HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Aiko ta tambayeta dalili Taki fad’a , Safwan ma y tambayeta tace bakomai , yace t kara hakuri indai Bata d dalili tace toh , har y Mata Karin Albashi tayi ta Mai godia sanan tace zata gd ta kwana biyu Dan innan t batajin Dadi nanko karya ta musu ,safwan y jajanta Mata yace taje ba wani Abu lpy ai tafi komai itama NAWAL ta d’an tausaya Mata Dan tasan Tana aikatuwa ‘yar , sanan SAFWAN y biyata Albashin t lokaci ma Bai cika ba tamai tuni ita indon yace b damuwa sbd yasan karamin karfi ne dasu y Bata wasu kud’in yace ta kaima Inna ,haka tayi tamai godia ta tashi t tafi tace ranar litinin zata dawo dake yau juma’a

 

*BARI MU GANI INDON ZATA DAWO KUWA*?????????????????????????????????????????

 

Maman shaheed????
[12/28, 6:59 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`BY MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki ko Matar gida_)

 

_shafi na biyar_

 

Cikin Farin ciki da zumud’i t samun hutu n kwana biyu Indo ta tafi gd ,Tana Isa t labarta ma Inna duk yadda sukayi da iyayen gdn nata Bata b’oye Mata komai ba …

Inna tayi salati , tace ohh ‘yanan Kika d’oramin ciwo , tace ai ba sab’o nayi ba inna ai kina d’an zazzab’i wataran , Inna tace kinci gdn ku ina ga yak’i kina ga k’ura ‘yar k’otar wuk’a kawai ,Tana dariya …..

Indo taba inna Albashin ta gaba daya harda kud’in d Dady su Noor y Bata taba inna , Inna t dinga murna Tana samai Albar ka dama kayan Abincin su sun kare , awo sukeyi ,Inna tace kema ki dauki wani Abu bakince Zaki sai kayan kwaliya ba d material d’in rariya d akata yayi ke bakiyi ba ?

Aiko Indo tace eh wlh har kin tunamin kud’in d nagani ne yasa na rud’e ai ,Inna tayi murmushi tace aikya rud’e ‘yar Nan Nima Naga Aukin kudin ,Dan haka gobe sai Aziza ta rakaki ku siyo a kasuwa dg Nan Kya Mana awon su dawa ,gero ,rogo Dan mudinga d’an wake ,dasu filawa Dan in kwad’ayin mu y taso mu kwantar dashi ,dama gaki d kwad’ayin wainar filawa ,in su haleeme na toyawa Kita tsaki to kin ci ki Mata cin k’oshi ,d y’ar shinkafar mu t hausa, Aiko Indo t kwashe d dariya Tana murna t fad’a cinyan Inna ….

Washe gari t tafi kasuwa tare d rakiyan Aziza suka gama siyayan su kala biyu ma ta siyo rariya material din ta sai musu takalmin roba iri daya d Azizi t Bata Aziza nata murna Dan dama Tana son takalmin Bata d kudin siya …..

Gdn su Indo d Inna y kasance cikin Farin ciki saka makon ci 3 a wuni baya wuce su Yanzu …..

Kwanakin Indo sun cika yau zata koma Aiki litin , Aiko tayi kicin kicin da Rai ,Inna ta gama gano ta, Dan haka tayi ta aikin rarashi Tana Bata baki t Mata Alk’awarin zata Kai Mata dikin material d’inta ,Aiko ta d’an saki Rai , har t gama shiri , still Tana Jin kamar Kar ta tafi dan ba komai take tinawa ba illa wahalar aikin gdn d sakar mata komai d akayi na gdn …..

Haka ta lalab’a ta koma .

**************
Barin Indo gdn ba karamin wuyar hidimar gdn NAWAL ta Sha ba Dan ji tayi kamar taje t dawo d indon ,SAFWAN ne y dakatar d ita daga k’udirin ta , Aiko t ji jiki ta sancewa Indo b k’aramin jigatuwa take d aikin gdn ba , gashi Noor t Bata ko Ina ,har Dena Bata kayan wasa tayi wai Tana Shan wuya wajen kwashe wa sbd haka t ke hanata wasa dasu wai sai Indo t dawo (Sha wuyan gdn)…

Indo taji haushin dawowan ta gdn bauta, itako momyn su Noor (NAWAL) Farin ciki tayi matuk’a Amman girman Kai Bai barta t nuna ba Kar ‘yar aikin ta ta Raina ta …,.

Indo Bata wani hutaba t fito t fara sana’ar Aikin gdn , Dan ma NAWAL ta rage Mata wasu d taimakon SAFWAN haka rayuwa taci gaba da tafia ,NAWAL Na ba Indo ummarni ,Indo na hidima d yara d dadyn su har Haneef y girma aka yaye shi Dama NAWAL tasa inflan ahannun ta Dan planning tun bayan c.s d’in da aka Mata d watanni wai karta Kuma samun ciki b shiri ,bada son ran SAFWAN tasa b ,ganin irin wuyar d Tasha yasa ya barta d sharadin za a cire Mata b sai yakai shekarun sa ba , tace t Yar da ….

Dan haka Tana final year d’inta , su Noor anata makaranta shima Haneef an tsundumashi a play group, Indo t Sami sauki hidima d su .

Mumyn su Noor nata murna sun kusa fita ta fara Aiki strike y kawo musu ziyarar bazata ,sai d suka shafe watanni Ana d’auki b dad’i ,daga baya aka janye ..

Yanzu haka sun koma satin su daya d komawa , Indo tanata hidimar yara

 

*CIGABAN LABARI*

Cikin kwarewa d gwanancewa d juriya Indo take gudanar d hidimomin gd ,yayin d mumyn su Noor t sake ragamar gdn hannun t , take tafiyar t makaranta batare d shayin komai ba , mussaman yadda Rayuwar Nan t zama sai Addu’a ,..

Yauma kamar kullin dadyn su Noor y gama Shirin tafiya office tare zasu tafi d mummy su Noor ze dropping d’in ta sai y wuce ,su Noor ko sun Jima d tafia school Dan school bus ce take d’aukan su 7:30 kullin …

Dan haka mummyn su Noor ta fara Kora Mata jawabi Kan t tsaftace ko Ina n gd t k’alk’ale har toilet din dadyn su Noor d bedroom din ,sanan t koma nata t gyara Mata shima ,sanan t gyara gd ko shayin lisafowa batayi ,shiko tuni yayi gaba y barta d lisafe lisafen ta Dan gab yake d k’udirar aniyar seta Rayuwar NAWAL ayanzu (nidai nace tab ka makaro ai) Dan y fara k’osawa d wasu d’abi’un ta ,sanan t bishi bayan t gama korama Indo jawabi suka tafi y sauke ta makaranta.

 

Indo injin tagumi ta rabza Tana karema gdn kallo Tana hararo aikace aikacen d zatayi ,tanata sak’e sak’e cikin ranta har d ‘yar k’walla a indon ta ….

 

Bayan t gama karanta wasik’ar jaki ta tashi ta fara aikin t ,kwakwalwar ta cike da tunani iri iri Kan wasu burikanta na rayuwa guda 3 da take fatan Allah y cika Mata su .

 

Haka t gama hidiman gdn har launch ta gama musu .

Yau dadyn su Noor be dawo ba , su Noor ne suka Fara dawowa sanan mummy su ta dawo itama ta kwashi girki, Indo t sallami su Noor Dan tafiya islamiya d d’an bala driver…

Itako hakimar ,kwanciya tayi bayan sun gama waya d dadyn su Noor sunata musayar kala Maina lovayya.

 

Bayan wasu watani , NAWAL ta gama karatun ta sun zana exam lpy , ta d’an Sami Nutsuwa a gd , Amman fa ko tsinke sai taga Daman d’aukewa sanan zata d’auke ,ga zaman gdn har y fara gundurar ta Dan tace zaman gd tsautsayi ne inji wasu ma aikatan fa Amman …

 

Dan haka yau t tafi unguwa gobe t zauna agd ,yaranta ko dumin jikin ta ba sosai suke samu ba Dan haka sukafi shakuwa d dadyn su Dan Yana jansu ajiki sosai har wasa sukeyi na goyo d cakulkuli suta kyakyata dariya , sai Indo itama suna wasa d Hira suna samun kulawa daga gareta Dan sun sake d ita sosai ….

Yaya Ahmad wan SAFWAN dadyn su Noor y samo matar Aure an gama komai bikin ma y rage saura 2mth ,SAFWAN nata ma su twins tsiya wai Suma su fito d miji ayi awuce wajen ,Ammy ce tace Kar y damesu ba yanzu ba sai sun gama karatu sanan ,sukayi dariya har yayan sukace ayi karatu lpy Allah y bada ilimi Mai Amfani ,suka amsa d Amin gaba d’ayan su …..

Su twins tare suketa Shirin bikin Yaya Ahmad d ita (Aunty NAWAL)aka siyo anko d duk wasu abubuwan buk’ata na bikin ,da kyar t Bari su twins suka siyama Indo Mai Aiki Ankon bikin har kala 3 ,wai ya za’ayi Susa Kaya tasa inji mommy su noor alhalin matsayin su b d’aya ba.

Nan su twins suka Kara gane ,kaskantar d Indo d takeyi ,Nan suka nuna Mata ai ba wani Abu , haka suka dinga Fadi in fada Amman bamai zafi ba Dan ba ta sigar fad’a suke Mata ba ,Dan Akwai girmamawa atsakanin su sosai haka suka dage suka dauk’an ma Indo har d’in ka Mata suka d’auki nauyin yi ba tare d sanin AUNTY NAWAL d’in ba …..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button