KUSKURE Complete Hausa Novel

Ammy t dakatar d ita d cewa ke banason surutu matar yayanki ce Akwai girmamawa a tsakanin ki d ita duk d Bata kyauta ba ,Kar n karaji …….
Sukayi shiru ,har hassana da take Shirin Kara nata bayanin t hadiye ,Indo ma shiru tayi …..
Ammy Ce tace suje su Kamala komai n gidan su shirya suje driver y kaisu su gaishe d Inna har su Noor m ashirya su ,sukace too murna fal cikin Indo ….
Kitchen suka fada suka shiga Taya iya Aiki ,suna cikin aikin hidaya tazo Indo d hidaya suna murna d ganin juna suka gaisa suka cigaba d aikin ..
Indo t gayama hidaya zasu gidan su d su twins gaishe d Inna ,Aiko hidaya tace wlh d ita za’aje Dan wanan zumuncin d ita za’ayi har take rad’a ma Indo doguwar rigar d zata sa da takalmi, su lndoo har anmanta d wasu dogayen riguna ma sai yanzu d hidaya t tuna Mata …,.
Bayan sun kamala komai ,saura Shirin fita zuwa gaishe d Inna …..
“”””””””””””””””
SAFWAN Ko tun komawar shi daki ba a ba kwanyar shi sukuni ba …
A zahiri y matuk’ar Jin tausayin Indo d Rayuwar t d duk wani Wanda yake kewaye d Rayuwar ta…
Amman Yana tuhumar kansa danme ze damu d Rayuwar ta haka g Abin d y kamata y dame shi can Rashin NAWAL !
Can Kuma yace hmmmm NAWAL din me , tunda t zabi Aiki Akan Shi har iyayen ta ma Ashe tunanin su iri daya ne,shima ko ze nuna musu da Dan halak sukayi ….
Kuma ma me ze dameshi yana tare da farin cikin shi yaranshi ,ga Kuma Mai kula Mai dasu ko uwar da ta haife su Albarka …..
Kai ma Ai Dole y Kuna nutso cikin damuwa d Rayuwar Indo ko Aishatu d yaji Ammy ta furta ,? Dan itace komai n yaran shi tun daga haihuwar su har kayau , ai gaida Mai gaisheka ko bace amsa ba , Dan Tana taimakama yaran shi ne kawai dalilin tausaya Mata …..
Ya jima Yana tunani akan Indo d Abin d y shafi yaran shi ,ganin tunani y Hana shi sukuni yasa ,ya gayaci baccin Dole ko ya Sami sasauci……
*Maman Shaheed*
[12/28, 7:08 PM] First Lady????: ???? *WRITING* ????
“`MAMAN SHAHEED“`
*KUSKURE* ????????♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)
_Shafi Na Ashirin d shida_
“SAFWAN” be farka ba saida yayi Ana kiraye2 sallah sanan y tashi y tafi masallaci…
Su twins sun shirya tsaf ,hidaya tacema Ammy zata itama ,Ammy tace su dawo lpy iyaa ma tace Adawo lpy ,su Noor d haneef d Janna karamar Babar su Noor sunata murna zasu unguwa kunsan yaro d son yawo ..
Indo ashiga cikin doguwar Riga yaluwa (yellow color) ta rolling brown veil ,tayi kyau matuka tare d taimakon hidaya tasa flat sheo d’in ta fuskar ta d’auke da fara’a wacce ta yalwata fuskar ta ,tayi make-up d’in ta wala’ba’asa (ba laifi ) tayi kyau matuk’ar kyau d kaganta kasan Tana cikin farin ciki bayanane….
Duk suka fito sukama Ammy sallama ,Ammy tabada sako a Leda taba hassana tace su ba Inna suce Tana gaishe ta ..
Suka karba , Indo t farama Ammy godia d Addu’a ,Ammy t dakatar d ita ta hanyar ba komai Kar ki damu ,kuje kuyi maza ku dawo ….
Har sun Fara tafiya Ammy ,tace hassana y baku yima huzna mgn ba ,kartaga kamar kun ware ta ,gaban Indo sai d y bada daram!…
Hassana ma tasan ba zuwa zatayi ba , ussaina ce tace ,Ammy bacci fa takeyi Kuma tace in aka tashe t Tana bacci kanta ciwo yake Mata shiyisa muka kyaleta .
Ammy tace ok, haka wani yake Kam bayaso a katse Mai bacci sai kansa y Sara ,toh kuyi maxa sai kun dawo ku nemi driver …..
Kafin su twins su fita Janna t dawo d gudu Tana cewa ,driver baya Nan wai ankirashi Kiran gagawa a gidan shi ….
Ussaina aka zuciya aka nufi hanyar fita don Jin dalilin d baze fada musu uzirin shi tun wuri ba ….
Ammy Ce ta dakatar d ita d cewa tsaya ,ta saka hijab suka nufi wajen baba Mai gadi …
Mai gadi n ganin Ammy y Fara Mata barka d yamma , ta amsa cikin sakin fuska hade d tmby shi uzirin driver …
Baba Mai gadi ,yace wlh muna tare tun d’azu su kawai yake jira ,yanzu aka kirashi wai yaron wajen sa ne me babur y Kade shi kamar Ana zargin y Sami gocewar Kashi ,shine yace bari yaje y gani yanzu ze dawo n baku hakuri kafin y dawo ….
Amman barin kirashi naji ……y d’aga waya zai Kira ….
Safwan y shigo gidan y dawo dg sallah …
Ammy ta dakatar d baba Mai gadi d Kiran d zema driver ..
Atake t ummarci SAFWAN da y taimaka y kaisu su ,
Yace Ina zai kaisu ?
Noor d haneef suka bashi amsa d gidan Inna wacce take bamu Aya d gyada me kirkin Nan d kace itama kakar muce Inna aunty Aishatu (Indo) Dady Dan Allah ka kaimu kaji?
Ya gane inda zancen y dosa ,Amman yace ma Haneef wace Aunty Aishatu Kuma?
Janna tace “lndo “Ammy tace mu dinga kiranta d anti Aishatu shine sunan t n gaskia ,Jin sunan yayi har cikin jinin shi d bargon shi d y rasa dalilin hakan ..
Ammy CE ta katse su d cewa ,Dan Allah kayi ka kaisu b jimawa zasuyi ba sai ka dawo dasu matuk’ar hakan ba’a shiga sabgogin ka ba driver ne wlh yaron say gamu d tsautsayi kaga Kuma tsautsayi Yana Kan kowa ..
Bashi d zabi ga su Haneef nata Mai nacin y kaisu , haka ya hakura kodan su Noor yace kumuje na kaiku ….
Sai a lokacin y hango Indo cikin wata mayar doguwar rigar d y shiga tantama shin Anya shi y siyo d hannun sa ? To ai shi daukowa yayi b zaba ba kawai ,Amman sune sukayi kyau….can kuma y kwabi tunanin shi d Kar y zarce yaje inda ba’a tura shi ba ,Yana Kara Satan kalon ta …
Itama Indo ajiyar zuciya ta sake d taji y amince zai kaisu kodan Kar farin cikin ganin Inna y koma ciki ….
Su twins baya suka shiga har hidaya ,Indo Tana Shirin shiga bayan ganin Haneef y shiga gaba kusa d dadyn shi , hassana ce tace Mata Indo gaba Zaki shiga Dan kece kikasan gidan ke Zaki nuna layin d gidan tunda mu ba sani mukayi ba…
Safwan beso hakan ba ,Indo ma ji tayi wani iri wani banbara kwai namiji da suna hajara lol, Amman Bata d zabi Jin muryar safwan na cewa kefa muke jira ,da sauri ta shigo Tana sunkuyar d Kai k’asa ,Haneef nata murna y matsa t zauna y jinginu d jikin ta Yana Mata Hira …
Mai gadi y bude musu gate ,suka Cinna hancin mota sai hanyar gidan Inna……
Suna tafiya Haneef yaga Mai sai d Apple, mango,banana, fruit dai komai Akwai a gefen titi ,Haneef yace a siya Mai har yanama dadyn shi magiya …
Dadyn nashi yayi dariya yace Kai kadai za’a saima Banda su Aunty Janna d sis dinka Noor?
Yace harda su Amman nawa yafi yawa ,ko Dady? Yace Kai Haneef Banda son Kai fa , Noor tace barshi Mana yaro n girmeka nawa ne zefi yawa su twins nata musu dariya har Indo d hidaya ..
Safwan parking yayi y ce Haneef din y fito suje asiya y nuna Abin d yakeso ,Indo t Miko Mai shi har hannun su n gogan n juna ,wani bahagon sak’o y shiga sasan jikin su indon d safwan din duk suka rasa gane kome hakan yake nufi ,yasa Haneef suka tafi …..
Leder 3 yayo Niki Niki d kayan fruit…y mikama su twins 2 y mik’oma Indo daya batare d y cemata komai ba ,itako ganin cewa Akwai waje a gabanta ne yasa y Miko Mata ta ajiye Mai ,Dan haka t ajiye d niyar in suka sauka t cemai g ledar sa …
Suka shiga sukaci gaba d tafiyar ,tare da taimakon Indo suka Isa har kofar gidan Inna…
Suna Fara fitowa sukaci Karo d nawara kawar Indo ,tanata bin su d kalo Tana Shirin shiga gidan Inna ,ganin Indo a cikin su yasa nawara dawowa d baya ,Aiko indon itama t ganta d gudu nawa tazo ta rungume Indo Tana cewa kawar zuwa ba sanarwa ?
Indo yayi murmushin farin ciki tace wlh zuwan ne yazo min kawai …
Indo Ce tace ma su Haneef d su twins su taho su shiga Tana kamo Janna d Noor Haneef dama Yana hannun ta ,