KUSKURE Complete Hausa Novel

“”””””
Bayan kwana biyu zama yanata wakana tsakanin NAWAL d mama ,maman bin duk wani taku d salon NAWAL Dan shawo Kan gaskia Dan tayi komai d hujja….
Haka ma su twins sunata karatun su Noor ko sun gama exam Noor t dau first position Haneef ko n 3rd position y d’auka yanata murna Noor nata tsokanar s wai bayi kokari b baza a siyamai komai b ,Aiko y dinga rigima Yana kuka da kyar Ammy d Alh suka shawo kansa d Mai Alkawarori sanan yayi shiru …
Dadyn su ma d yazo sai d y babashi hakuri , y cika musu Alk’awarin d y musu y kaisu Shan ice_cream y musu siyaya d kaisu wajen wasa suda Janna kawai haka suka dawo gida d Kaya Niki Niki ..
Kowa sai d yaci har huzna uwar Shan kamshi d fi’ili …
Ranar d dadyn nasu y dawo dasu Noor t karbi wayar dadyn su nata gyame sanan t Kona wasan pix Tana daukan Haneef d Janna har su aunty twins har Indo t shigo cikin pix din har janna taba wayar wait d’auke su a aunty Aishatu su ,Haneef a gefen dama Noor a gefen hagu ,Indo batasan wayar waye ma d bazata Bari a d’auke t ba ,ganin yaran n cikin farin ciki yasa t biye musu Dan tayasu farin ciki ta tsaya aka musu pix din kusan guda 5 sunyi kyau sosai a hoton Tana sanye d wani Riga d skirt d hassana t Bata masu kyau daidai jikin t d’inkin y zauna Mata sosai ….
Sun Sha hotuna sosai har su aunty twins sai d Noor t d’auka t d’auke su d indon ma indon duk t fisu cinye hoton har huzna Tama 1 pix a badan halinta ba ,baza ace tayi kyau b baza ace batayi kyau ba hhhh , haka t gama cikama dadyn t waya d hotuna na zabe d na zubarwa ,sanan t mayar Mai …
Shiko ,Yana gidan Dan Taya yaran shi murna Dan ganin su cikin farin ciki ,ganin huzna ta Fara shishige Mai yasa y bar Mata sashin Ammy y koma inda yake zama y huta inyazo gidan …
Can ma t bishi ,ganin iskancin t y fara karuwa yasa shi barin gidan ko sallama bema su Noor ba ….
Washe tari Indo ta tmby Ammy zata gidan Inna t kwana biyu Dan Allah !
Ammy tace b komai taje ,Indo murna kamar tayi ihu , t shirya ‘yan kayanta ta zuba a wata jaka d ussaina t Bata , kodan t nisanci wulakanci d kalon raini irin n huzna taso barin giran n wani lokaci Dan zaman gidan Ammy yafiye Mata zaman gidan su Noor ….
D rigima d kuka d dabara Indo t rabu d su Noor d haneef hatta Janna t Saba d Indo yanzu itama Bataso tafiyar indon ba , d wayo d dabara d su Hassana d Ammy suka dingama su Noor sanan Indo t samu t bar gidan zuwa gidan inna….
“Washe gari SAFWAN bezo gidan Ammy ba d wuri y dawo daga office Yana gida …
Yana hutawar shi yanata Aiki a laptop din shi , yaji Ana nowking a k’ofan parlour y zata Bala driver ne Dan yace ma Mai gadi y kirashi inya shigo Dan y siyo Mai Abinci y zama gwauron Dole …
To y zata Bala driver ne y tafi y bude k’ofan Waze gani ?
*HUZNA* Ya k’ani cikin wata matsiyaciyar kwaliya komai a bayane aci makeup kamar wata Aljanar dare …..
Takaici d bacin Rai ko magana be iya Mata b y dawo y zauna a kujera y Cigaba d aikin shi..
Ganin y Bata hanya t zaci Yana maraba d ziyarar bazatan d t kawo Mai ne ,gashi Dadi y rufeta taci sa’a Yana gida dama tazo gaishe d NAWAL ne …
Ganin ko kalon inda take beyi ba , gashi bataga NAWAL b yasa tayi magana cikin wani salo ..
Yaya safwan Ina Aunty tawa?
Sai d ta maimaita sanan yace Bata Nan t fita yanzun Nan ….
Wani dadine y Kama ta ,gani daga ita sai shi zataci karanta Babu babaka …
Ta fara zame gyalen ta ,Tana wani Mika , shiko basan tanayi b attention dinsa Naga aikin shi …
Can tace Yaya nifa ita nazo gaisarwa ,yace toh ai sai ki bita gidan su taje kinsan gidan ai ?
Tace n sani Yaya Amman wlh yanzu bazan iya ganewa b Dan Allah ko zaka kaini Dan Ni ita nazo gaisarwa dama ..
Yace baki Kai b gaskia ,inada Abin yi ,Kuma m Ni aike zanyi yanzu zuwa siyo min Abinci ..
Huzna akace lass Yaya batama girki b ta fita ?
Ganin shishigin zaiyi yawa yace ,ninace taje ba matsala …
Aiko huzna t Mike tace toh Yaya barin taimaka ma , mekake son ci nadau nauyin girka ma komeye shi komin wuyan shi kuwa Wajen dafawa ..
Safwan y gama gajiya d gani d sauraran ta uwa uba b Abin d yafi bukata d y wuce t bar gidan yasa shi cewa ..
N hutar d ke kinsan b kowane Abinci nake ci ba ..
T yatsine fuska ,haba Yaya Naga har girkin kucakar yarinyar Nan ci kakeyi har d Kari !
Yace wace Kuma kucaka?
Kafin y ajiye maganar tace house girl dinan gidan Mana kazama ,kucaka wai har Tama girki kaci ..
Y d’ago Karo n farko d y kaleta har y Lura d irin tufar d tasa y hango rashin tarbiya karara atatare d ita ….yace indon CE kucaka? To ai tafi Mata d dama wacce Kika Raina Dan ta iya Abin d Mata d dama Basu ita b ta tatara abubuwa d dama d wasu matan Basu malaka ba ….
Maganganun sun taba ran huzna t Fara zuwa wuya , tace Amman dai Bata fini b ko Yaya S?
Y Wurgo Mata wani kalo yace kewa?
Tace Ni huzna jinin ka Mana Tana Mai wani shu’umin kallo.
Yace sake dubawa dai ,nidai n gama magana t Dara Mata d yawa Yar Aiki Mai share2 d goge gogen d wasu suke rainawa tunda suna ganin wayo ko dabara su ce yasa Allah yayisu a haka ita Kuma yayita a Karkashin su…..
Can huzna tace wai Yaya me kake nufi ne?
Yace duk Abin d tunanin ki y Baki shi nake nufi .
Tace nifan ba fahinci inda kasa gaba ba kodai kana cikin…….ta kasa karasawa Tana karyata kanta haba indon banza meze ci d wata Indo meye Abin kalo ko gani ko Aure a tare d ita d har safwan zai dinga ………Bata karasa b aka yi sallamar a k’ofa .
Safwan ne yace shigo ..
Dan Bala y shigo cikin salama yace Alh gani ….
Safwan y miko Mai 2k yace Dan Allah k min takeaway irin n ranar Nan ka kawo min yanzu ….
Huzna CE tace haba Yaya kabari aunty NAWAL din t dawo Mana sai t girka ma ko Ni yanzu n girls ma yafi fita siyo Abincin wajen ai …
Sai a lokacin Bala y Lura d huzna ,har y gaishe t Yana cewa toh Alhj asiyo ko a barshi ?
Huzna t mikama Bala hanu y Bata kudin ….
Safwan y zaro ma Bala driver Ido Yana cewa zakaje Aiken ko nazo naje d kaina?
Har zai mikama huzna kudin , ya zake cewa ita t aike ka koni,?
Bala yace Amin Afuwa yalabai barinje y fice y bar huzna n miko hannu kamar Almajira t sadaka ta lekoma ta koma…
Sanan y ajiye komai d yakeyi y nuna Mata gyalen t d t ajiye Kan kujera yace d’auki abunan naki ki koma gidan Ammy ko kibi wacce kikazo nema Yana nuna Mata hanyar waje ……
.ganin b wasa atare d shi Bata d Alamar cin nasara akansa yasa ta d’auki gyalen ,tace yanzu Yaya Ni Keke Kora a gidan ka ? Taimako y zama laifi?
Yace kiranki nayi ?inke Baki ilimin sanin cewa duk inda mace d n miji suka kebe to Akwai n 3 su “shaid’an” to Ni nasani Ina neman tsari d Allah n…
Huzna tace to sai me Yaya ai ‘yar uwar kace Ni sai Mai ,kome kamin ai jinin kace Ni ….
Ganin batasan me takeyi ba ,son ranta y dana neman danne donar Allah d annabin sa yasa y Mata fata fata y Mata umarnin gagawa d ta koma gidan Ammy ko Tabi NAWAL gidan su ….
D bacin Rai d takaicin Abin d y Mata tabar gidan tare d wani yanayi d yaketa Mata yawo a ilahirin jikin ta ….tare d cin Alwashin sai t cimma muradin t akan sa sai y shiga halin d ta shiga ayau d suka kebe daga shi sai ita, shi sai y shiga Wanda yafi nata ma d ta shiga gashi b biyan bukata …..
Bayan fitar t y dauko wayar sa Yana Dane Dane bemasan inda yake shiga b hannun shi y Kai gallery din wayar sa besan sanda y shiga b y shiga wajen hotuna ..