HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Safwan n cikin mota idon sa kirrr….Akan Indo ya kaleta y Kali yaranshi d farin ciki y bayyana a fuskar su Yama rasa gane murnar me sukeyi d zuwa gidan su indon ,can Kuma yace Koda yake shimfidar fuska ai tafi ta tabarma , Yana Kara binsu d kalo ..

Su twins sunyi gaba har hidaya ,safwan ne y Kira Indo d sunan Aishatu Wanda shikansa besan sanda yayi Amfani d Abin d zuciyar sa ta ayyana Mai ba ya jefar d Abin d harcen sa yaso furtawa wato (Indo) …

Ba Indo ba kowa sai d y waigo Dan y tabatar Kiran sunan daga bakin shi y fito ,Aiko kowa y tabatar shine y Kira ,sunan y zauna a bakin shi kuwa g iya fitar d sunan d yayi ,Indo dai ganin tabas d ita yake kudun Kar ta bada shi yasa ta zuwa tace naam dadyn su Noor cikin wata kasalaliyar muryar ..

Muryar ta sakar Mai d sakonni da dama a jikin shi ,da wata irin murya Yana Mata wani irin kalo, kalon d Saida ta shiga firgici…

Yace wa Kika barma ledar Nan?

Tace au inace takace ai..

Ya Mata wani kalo , ai Dole ta zama tawa tunda g biri natacin wanan uwar ayabar zuwa Nan d sati biyu na cinye , dariyace ta kusa kubcema Indo Amman Kar yace ta Raina shi Dan ba kowa ne yakeson dariya ba in yayi magana , Dan haka tace in d’auka in shiga dashi ne,?

Ya d’auke kanshi gefe yace in kinyi ra’ayi ba , inko Baki yi ba ki Bari har asamu Mai d’auka y shigar Mata dashi ..
..

Jin kalaman shi yasa ta gane n Inna ne ,Dan haka Kar maganar tayi tsayi gashi Ana jiranta yasa t d’auka ta Fara jero Mai Addu’a….har Saida y dakatar d ita d wani salon kalon d NAWAL kawai yakema irin kalon ….

Shiko besan ma yayi ba ,itako Jin wani Abu bako atare d ita yasa tayi saurin barin wajen ta nufi inda su twins suke jiranta ..

Da sallama suka shiga ,Inna n ganin su ta karbe su hannu bibiyu tanata murna Tana cewa su Noor su matso kusa d ita…..

 

Aiko Nan su twins suka Fara gaishe d Inna cikin kulawa d fara’a take amsawa ..

Sun Sami gidan tsaf tunda b yarane d ita ba komai kalkal tanata tuyar wainar filawa wai tayi sha’awar ta …

Dan haka tace ma Indo tazo ta Kara kwaba kulin wainar ga filawa a roba tayi maza ta soya musu Dan gidan y gauraye d kamshin wainar taji Albasa Mai ganye d attaru Tana fita gwanin sha’awa …

Hassana ce tace laa Inna da
Kin barshi akoshe muke …

Inna tace haba ‘yar Nan ai abar sha’awa ce kwa maida yawu ga kamshi duk y cika gida saidai ko in bakwa iya cin girkin mu yaku bayi ,Jin haka ussaina take laa wlh aa Inna ko daya a duk daya muke atoya zamuci…

Inna tace toh yanzu naji Batu g filawa ga yaji dazu Yar Albarka nawara taxo ta daka min shi Ashe Kuna hanya. …

Indo d nawara d hidaya nata hada kayan wainar wani n toya sairan kulin wadu Kuma n kwaba sabo wani n yanka Albasa …

Bayan hassana t mikama Inna ledar d Indo t ajiye batare d tace Mata komai ba ,tace inji Yaya safwan yace abaki ..

Aiko Inna tayi ta shimai d Albarka ,Tana ma iyayen shi Addu’a sunji Dadi sosai ..

Noor ko d Hannah d Haneef Inna ta cikasu da data d karass sunata ci suna nishad’i …

Nan d Nan aka Fara soya wainar nawara CE Mai suyan Tana mik’oma su twins sunata ci cikin Jin Dadi d nishad’i Abin su Nan d Nan suka Saba d Inna wata shak’uwa ta shiga tsakanin su ,kamar b yau suka Saba ganin juna ba …

Sunci sun koshi sanan suka wanke manjan hannun su , Inna ta Basu su kantu Mai siga d Mai gishiri d Aya d gyada har su hanjin ligidi ,su Noor sunata murna zasu sha Dadi in sun koma gida .,..

Sukama ,Inna sallama bayan sun Bata sak’on Ammy Nan ma addu’a tayi Tama Ammy d Abban su ,tamusu fatan Isa gida lpy , har Tana cewa agaida uwar d’akin Indo hajiya NAWAL ,sukace zataji …..

 

Suka doshi mota Dan komawa gida , safwan na gaban mota yanata Danna wayar shi wai har yaje wajen abokin shi yanzu shima y dawo , Indo d nawara badon sun so ba suka rabu d Alk’awarin Indo na Nan zuwa bayan an kwana biyu …

Yadda suka Zo haka suka koma suna baya Indo d Haneef n gaba ….

Koda suka shiga ,huzna na zaune a parlour ta gama baccin asara ,tanata Shan kamshi ..

Taji haushin fitar su d Kuma zuwa inda sukaje ,Tana ganin hakan kaskanci nee zubar zubarwa Kai d kima su rasa inda zasu wai sai gidan su Indo Mai Aiki wahalaliya boyiboyi …

Harda safwan d take kalon kamar y waye Ashe tsako ne ?

Harda su Noor sai kace zasu wani irin outing dinan irin zasu yawon zaga gari dinan …tir …

Bata Kara firgita d shiga bacin Rai ba sai d tayi tozali d Indo d rigar d tafi so acikin kayan d taketa so da sanin na waye acikin gidan,…..

Bacin Rai d takaici karara ba sayawa a fuskar huzna ,gaba daya kwanyar ta ta shiga rud’u shin indon CE wai ? Kuma dama kayanta ne? Safwan y siyo Mata? Kodai Ammy CE ta bashi kudi y shiyo Mata? Dan NAWAL ko Indo zata tafi tsirara tasan bazata sai Mata wanan zuka zukan rigunan ba sadai ta tafi tsirara …

Kai Ina badai safwan bane y siyo Mata kayan Nan , indon ? To ai daga wajen shi aka taho d kayan Kuma ance na sako NE kamar yadda hassana ta shaida Mata ……

Kai Aiko sai ta tabatar sanan zata yanke hukuncin Dan haka ta d’auke idon ta d’aga Indo Dan samun sasauci …

 

Suko sunata ba Ammy lbr karamci irin n Inna d Abin d ta Basu ,twins hidaya Indo duk su suka Fara yima huzna magana t amsa na hassana d ussaina Amman Taki amsa n hidaya d Indo ..

Hidaya dai yatsina Baki tayi ta tafi wajen iyar ta ma …

Indo ko waje ta nema ta zauna tanata gayama Ammy sak’on godia d Inna ta Bata .,….

Ammyn nata cewa ba komai yima Kai ne , huzna nata Jin haushi yadda suke ma indo d iyayen ta suna d’aukan kansu daya salon ta Raina su ,Anya Indo Basu mallake su Ammy ba d asirin su irin na matalauta ? Wanan shine tunanin huzna .

Shiko safwan masalaci y nufa ganin magriba ta yi…..

 

 

*MAMAN SHAHEED*????
[12/28, 7:08 PM] First Lady????: ???? *WRITING* ????

 

“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_Shafi Na Ashirin d bakwai_

 

“`Mum meenat tafiyar tamu ba irin tasu bace ,so ne na tsakani da Allah ,kedai cigaba d sambado Mana “` *MIJIN KWAILA*????????????

 

“`AUNTY ZULAIHA AMSHI Nagode da sadaukarwa , Allah yabar Zumunci ya Raya Mana zuriya“` *AMINAU BAIWAR*
“`Acigaba da gashi Yana kawo light har sai sak’on ki y Isa inda Kika turashi zamu daina bibiya“`????????

 

“`Bilyn Abdul Kuma ta,kinzo Mana da sabo Mai ilmintarwa muna biye dake, Ana tare iya wuya“` *Siyasa Ko Kabilanci* “`Allah ya Baki ikon d hazakar ci gaba da antayo Mana muna antayawa muma“`????????

 

“`my first lady(ummah shehu) muna biye da kefa a “` *MUHAMMAD NAMADI*(My dream) “`cigaba d Aiki muna duba Miki Yana kyau yadda y dace“`????????

 

“`AMNOOR Tawa kina kamshi muna binki d ALHARAMAIN ,littafi n nishad’antuwa wa gami da wa’azantarwa“` *KUSKUREN DA NAYI* “`Takai tace kamar yadda kikace Amman zamuso y zama Mai tsayi “`????????

 

Shiko safwan masalaci ya nufa ganin magriba tayi….

 

Bayan safwan ya dawo dg sallah ,Ammy ta umarci Indo d takaimai Abinci inkuma tafiya dashi zeyi Kuma to, ta dai tmby shi t had’a Mai Dan tasan mommy su Noor ta tafi Aiki yanzu ,cikin bin umarni badan taso b ta tafi ta tmby shi…

Cewa yayi aa ta zuba Mai ya tafi dashi yanaso isha’i tamai a gida Dan Akwai aikin d zaiyi n office dinsu through internet…..

Yana yi Yana binta d wani kalon d besan Yana yi ba ,atunanin shi kalon tuhuma ne d tantama Akan shidai b zabo kayan jikin ta yayi b toh Amman danme kayan zasu zauna Mata kamar irin wani end of d class y dauko Mata dinan ,shi gaskia kawai daukowa yayi kamar wani ne y tsare shi yake tuhumar shi …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button