HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

 

Waima Ubanme y kawo ki gida na?bakiji me nace Miki bane ,ko kin d’auka sakarai ne Ni me magana biyu kamar yadda kike sakarya?

Waya kirakiya ? Bance ki wuce gidanku ba ? To bancanja ba kije kici gaba d duk abinda kikasa agaba Wanda kikaga Zaki iya ,tunda Naga Alama baki d control ko acan …

.Aiko NAWAL tayo cikin shi d masifa wai Kar y zagamata iyaye …..

Yace nadai Gaya Miki ,kiyi gagawan barn gidanan Kuma wlh Dan ba gidan hadin gwuiwa bane bare kice tare muka siya …

NAWAL t karema gidan kalo tace, wanan Abin har shine Abin takamar ka safwan , to kayi gagawa dawo d wacce zata maye maka gurbina “oooo n manta g Indo ma ai ko?

Naga tafi Kama d class dinka , ina jiran katin gayata sanan zan Kara tabatar d cewa da Dan halak safwan nayi…,..

Fuuuuu!
Ta tafi d’ebo kayan ta Don barin gidan…

Shiko cewa yayi kwarai kuwa wacce Kika Raina tafiki d komai ,karamin mutun Ce Mai babban tanki ,keko babbar mutum Ce da k’aramin tanki , Dan hakin d ka Raina yakan tsolema ido ki tuna wanan .,..,…

 

Bayan t dibo kayan zata fita tace , Ina jiran gayatar gagawa fa ?

Safwan yace hmmmmmmmm Allah y Mana maganin jayilci , kinyi d Dan halak yarinya ….

Juyowa tayi tace yariya Tana bayan uwarta fuuuuu tayi waje ……garammm ta bugo mai k’ofan parlour…..

 

*Maman shaheed*????
[12/28, 7:09 PM] First Lady????: ???? *WRITING* ????

 

“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_Shafi Na Ashirin d takwas_

 

“Safwan dai Ranar kwana yayi d tunani iri iri ,zuciyar sa t kasa samun sukuni ta tunanin makomar yaran sa d y cika Mai zuciya”

Wata zuciyar ce tace Mai ,Mai zai dameka Dan karabu d wacce damuwar d abnin d tasa a gaba nadaga aikin t yafi tarbiyar yaranka d Basu kulawar d duk wata uwa y kamata ace tanaba yaran d suka fito dg tsatsaon ta?

Tun b yanzu bafa haka take ,ai yanzu kamar wani yunkuri kayi n ta gyara *KUSKUREN* Ta Amman taurin Kai d tsageranci d jin ta Isa ita watace yasa d shafawa fuskarta toka ,yaushe zaka cigaba d zama d wacce Bata d’auke ka Miji ba ,baka Isa k hanata t hannu ba ,bafa yanzu akeji b gaba akeji in kun Kara Tara iyali ,kaga ko zaman sai Abin d Hali yayi kawai , safwan yayi na’am d kalamai d maganganun zuciyar shi …

D taimakon Addu’a y samu yayi bacci aranar ……

“”””””” bayan isar NAWAL gida ,tayi sa’a mama Bata parlour hakan y Bata damar sanda zuwa d’akin ta jibge kayan d t lodo gidan safwan nata ..

Zuciyar ta cike d takaici d bacin Rai d ta ki yarda d Amincewa Akan na korar d mijinta farincinkin t ya Mata ne , Wanda kowa yasan hakane ..

“Sai daga baya t fito parlour ,taga mama Tana kalon TV shine itama t zauna t Fara kalon ….

Mama tace yaushe t shigo ,tace dazu mama inata salama bakiji b shine n wuce naje n gabatar d sallar isha’i,mama tace yayi kyau Allah y karbi ibadun mu,tace Amin..

Ganin NAWAL cikin wani yanayi n dogon tunani ,mama n kula d ita,tace y dai NAWAL lpy naganki wani iri?

NAWAL t kakalo murmushin Dole tace lpy wlh..

Mama dai shiru tayi Amman Tana zargin wani Abu …

Can mama tace Niko NAWAL kina neman su Noor kuwa a waya banji kunyi waya ba ?

NAWAL tace laa mama muna waya dasu ai ko dazuma munyi waya ….

Mama tace kiramin su Nima naji lpy su …

NAWAL hannu n rawa t d’auki wayar t Fara laluben Wanda zata Kira ,tasan dai suna gdn Ammy duk d cikin bakar maganar safwan t gane hakan ..

T Fara tunani Wanda zata Kira ,Ammy? Aa sadai hassana Dan ussainan Nan m wani lokaci Akwai fitsara .,..

Tanata Addu’a cikin zuciyar t kan Allah yasa wayar Taki shiga ta Fara Kiran wayar ko Taki tafiya matsalan” network “is not reachable” hakan y faranta ran NAWAL t confidence d’inta take gayama mama wayar yaki shiga …..

Mama dai n son tabatar d wani Abu a yanzu ,yasa tace bani wayar naji t karba ta Kira number still dai “is not reachable ” mama tace network problem ne maybe Inna gwada Kira d tawa Kuma y tafi kinsan wani lokacin akan samun haka ..

NAWAL kamar t sa ihu ko t Hana mama ,Amman b yadda zatayi Dole t hakura gashi Abban t baya gida d yake giya Mata baya mama ko yanzu zata gano t ta cimata mutunci Tana ganin damar t korata gidan mijin t indai tasan sabani suka samu kafin Abbah y dawo ….

Dan halak NAWAL taci gaba d Addu’a ,Allah yasa tata wayar ma Taki shiga ..

Mama n dailing number a phone d’inta akaci sa’a t Fara ringing ,ran NAWAL kamar y fito t daskare a zaune ..

Hassana tayi sallama Bata d number maman NAWAL..

Mmn NAWAL t amsa ,hassana t gaishe ta ,…

Mmn NAWAL t karbi gaisuwar ..

Mmn NAWAL tace ,Baki gane Mai magana bako ‘yan biyu so nake naji lpy su Noor d maman taku tunda t kwace min me gida ….

Hassana d mama muryar su asake cikin Raha ,hassana tace last mama sai yanzu na gane y gida yasu Auta?

Mama tace lpy suke , hassana tace ga Noor din ai muna tare har Haneef din Ammy CE dai take daki ….

Mama t Fara magana d Noor bayan t gaishe d mama tanata Mata surutu wai zasuzo ai ,sanan akaba Haneef shima surutu y dinga ma mama su Hassana nata dariya d Indo ,itama NAWAL ganin mama bazata Mata tayin magana d yaranta ba yasa tace mama bani shi …..

Maman Tana sane Taki Mata tayin magana d su Akwai manufar ta akan hakan ,

Sanan t ba NAWAL din …..

NAWAL n Jin muryar Haneef tayi ajiyar zuciya ta Kara tabatarwa d yaran Ashe Tana jinsu har ranta ,sun Jima suna Hira Tana tmby shi yaushe zamuzo gidan mama ,yace shi baze Zo b suna tare d Indo a gidan Ammy sunata Jin Dadi Kuma sunje gidan Inna aunty Aishatu ma ta Basu kayan Dadi d yawa ….

.tun lokacin d Haneef y Kira sunan Indo annuri d farin cikin NAWAL suka gushe ,atunani d shirmen ta ta bada GUDUMAWA samun sabani tsakanin t d mijin ta safwan ,Dan haka tace ma Haneef y Bata Noor su gaisa ….

Dan shi t gama d sabin sa sakamakon sunan Indo d y Kira ,

Noor n karba t Fara gaishe t Tana cewa momy yashe zakizo gidan Ammy?

NAWAL tace Ina Nan zuwa my Noor Aiki Ne yake hanani sukuni ,Kuma ai zakuzo gidan mama ko ?

Noor …..tayi shiru kamar Mai tunani …Indo t gama karantar yaran tsaf fiye d uwar d ta haife su ,ganin Noor tayi magana Indo t girgiza Mata Kai t Mata Alama d Kai Akan tace eh ,Dan duk sunajin hirar nasu ….

Sanan Noor tace zamuzo Amman d Aunty Aishatu zamuzo d su Aunty twins…

Cikin murna d farnciki ,NAWAL take cema Noor ..

My Noor….wace Kuma Aunty Aishatu?

Noor tace laaa momy Baki Santa ba?

NAWAL tace eh my Noor ,wacce ce?

Noor Tana kalon Indo tace aunty Indo Ce fa ,Dady yace ta girmemu mu dinga ce mata aunty Indo ,yanzu Kuma Ammy tace sunan t n gaskia aunty Aishatu shine tace mu dinga kiranta d haka muna tare d itama a gidan Ammy munata Jin dad’in mu ….

NAWAL t gama zuwa wuya t kulu matuka d kalaman Yar Tata , itama duk t gusar Mata d farin cikin ta “mama nata karantar NAWAL itako Bata sani ba ”

 

NAWAL tace , to yaushe zakizo din ?

Noor tace sai dadyn mu yazo zamuce y kawo mu muda aunty Aishatu ….Jin yarinyar zata falasa ta d karyar d Tama mama ,yasa tayi gagawan cewa toh ki Bari ni zanzo kafin kuzo din kunji ,Noor tace toh ,sanan hassana t karbi waya suka gaisa d NAWAL ….

Bayan sun gama gaisawa ,NAWAL t kashe waya taba mama wayar ta tatafi daki Dan samun sasauci daga bacin ran d t dorama kanta yanzunan akan wata d batasan tanayi bama …

 

Tayi nisa cikin tunani , Mara mafita Dan Kan NAWAL y kule ko hanyar samun kofar mafitar matsalar ta batayi ……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button