HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

 

Tozali d fuskar Indo a hotunan d Noor t dinga d’aukan su yasa safwan zabura y gyara zaman shi Yana karema hoton kallo y Cigaba d dubawa Indo Ce dai d y sani kamar a gaban shi har mutsika idon shi yayi ko gizo wayar take Mai yaga dai itace y Nuno inda aka d’auke t d Noor d haneef Tana tsakitar su y zaro ido ,idon shi kur akan Indo .,….

 

*Maman shaheed*????
[12/28, 7:09 PM] First Lady????: ???? *WRITING* ????

 

“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_Shafi Na Ashirin d tara_

Safwan dai mamaki y dingayi ,d tmby yaushe aka d’auki wanan hotunan a wayar shi ?

Can y tuno lokacin d Noor t karban Mai waya wai zatayi game anan wata t dinga Mai wasa d ways t dinga d’aukan Mai kowa a waya …..

Can Kuma y Cigaba d duba hotunan Yana cewa Ai gwanda adauki pix din indo d a daukan Mai pix din Huzna Mara tarbiya sakarya ..

Kaf sai d y gama duba hotunan Babu ita sanan yace ,d andauka d y goge ..

Zuciyar shi t tmby shi to Damme baze goge n indon ba ?

Sai yaba zuciyar shi amsa d kodan su Noor baze goge b Kuma wasu m ai tare suka d’auka ,

Y Nuno wani pix din indon ita kad’ai tayi kyau kamar asace ta a gudu ..

Y fara kare Mata kalo cikin wani siga ,Yana tunani d hasashen ko girma t karayi yaga kamar…….ganin zuciyar sa d kwakwalwar sa zasu Kai shi inda Bai je ba y sa yayi saurin dawowa y tsaida tunanin sa …

Yaga indai Bai ajiye wayar b baze bar ganin indon b ,Dan haka y ajiye wayar y shiga wani dogon nazari…..

***********

Indo t Isa gidan Inna lpy ,taba Inna sak’on Ammy ,Inna nata Mata Addu’a…

Bayan t huta taje gidan su nawara ta gaishe d momyn t bayan sun danyi Hira ta rakota gidan Inna sun Sha Hira , sosai..

Har nawara take cema indo waye Wanda y kawo su kwanaki?

Indo tace shine uban gidana Wanda nake Aiki a gidan shi dadyn su Noor…

Nawara tayi dariya tace, Kai Amman Akwai fahimta a tsakanin ki yaranshi ,Amman shima d fahimta tsakanin ki dashi ko?

Indo tace kamar y?

Nawara tace kamar yadda n tmby ki..

Indo tace ohon Miki ni ban fahimce ki ba ,keda hidaya in kunso gulmar ku bazaku fitoma mutum d Abu barobaro b zai kuta sashi a duhu …

Nawara tayi dariya tace,laa ban tmby ki kawar mu hidaya b?

Indo tace Yar gulma kamar ki ,Tana lpy tun shekaranjiya rabon d mu hadu ..

Nawara tace mune masu gulma ko ?

Indo tace eh Mana ,in ba gulma b kudinga min mgn d zan fahimce ku Mana ,Amman sai ku dinga kudindine Ni …

Nawara tace , hmmm shikenan barin kyaleki sai kamshin hasashena y fara yawaita d har yan gari kowa zai sani ,na Dora daga inda Kika dakatar Dani ….

Indo tace ke kikasan wanan karatun ,Ni ban gane ba ….

Suka bar wanan hiran ,nawara t faraba Indo lbr saurayinta d zata aura ,Tana Gaya Mata yadda yake nuna Mata so d k’auna Mai tsafta g kulawa d yake Bata …

Lokaci na farko a tarihin Rayuwar Indo d hasashen wani da namiji y bijiro cikin tsarin Rayuwar ta , Fara tunanin shin zatayi soyaya? To inzatayi d wama zatayi shin zata samu Wanda zai sota fiye d tunanin ta Kuma zai taimaka Mata wajen cikar burikan ta ?

Nawara nata ma Indo mgn ,Indo an Lula duniyar gano amsar tby ta..

Sai d nawara t datata sanan Indo t dawo hayyacin ta ..

Nawwara tace kawar meke faruwa ,meke damun ki d har y jefamin ke a tunani ?

Nawara tace plss karki boye min komai ,wlh wanan hirar d nake Miki bantaba yinta d kowa b ,yadda d ke d sanin ke wacece agurina yasa bake gaya Miki Abin farin ciki d y sameni ,d na bakin ciki ne ma d zan Gaya Miki wlh ,Amman inhar Kika Yi yinkurin boye min Abin d kike tunani wlh daga yau shaku d kokwanto zasu shiga tsakani na dake zasu Mana gatanga Mai kwarin d rugujeta sai ikon Allah.

Indo ta yi ajiyar zuciya ,Bata d hanyar gujema tmby nawara..

Dan haka ta sanar Mata d Abin d take tunani cikin zuciyar ta …

Nawara tace kawata karki damu ,na tabata Akwai Wanda suka taba Miki tayin soyaya kikaki Basu hadin Kai , Dan ba namijin d zai ganki beji kin kwanta Mai ba uwa uba Wanda ya sanki yasan d’abi’un ki d halayar ki d dadin zama d mu’amalar ki yaji beyi sha’awar ki zama Mata agare shi ba ..

Komai lokaci ne , nasan tsarin ki nakin kula samari ada ,ayanzu ki dinga kulasu ko b kowane Tom and Jerry ba , plz daga yau duk Wanda y Miki tayin soyaya t sigar d y Dace inhar kin tmby d nutsuwa hankalin shi ki fara julashi Dan Allah karki ki Amfani d mgn ta ..

Indo t nisa tace hmmm,naji Amman sai n tatara n dawo gidan inna Danni n gaji d aikin Nan ma..

Nawara tace kun rabune d su ,Indo tad’an saya tace aa matar gidan ce take aikin kwana a asibitin su shine muka koma gidan karkar su Noor maman dadyn su Noor din Kuma wlh Basu d matsala inajin dadin zaman gidan ko zasu rabu Dani sai ansha fama …

Nawara tace to ki Kara hakuri ki barsu zuwa wani lokaci , tace ki fara Aiki d maganar d n rokeki ko agidan Nan Akwai wani hasashe d nakeyi nake so y zama gaskiya kinji Dan Allah….

Indo tace a gidan mutanen? Zan bude musu kamfanin Hira d weni kato?

Nawara tace to meye? Su twins basa yi ne ?in kikayi korar ki zasuyi?

Indo tace aa sunayi ,Kuma banajin Akwai wani Abu d zai faru Sam Dan mutane ne masu karamci wlh ,kawai dai inajin tsoro d kunya idan dadyn su Noor yazo y ganni tsaye d wani !

Nawwara tayi dariya Mai isarta ,lokacin Indo har t Bata Rai tana Mata wani kalo ….

Nawara tace yi hakuri kawata ,wlh b azaki gane bane , Anzo wajen d nakeso n baza komata t cafko min duk Abin d y shiga Ni Kuma nayo waje dashi ….

Indo tace ohon Miki ke kikasan me kike nufi ,

Nawara tace ubangidan ki fa ba babanki bane , ko Akwai Yar tsama a tsakanin kune? Ko Yana nuna Miki tsana ko tsangwama ne ko zagi ko cin zarafi?

Indo tace ko daya be taba nunamin ba ,kawai dai girmamawa d mutuntawa shine atsakani na dashi bama doguwar magana ma dashi bashi d matsala Kuma Kinga yanzu ma yadan sake jiki Dani kadan fa Amman b kamar da ba ,kodan Ina tare d yaranshi Suma suna tare d Ni

,kinsan ance me da Wawa,inji nawwara Amman ahankali zamu Mai fatan sakowa gaba daya sai ma mun hadu d hidaya Naga ke sai ankawo Miki agajin gagawa….

Indo tace ,ku kuka sani keda itan ..

Nan dai nawara t baba Indo shawarwari masu tsabta d inganci d cire Mata shak’ar duk Wanda zeci zarafin ta ko y yagata a cikin jama’a…

Sunjima suna Hira kafin t koma gi …

Inna d Indo ma ranar ansha Hira sosai harda mafarkin d Indo ta tabayi d wani datijon d yaro y bige Saida taba Inna …

Inna t jinjina Abun itama taba Indo lbr nata mafarkin kusan irin shi itama d wanna datijon d duk suka kasa fasalta surarshi ko kamanin shi azahiri……

 

Nan suka dinga Al’ajabin Abun d mamaki d gano ma’anar mafarkin ,can Kuma Inna tace komadai maye Addu’a n maganin komai sai gobe muyi sadaka Akan mafarkin insha Allahu..

Haka sukayi kwanan farin ciki jika d Kaka …..

************
Su Noor ko baduji dadin rashin Indo ba ,Dan rigima suka dingayi wai akaisu wajen Indo ko amata waya ….

Twins nata Basu hakuri ,sai d kyar suka hakura d dabara ..,……

Huzna ko dama tun dawowar ta gidan t dawo d bacin Rai matsanaici su twins n Lura d ita Bata gaya musu ba Basu tmby ta ba , sai d t gama kumfar t ta sauka taje tayi baccin asarar ta sanan t dawo falon ,ko rigimar d su Haneef sukeyi akan Indo shi y Kara kular d ita take karajin tsanar Indo kamar sun had’a miji ga yarama wai sun iya kinibibi akanta ko wace ita agaresu oho ko kalon su batayi b bare t rarashe su .,.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button