HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

NAWAL ta ninke mama tace ba Dole ma suzo ba mamata , mama tace zangaya ma SAFWAN din da kaina ma ,Dan yanzu zanga sintiri tunda iyalin shi na gidan Nan…

Jin mama zata d’ago ta ,NAWAL tace laa mama kin manta tafiya fa zeyi sai dai waya d zetayi …

Mama tace au na manta ,zamusha waya Kam Dan ma yaransa basa Nan d n gaji d gwarancin Haneef…

Allah dai y dawo dashi lpy, NAWAL ta ce Amin jiki a sanyaye har mama t kusa gano ta ..

Tace y dai NAWAL ?

Ta yi saurin basarwa tace b komai gajiyan Aiki ne be gama sakeni ba ..

 

Mama tace toh ki samu isashen bacci Mana ,ta tashi ta koma room d’inta cike d tunanin y zatayi t d’ebo kayanta a gidan SAFWAN……

 

 

*Maman shaheed*????????
[12/28, 7:07 PM] First Lady????: ???? *WRITING* ????

 

“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)

_Shafi Na Ashirin d biyar_

 

*MIJIN KWAILA*
“`Back again“`
_MAMAN MEENAT ALLAH YA BAKI IKO DA DAMAN CIGABA DA SAMBADO MANA MUNA ANTAYA KARATU_

????????????????????????

 

Bayan NAWAL ta koma dakin ta d’an taba bacci sanan t koma chart ,tanata nad’an bayan ‘yan Groups din su …..

 

Mama dai saitayi kamar zata tbmy NAWAL Abu sai Kuma ta saurara ,shiko Abbah ko ajikin shi y yadda 100% da bayanan ‘yar tashi Dan haka ba wani damuwa a tare da shi ……

 

“””””””””””””””””””
Huzna dai har yanzu neman inda zataga dogayen rugunan Nan take ,ta kasa gano inda suke ,har kayan su twins sai d tayi bincike aciki batare d kowa y ganta ba ,bataga Alamar nasu bane ….

Noor d haneef,d Janna sunata sauraron tatsuniyar d Indo take musu ,sunata Jin Dadi ,suna Mata tmby Tana Basu amsa …..

Ammy d su twins sunata sauraron su ,ganin yadda take musu tatsuniyar cikin hikima d kwarewa d nuna musu tarbiyar cikin tatsuniyar d yadda take Basu amsa cikin gwanan cewa gashi ada Ammy Tana tunanin batayi ilimin zamani ko kadan ba ,sai gashi tunanin Ammy na neman zama ba gaskia ba ,Dan haka tace Indo!

Indo t tsaida tatsuniyar tace naam! Ammy,

Ammy tace meye matakin karatunki ne kuwa Aisha Indo?

Indo tace ,nayi primary bayan n gama naci gaba d secondary zuwa junior section tunda nayi j.s.s CE banci gaba ba sakamakon wasu dalilai,nayi karatun Addini kadan y rage ban sauke b ,Kuma na Dan San wasu litatafai ,Amman inada burin cigaba yanzu insha Allah Dan Ina Tara kudin Aiki na ma Dan dasu nakeson ci gaba tare d tallafin Inna d sana’ar d zamu Kama nida ita in zanbar Aiki Dan bazan iya hada Aiki d karatu ba shiyisa zamu Kama sana’a d Inna tunda babana y Bata ,hawaye suka Dan zubo Mata lokacin d muryar ta ta raunana sosai cike d damuwa ….

Ammy d twins tausayin t y kamasu tun basuji tarihin Rayuwar ta ba ….

Ganin kuka n Shirin cin karfin ta ,gashi su Noor d haneef d Janna sunata son ganewa ko kuka take yi..

Dan haka Ammy tace su taso suje suyi wasa a dakin su d kayan wasa anjima Indo au Aisha daka yau ku dinga kiranta aunty Aishatu shine asalin sunan ta kunji yaran kirki ? Aiko sukace toh dama sunan ta Aishatu ake cemata wata indoooo? Suna turo baki suna neman amsar tbmy su a wajen indon?

Tayi kokarin hadiye kukan tace, eh Noor innata ce take kirana Aisha Indo ,daga baya take cewa Indo kawai shine kowa y d’auka ,Amman sunan Aishatu d mahaifina y rad’a min ,

Aiko suka sa tsale suna cewa daga yau Anti Aishatu zamu dinga ce Miki ai kinaso ko? Ta gyada Kai Alamar eh Tana musu murmushi d nuna godiyar so d suke nuna Mata a wanan gidan …

Ussaina ce tace maza aje wasa akwai sweet a gefen wardrobe kowa y d’auki 2 kubar min sauran d gudu suka tafi suna murna …

Hassana Ce ta kamo Indo t dawo d ita cikin su suka zaunar d ita tsakiyan su ,Ammy n kujeranta d ban ,sun manta d ma huzna na gidan tanacan Tana bacin asara bacin gado n rashin zuciya wai ka’ida sai tayi bacin a Rana so biyu ko uku kulin …..

Ammy CE tace Aishatu ,bani tarihin Rayuwar ki Kuma ki yi kokarin gayamin gaskia Kar ki boye min komai ,duk d nasan karya b halayar ki bace a iya Dan zaman d nayi dake a mu’amalance na Dan fahince ki daidai gwargwado..

Aiko Indo ta nisa ,Ido tab d kwala t Fara magana …..

Tana cikin Basu lbr ,sukaji sallamar Yaya safwan y shigo , Indo tayi nisa cikin lbr Rayuwar ta ko sallamar sa bataji ba balle t ganshi …

Ammy ce tamai nuni d hannu Akan y zauna ,Kar yasa indon katse lbr d take Basu Dan ta gama fahimtar girmamawa d taka tsantsan d yake tsakanin indo d safwan Dan za’a iyacewa Indo n tsoron sa tsoro irin na uban gida d yaron gida duk sun San wanan inda yake zaune ma Bata zama Dan girmamashi sadai in Ammy CE tace t zauna sai Tabi umarni ….

Dan haka y bi umarnin Ammy y zauna yanata Danna waya irin bashi d Abin saurare a Rayuwar indon Dan y fahimci Kan lbr d take Basu …

Indo ba Abin d ta boye ma su Ammy nadaga Rayuwar ta ,har Wanda Inna ta Bata lbr d Wanda ta sani d wayon ta har barin mahaifin ta garin d matakin karatun ta na ilimin Addini LITATAFAN d tadan sani n Addini d irin kokarin ta a fanni bitun Boko d Addini yayin da kuka yaci karfin ta d take Gaya musu sun hakura d Abban ta Dan ance musu ma wai ya mutu ,Bata d uwa Bata d uba Dan haka take d’aukan kanta marainiya kuka y sake kubce Mata hassana d ussaina n Bata hak’uri jikin su a sanyaye …..

Ba Ammy ko ussaina ko hassana ba hatta goga SAFWAN lbr y saukar Mai d wata irin kasala d ya rasa Dame ze kirata gashi bakin sa ko zuciyar sa ko kwakwalwar sa Basu bashi izinin furta komai akai ba saima korashi d sukayi duniyar masu tunani ,ga waya a hannun sa Amman y kasa latsa ta ,komai nashi y tsaya n wucin gadi…….

 

Su twins sunata rarashin ta , ganin baida dama ko ikon sarafa kanshi yasa y tashi y fice zuwa resting room Dan dogon nazari …….

 

Indo saida tayi Mai isar ta sanan tayi shiru tare d rarashin su twins…..

Ammy CE tayi ta Bata Baki d hakuri gami d nasiha d nuna Mata cewa zasu tayata addu’a indai mahaifin ta na Raye Allah y bayana shi inkuma y rasu Allah y gafarta Masa d mahaifiyar tata ……

Sanan ita Kuma Inna ,Allah y Cigaba d talafama Rayuwar su ita da indon ,Kuma tace Mata anjima sai suje ita d su twins su dubo Inna Dan ganin lpy ta ……

 

Indo cikin murna d zakuwa tace ,Amman na gode Ammy,Allah y Kara girma, Daman inason zuwa na ganta n rasa yadda zan tmby ne!

Ammy tace Damme? Keda kakarki daya tilo zaki ki tbmy zuwa dubo lpyr ta d kin Gaya min d tuni kinje wlh .,

Indo tace Naga momyn su Noor Bata barina naje ne sadai idan Inna Bata d lpy ….

Ammy tace sbd me?

Indo tace sbd Aiki !

Ammy tace wanan b daidai bane ,kice b duk sati kike zuwa duba taba ma Ashe?

Indo tace tab , bantaba zuwa n dubata bayan sati 3 bama ,Ni d zuwa wajen Inna sadai fa idan Bata d lpy ko Inna d’auki Albashi na, sai n kaimata n ajiye Wanda nake ajiyewa in ba hakaba bana zuwa kwatakwata wlh Bata Bari na naje .,.

Aiko Ammy bataji Dadi ba ,Nan ta Kara tabatar d Abin d su twins suke sheda Mata na azabtar d Indo d NAWAL take d kaskantar d ita d nuna Mata ita b kowa bace face Yar Aiki wahalaliya Mara ‘yan ci *KUSKURE* Ne wanan kowane Dan Adam yanada irin tasa darajar ,ba kasan matsayin sa ba awajen Allah ….

Ammy ta ce gaskia NAWAL Bata kyauta ba ban sani ba tuni d na gyara Al’amarin , hakan ai ba adalci bane ….

Ussaina tayi caraf tace , wlh aikin Aunty NAWAL yafi dahaka ma wlh ai dai ….,…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button