KUSKURE Complete Hausa Novel

Wanan bayani b k’aramin tasiri yayi a cikin zuciya d ilahirin jikin NAWAL ba ,taji dama itace ,can Kuma tace Kai duk duniya Akwai wani namiji cikake Mai kwarjini d haiba kamar safwan d’inta kuwa?
Cikin zuciyar ta tace ,gaskia babu ,
Ganin lbr y Dora anatayi Ana shewa anama , jamcy murna ,yasa NAWAL bin chart dinsu Tana nishad’antuwa ranta har y Mata fes..
************
Safwan be bar gida d wuri ba ,sai d y biya ta supermarket y masu Noor shopping d lndo y Kara siyo Mata wasu mayun dogayen riguna irin Wanda maman shaheed take siyar wa , masu kyau ,sanan yaje Kan underwear zai zaban Mata , Isa d nuna Girman Kai d Jin yafi karfi , yasa fasa zaban Mata wai Kar t rainashi irin besan ma Tana sawa ba …
Y wuce wajen takal mi ,har y fara d’aukan size din NAWAL y tuna bafa ita zai saima b ,atake baccin ranshi y dawo sabo ,y dinga tunano lokacin d y Kali ‘yar kafar Indo y zaban Mata wasu flat guda 3 kawai ya koma Kanwasu wasu hijabai y d’auki 2 y koma kan su kayan motsa Baki y jida har su twins ,y gama y settiling bill y fice zuwa gidan Ammy….
Koda y Isa su Noor d haneef nata murna ,sukazo suka gaishe shi , shima y gaishe d Ammy y gaishe d Alhj su ,Alhj su nata tsokanan Haneef …
Bayan Ammy tamai tayin Abinci t tambayeshi lpy NAWAL b yabo b falasa yace lpy take Tana wajen Aiki …
Yaci abinci yayi Kat , ya ma Alhaji su adawo lpy y rakashi har wajen motar sa dake fita zeyi ,sanan shi Kuma y dawo parlour y Kira hassana ya Bata car keys din sa yace taje mota ta d’ebo Kaya ita d ussaina Kar su Bari huzna t je Mai wajen mota ,hassana t Fara dago zancen tace toh Yaya …
Hassana d hussaina suka kwaso komai ,suka zube a parlour gaban Ammy ,
sai ledan hannun ta d ya rage na karshe n kayan Indo ,inda t tafi d ledan zuwa Resting room inda Yaya safwan din yake don Mika Mai makulin motan shi Kuma ta tmby shi kayan waye aciki ?
Koda taje tmby shi ,yace na Indo ne Akwai Wanda kuka dinka Mata bikin Yaya kingansu kocikin kayan su Noor?
Tace eh ,yace to ki hada Mata d wad’anan Danni Banga sauran kayanta b shiyisa n siyo Mata wadan Nan ,hassana tace Aiko sunyi kyau Yaya godia take , t Mika Mai makulin Tana Shirin fitowa sukaci Karo d huzna ….
Sai da ledar hannu hassana t fad’i kayan suka d’an leko , hassana tace Kai huzna kin dinga sallama in kinshigo waje Ni har kin tsoratani g bigeni da kikayi Kuma aikena akayi …
Aiko huzna tace sorry ,nayi sallama bakuji bane ,Kuma wanan kayan nawane ,yayane yace ki kaimin Kai ilove my Yaya S wlh muga kayan ,ta janyo wata yaluwa d jar Riga masu kyau ,tace laa wlh irin Wanda maman shaheed take siyarwa ne ,dama inata neman su nagani a group d’inta harma wasu GROUPS din fad’uwa tazo daidai d zama ,Kai nagod…….
Hassana ce tace haba huzna ,waye yace Miki nakine sai zuba kike kamar lalatacen famfo?
Shiko safwan duk y gama kulewa d sanaben d huzna takeyi ,wai ma uban
Me y kawo ta y akayi tasan yazo Dan haka y dawo Nan fa ….
Hassana ganin huzna Bata d niyar sake kayan, t d’an fizgi kayan ta mayar cikin ledar t bar wajen ta nufi hanyar zuwa main parlour su ….
Atsaye tabar huzna na tunanin kayan uban waye to? Itace ai bakuwa a gidan ,toh kayan su twins ne kenan ,Inna sune Kuma ai zeyi karar karata itama y siyo Mata ,tanata tunanin da be shafeta ba har safwan y banko k’ofa y sa key y koma ciki Dan Kar ta shigo Mai ..
Aiko taja wani mugun tsaki ,yajita Sarai yace wawiya Mara class ….
Itako cikin son Jin gulma d kayan ko n waye sai ta gani Kuma taji, Dan yanzun ma ai gulma tazo yi tunda taga Ana shiga da kayan ,shine tazo ganin kwaf …
Aiko kafin ta koma ,hassana tasan Hali Sarai tayi maza ta kaima Indo kayan d’akin da jiya suka kwana d su Noor ,taje kitchen Kuma ta sanar ma Indo komai ta Gaya Mata har inda t boye Mata kayan yadda b kowane ze gani ba Dan ko Ammy Bata ga kayan ba hassana dai ta fad’a Mata d Baki ,tace safwan din ya kyauta ..
Huzna Koda ta dawo parlour t zauna Dan ganin inda za a Kai kayan , taga an bud’e duk wani Abu na tabawa Ana bawa kowa har ita wasu Kuma aka Kira Indo akace ta Adana a fridge aka Bata nata d na su iya Mai Aiki ..
Aka d’auko kayan su twins akace Indo g kayan yaranki ,har huzna zatace ya akayi suka zama yaran Indo house girl , amman ganin Ammy ta fasa mgn , tasan dai b anan taga dogayen rigar Nan ba ,shi yisa ma Bata ko Kali jakar ba …
Tanata raba ido taga anyi rabon dogayen rigunan maman shaheed taji shiru gashi taga yanzu hassana nason ta Fara rainata Dan haka t Fara Jan girman ta , Kuma d kunya ta tambaya Dan haka tayi tsit ,Amman taci Alwashin gano kayan ko na uban waye ,
SAFWAN sai d yayi baccin sa son ranshi ,sanan y tafi masallaci sallah ,Yana dawowa Yama Ammy sallama wai zaije wajen abokin sa ,Dan yau ko d Indo Basu had’u ba itako tanacan Tana cewa sai y fito zata Mai godia kayan d y siyo Mata ,
Indo d hidaya suka gama ganin kayan d y siyo ,hidaya t dinga yaba kayan tanaso tace wani Abu Amman Tana tunanin yadda Indo zata d’auki maganan,Dan haka tayi shiru kawai ,sunata yaba Kaya …
Ganin b undies sai najikin ta ,Amman aciki ba ko 1 tace oo namanta , gwanda ma d be d’auko min undies din ba hidaya , Dana shiga uku d kunya ai d bazan Kara kalon shi ba har n mutu ,suna dariya ita d hidaya ,hidaya tace keko zakiyita kalon sa munafurfur Tana tsokanar ta ,oho Indo Bata masan me hidaya take nufi ba Abin ta …
Hidayace tace Tana da wasu sababi guda biyu zata d’auko Mata gobe ta taho Mata dashi insha Allahu ,Dan wanan dogayen rigunan sai d kayan gyara yada komai zai zauna a mazaunin sa ,hidaya tafi Indo wayo sosai ,itako Indo bama tasan wani manufar hidaya ba ta Mata godia suka boye Kaya suka koma hiransu n duniya.
************
NAWAL bayan t gama chart ,ta samu bacci y dauketa Tana farkawa tayi wanka taci abincin t ,ta shirya ma mama karya d gaskia baya Abban ta y fita …
Wai safwan ne zeyi tafia ,shine zai kai su Noor hutu gidan Ammy ,Indo ma kakarta ba lpy shine itama tunda Nan gida yafi kusa d asibitin su shine ta dawo gida …
Mama harga Allah t yarda Amman Tana Jin wani Abu cikin ranta , Amfani d kafadi Alkhairi ko kayi shiru yasa take barin maganar , take kyauta Tama ‘yar tata zato ,Amman sai tace Akira Mata safwan din tamai magana meze Hana y bar su Noor din suzo Nan ku hadu wuri daya ai ba wani Abu …
Aiko hantar cikin , NAWAL ta kad’a ,ta dake irin jarumar Mai shirya film din Nan tace , aa mama ki barshi kinsan Abun dangin miji ba’a yi musu daidai Kar yace bama son yaran sa suje gidan Ammyn sa ,Dan kinsan ji suke d Ammyn Nan kamar ta gwal …
Mama tace ,eto banaki Taki ba ,yadda suke jikoki anan can ma haka suke ,sunfimu iko ma ,Kuma d kike cewa Ammyn su kamar t gwal ai duk d’an kirki Dole yaso mahaifiyar sa Kuma ai tayi ne arayuwa koni tana birgeni tsari d yanayin Rayuwar ta Yana burgeni wlh ,ke Ashe bakya ji Dani d har kike cewa uwar wasu kamar ta gwal to Ni t karfe ce Ashe ..
Aiko NAWAL t rankwafo ta rungume mama tace wlh Niko nakeji dake kamar ta diamond nakejin ki mamata tafi ta kowa fa ,uwa d ‘ya sai Allah, zuciyar mama fes taji dad’in kalaman ‘yar tata ,tace toh godia nake ,Amman a gayama SAFWAN din karsu cinye hutun nasu acan su rago Mana wani suzo suyi Mana anan ..