh karya kike namiji nake tsayaye Wanda ya Isa d gidan shi ,in baki sani ba yanzu Zaki tabatar ….

Aiko Tana kuka Tana gasa Mai munanan kalamai tsabar bacin Rai d takaicin y mareta akan Indo Kuma a gabanta , Indo toshe kunnen ta tayi tanata kuka tana ZARGIN itace ummul aba’isin fada tsakanin su , wlh barinta gidan yafi Mata sauki d dai ta shiga tsakanin su Basu taba fad’a ba tun da take dasu sai yau ,duk d dai Abun a bayane yake lefin duk na momyn su Noor ne …

Cikin kuka Indo take cema, dadyn su Noor Dan girman Allah kuyi hak’uri indai akaina kuka Sami matsala wlh ko ayanzu daidai nake d nabar gdn Nan Bari na har abada kuwa Dan Allah ku gafarceni …..

Bata karasa ba NAWAL ta rufeta d duka Tana cewa Dan ubanki kyace Zaki bar gidan Mana tunda burinki ya cika ,har Tana tatakata kamar kayan wanki …

A fusace safwan y finciko NAWAL ya yarfa Mata maruka har hud’u masu kyau Saida yatsun sa suka fito a fuskar ta …

Yace ba inda Zaki Indo kina tare dasu Noor , ke Kuma daga yau in Kika sake zuwa night duty daga can ki wuce gidan ku ……..zan gani in na amsa miji a gareki ….

Indo Ce ta Kara rushewa d kuka tana toshe kunnen ta , batayi zaton haka daga dadyn su Noor ba …

*Tur Kashi ga k’oshi ga kwanan yunwa*

*NAWAL*
????
*SAFWAN*
????
*INDO*

……… ……… ………

*MAMAN SHAHEED*????
[12/28, 7:04 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi na Ashirin da d’aya_

 

“NAWAL gidan su ta Fara nufa ,ganin ta cikin wani yanayi yasa mama tmby ta ko lpy?

Nan t ke fad’ama mama duk Abu buwan d y faru harda k’arin na abin da be faru ba , har Abban ta shima yaji tun kafin ya tabatar da gaskiyar ‘yar tasa , a tunanin shi bega laifin Yar tasa ba Dan ganin ta yi k’ok’arin neman n kanta Dan ta zama wata da duniya zatasan da ita…

Ita ko mama fad’a ta Fara yi Mata na tsakani d Allah Tana nuna Mata Tabi umarnin mijin ta matuk’ar be sab’a shari’a ba ….

Shiko Abba cewa yayi indai baza taya ‘yar ta kwatan ‘yan cinta ba ,to tabari a neman Mata akanme ze hanata Aiki , night duty Kuma ai d’orowa takeyi kamawa tayi ,shi inda ba a night duty y samu likitoci a asibitin d yake zuwa yake Kai yaranshi in bukatar hakan tazo,har ita NAWAL d’in haihu da tazo ai cikin dare suka tafi asibitin Kuma kwana tayi ai ta Sami likitoci harda Mata ,inda ba a night ta Ina zai Sami taimakon gagawa ?har a kular Mai d ita,

Kinga ko ai night duty shima ya Mai amfani a rayuwa Yana Kan yi Mai Kuma , Koko itace baya son t Sami Lada biyu n Jakarta d n taimakon Al’ummah ?

Dan haka zanyi duk Mai yiwuwa Dan ganin n jagoranci aikin ki ,in ita maman ki bazata dafa Miki ba ,ki kwantar d hankalin ki kinada Ni NAWAL din ta ,tayi murmushi Mai cike d so d k’aunan mahaifin nata Tana cewa Abba n gode d kulawar ka gareni ….
Mama dai Addu’a shiriya ta musu,

Dan haka NAWAL bataje ko inaba ,ta zauna gidan su Tana jira time yayi ta karasa gidan Auntyn ta d tace zataje Dan neman solution …..

************
Safwan yana Isa Gidan Ammy d gudu Janna tazo ta tari su Noor shiko Haneef Yana mak’ale a wajen dadyn sa ,y ki zuwa duk wajen su ,Dan haka yace su rabu dashi ,suka kyale shi suka wucewar su zuwa main parlour gidan… .

Noor ce ta Fara kwad’a sallama tana ganin Ammy ta haye kanta d gudu,itama jannah zama tayi kusa d amjyn, Tana Mata dariya noor Tana tamby Ammy su twins…

Yaya ne dake gefen Ammy yace Noor karki karyamana farin cikin mu uwa tagari maganin kukan mu ,Ammy tayi dariya tace ai wanan k’awar tawa Dena k’awance zanyi d ita Naga karfin ta k’aruwa yakeyi dan takusa Fina k’arfi ,duk suka sa dariya har janna da Indo d take neman wajen zama a Kan carpet …

Ammy ce tace t hau kujera ,sanan t hau Tana gaishe d Ammy cikin girmamawa ,cikin karamci da iya tarban bak’o Ammyn ta amsa Dan awajen ta su twins suka gada girmama kowa,..

Suna cikin gaisawa ,safwan y shigo shida Haneef bayan sun gama gaisawa d Mai gadin gdn Ammy ..

Janna CE ta Fara gaishe d yaya safwan ,Yana amsawa Yana tsokanar ta wai Ammy Bata ji d ita tunda har t iya barinta taje wani garin Tana Autar Ammy guda …

Yaya ne y kamo hannun Haneef Yana cewa oyoyo ma boy ,Zo mu gaisa ,Haneef y k’arasa gunsa Yana gaishe shi ,ya koma wajen Ammy Yana gaishe ta ,Ammy tace yauwa me gidan Kai ka gaisheni d Kai nake Auren Amman Noor ko bana k’awance d ita Dan ko gaisheni batayi b sema turmusheni d tayi ,safwan yasa dariya Yana cewa zata jika Mana Aiki Tana turmushe Mana farin cikin mu na gidan duniya d kiyama wato Yaya kana kalon ta …

Dariya yayan yayi yace haba, ai bazata turmushe ta ba Ammyn Ca d raki kasan in tsufa y fara zuwa ,Indo ma kalon Sa ta tsaya yi Dan mamaki kamar Mai magana d kakar sa y lauya zance yanzu,tsarin su na burge Indo wasa d sanyawa junan su farin ciki ta hanyoyi da dama ,

Ammy ma cewa tayi au tanan ka bullo? Kamanta me kace d’azu ko? Indo kinji yayan naku ko? Indo ta d’ago tayi ‘yar dariya tace najishi Ammy Tana Mai Jin kunyar su dukan su ,safwan ma kalon ta yayi Yana Mai son karanto kunyar me indon takeji atare d Ammy d Yaya Kai harma shi ,Amman Yaya y katse Mai tunaninsa d cewa Bari lokaci ya k’arasa mu wuce masalaci ko ?,Haneef yace Nima zani yayan Dady dake haka suke kiranshi shi d Noor ,Yaya yace insha Allah kafata kafarka babban yarona ….

Noor ce take t tmby Ammy inda su aunty twins suke, Ammy tace suna gidan su hameeda sunje barka ne mustalakiya ce ta haihu shine sukaje ganin babyn yanzu zasu dawo lNaga sun Jima in Basu shigo ba sai kije ki kirasu …tace toh Ammyn Dady..

Sallama Sukaji ta Aunty Amaryar Yaya d su twins d’in d gudu Noor t Isa wajen su kowannen su sai d tamai oyoyo , suka k’araso suka zauna sunama Indo magana ,cikin Jin dad’in dawowan nasu take gaishe su suna amsawa cikin sakin fuska itama taji dad’i har t saki jikin ta d Ammy t tashi t bar musu wajen …

Yaya d SAFWAN ko sun tafi d’auro Alwala Don tafiya masalaci yin sallah juma’a …

Suko Hira suka Fara suna sako Indo cikin hiran ,sanan Ammy t Kira twins tace Mata su Taya iya aikin girki Dan ayi Mai kyau d dad’i Kuma Dan t Kamala d wuri ,tunda Akwai Baki a gidan ,Kuma huzna ma ta kirata a waya wai zatazo hutu gdn …..

Twins d tanata murna ,jin ance huzna na zuwa ta d’anji wani irin tasan sarkin matsala d Shan kamshi zata Zo ,ita halinta ne yake had’ata dasu twins ,Sam halin su b daya bane ,Ammy tace lpy dai hassana?

Ta k’ak’alo murmushin Dole tace lpy lau Ammy ,ta wuce tana Kiran ussaina su nufi kitchen..

Ko d t gayama ussaina sak’on momy cewa sukayi indo d aunty sufaya tare za’ayi aikin d su ,ba yadda hassana batayi dasu ba Dan su hak’ura Amman sukace Inna Sam ,haka suka nufi kitchen d’in tare ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button