HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

dadyn su Noor ne y Kira hassana yace Ina su Noor ko suna tare d indo sun kwanta?

Hassana tace aa wlh gasu Nan sunata rigima harda kuka wai akaisu wajen aunty Aishatu ..

Dadyn su yace to akaisu Mana , ko ba tare suke kwana ba?

Hassana tace tare suke kwana ,indon CE Bata Nan Tana good Dan Inna taje gaishe ta .,…

Yace ,haka kawai t tafi kodai wani Abu akayi? Hassana tace aa lpy Lau sai d ta tmby Ammy ma sanan t tafi ,taje nee kwana biyu …..

Dadyn su yace har kwana nawa zatayi ?

Hassana tace wlh ban sani b sadai munganta …..

Yayi shiru badan ranshi yaso hakan ba Jin ance yaranshi nata rigima in Akwai Abin d yakeso a yanzu be wuce farin cikin yaranshi ba ,rabon d yaga kukan su har y manta Amman yau harda kuka akan rashin Indo?

Jin kukan Haneef yace abashi Haneef din ….

Akaba Haneef waya ,dadyn shi y fara aikin rarashi Yana tby dalilin kukan ,yadda hassana t fad’a dai hakan y fada shima ,Nan y dinga rarashin shi d Mai wayo akan ze kirata gobe zata dawo sanan yayi shiru ..

Yace aba Noor itama murya cikin shagwaba ,y dinga rarashin t Yana Bata hak’uri har saida tamai Alk’awarin t daina kuka sanan y kashe wayar zuciyar sa cike d tunanin y zeyi d tafiyar Indo gidan Inna ,ya yaranshi sun shaku shi besan shakuwar tasu har takai haka b sai yau …

Huzna ko kuluwa t Kara yi duk Abun d akeyi Tana Jin naji Tana kalon na kalo ,cikin ranta t Fara tsanar yaran Tana cewa ai ko Auren safwan tayi sai tayi d gaske akan Taran inba haiaba tas zasu kashe Mata Auren d baban su Kuma d deal luv din su y fada ita d safwan wlh Indo sai tabar aiki agidan Dan zaman gidan sai y gagareta Tama Bata Dace d zama ko Mai wanke toilet din gidan ba bare har tayi girki d gyara komai n gidan har suci suna Santi har a bar Mata ragamar yaran gida uwa uba gashi yanzu t asirce kuruwar yaran har suna kuka Dan ta tafi gidan kasar d ta baro shegu kawai har ita ,tanata karatun jaridar jakuna ………..

 

*Maman shaheed*????
[12/28, 7:10 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

By
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar_)

 

_shafi Na talatin_

 

Ran Huzna iya baci y gama baci ,daga baya ma tabar musu parlour t koma d’aki ….

Safwan ma ranar kwana yayi Yana tufka d warwara akan shakuwar yaran shi d Indo ,y sake tir d Hali d dabi’u irin na NAWAL d ta jefa yaranta t data Basu kulawar d Indo take basu d be Sami matsala kamar haka ba d ta amsa sunan ta na uwa agare su ,Amman yanzu gashi ta raba Mai gida ,inda yaran shi suke samu kulawa daban ,wacce ta haife su daban ,wanan wacce iriyar rayuwace d NAWAL t jefasu gaba daya?

Kwana yayi Yana tunani ,da Jin zafin Abin d NAWAL tayi ga Yabo d yake ma Indo cikin zuciyar shi n kula d yaran shi d takeyi uwa uba Basu tarbiyar d ko uwarsu iyakacin abinda zata musu kenan..

Yana cikin tunanin ,y tariyo maganganun NAWAL d takecewa y maye gurbinta d Indo ,atake kirjin shi y bada wani gajeren sauti , y rintse Ido tsabar Jin zafin maganar ….

Ya tabatar d lalai NAWAL t boyemai abubuwa a iya sanin d y Mata ko Kuma ta mugun canzawa daga NAWAL din d y sani zuwa wata daban ,y tuno d kalaman d suke sanyayama junan Rai akoda yaushe in suna cikin nishad’i tun kafin Auren su har Auren su ….

Sukance ma junan su ,daya baze iya rayuwa ba indai ba daya ,Dole bazasu iya ba sai suna tare d juna ,to gashi t karyata abin d take gayamai da kanta Dan ita t Fara bilo d hakan …

Y Jima Yana mamaki d tunani akan Rayuwar su t farin ciki zuwa yanzu d komai y canza y Karo tuno zafafan kalaman d t dinga duban idon shi Tana Gaya Mai ,y Kara tabatar d cewa lallai NAWAL ta gama rainashi ,ga babban raini d take hadashi d Indo yarinyar d kyakyawan motsi Bata iyayi in Yana wajen tsakanin ta dashi girmamawa d ganin mutincin juna shine zata dinga hada shi d ita Dan t rainashi?

 

Wani sashin zuciyar sa y tmby shi ,kafi karfinta ko ? Ka wuce sanin ta ?….

Yayi saurin gujema tunanin wani sashin zuciyar tasa d cewa bance dai Amman hadin ai Bai hadu bama ,Ina sai d yayi da gaske sanan yayi watsi d tayin Indo d zuciyar sa take kawo Mai …..

 

***********

NAWAL ta cigaba d gudanar d komai nata ,mu’amalar ta dasu Laila d doccas sai Abin d y cigaba ,suna sha’anin su son ransu sun yadda d junan su sosai g d’aukan shawarar junan su kamar wahayi ko hadisi ,hakan zaman nasu yaketa wakana …

Indo nagabatar d Rayuwar ta cikin kwanciyar hankali d jin Dadi gata ga Inna ta g kawar ta nawara ..

Yaune hidaya t kawo Mata ziyara ,suka hadu d nawara sunata ma Indo tsiya akan saurayi d Bata shawarwari ta d’auki n d’auka tayi watsi d Wanda taji wayewa ta shigo ,suna Mata hakane Dan t goge d yanayin zamani d y canja itako gani take zasu kaita inda Allah Bai kaita ba ,gwanda nawara ma ,Amman hidaya itama ai kamar indon take masu rangwamen gata masu neman n rufama Kai Asiri Dan mamanta t rasu sai mahaifin ta d take taimaka musu ita d ita Kuma shima b karfi ne dashi ba ,Dan haka Indo take sata a sahun su Dan kusan jirgi daya ne y d’ebo su ..

Sun Sha Hira gab d hidaya zata tafi t dagama Indo hankali d rigimar d su Noor suketayi tun tahowar ta gidan Inna har yau Basu Dena ba Abu kusan sati guda ,Amman Basu hakura d ita ba …

Aiko duk Indo ta canja taji ba Dadi ,Kuma dama tanajin yaran aranta hakuri takeyi kawai sbd b Wanda zatama hirar ,haka dai suka raka hidaya ta hau napep suka dawo nawara tayi gida akabar Indo cikin tunanin halin t suke ciki ita d su Haneef …

Itama ta Jima Tana tunani akan shakuwar su d su Noor gashi b Abun d suka had’a ,rasa gano amsar tunani d shakuwar su d su Noor yasa t karbi aikin Inna t k’arasa t gyara ko Ina ……

 

Koda dare tayi haka Abin yake ga su Noor kwana sukayi suna rigima ,sai da Alhj su twins yata mafan rarashi Yana Al’ajabin shakuwar yaran d Mai Aikin ,Ammy ma mamakin hakan take ,Amman duba d sanin halayen Indo kyawawa managarta (halinka jarin ka) yasa bataga laifin yaran ba Dan ita kanta tasan yadda Indo take kula d yaran tasan uwar su ma Bata kula dasu haka g inganta musu tarbiya d takeyi Dan haka take sake son tarayar Indo d jikokin nasa …..

 

Washegari d wuri dadyn su Noor y Zo Dan ganin yaran shi y ga halin d suke ciki akan rashin Indo a tare d su ….

Koda y Zo suka dinga murna d Mai magiyar y kaisu wajen Indo ,y dinga musu wayo d rarashi y samu ze gudu ,Ammy t kirashi tace y d’aure ko in y dawo ne y kaisu gidan Inna su gaisa d Indo ko zasu barsu suyi bacci yau …

Y jinjina Abun sosai kafin yace ,Ammy ai d su Hassana sun kaisu …..

Ammy tace hassana d hussaina basa Nan anjima sunada bikin Kuma jiya akayi kamu basuje ba yau za’ayi wini d dinner shine zasu Kar dai ace baduje ba ……

Ganin y tsaya tunani ,yasa Ammy magana tace Mai to saidai idan kwatantama huzna gidan zakayi sai t kaisu ….

Jin an sako huzna yayi saurin ,kawar d zancen yace aa zai dawo d yamma y kaisu kawai ,Ammy tace ko kaifa ,Allah y dawo dakai lpy .,.

Yace Amin. ,y tashi ze fita ,Noor tace Dady zaka kaimu wajen aunty Aishatu?

Yace eh inya dawo daga ok office ba ,Yana musu murmushin sa Mai kayatarwa ,Aiko Haneef yasa murna Yana cewa yeeeee ….

Safwan d Ammy ma tsayawa sukayi suna kalon yaran suna Kara Al’ajabin kaunar d take gudana a tsakanin su d indo sun tabata inda Tana cutar dasu d bazasu k’aunace t haka ba ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button