HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Dadyn su Noor y momyn su Noor take ?

Yayi wani ajiyar zuciya Mai Alamar tmby ,daga bisani yace Tana lpy …

Take a gaisheta ,dama inason zuwa d’ebo kayana ne ina tunanin Kar n Kara haifar muku d matsala ,duk d an samu Rashin fahimta irin n momyn su Noor Dan wlh a tsarin rayuwata banason n haifar ma kowane Dan uwana musulmi matsala komai kankantar ta ,wlh itace Tama Abin mumunan fahimta Dan Allah ka Bata hak’uri dadyn su Noor yayan su aunty twins da ga Ammy datijuwar Arziki …..

Besan lokacin d y d’ago Yana ma Indo wani duba ba n yabo d tabatar d cewa kirarin Nan daga bakin t yake fita d gaske?

Bayan y tabatar y yaba d kirarin yaji Dadi kuma matuka ,y ji dama tanada gurbi ko n ‘yan uwantaka a zuciyar sa d y fara sheering damuwar sa da ita ko yasamu sasauci daga radadin d zuciyar sa Kan Masa lokaci zuwa lokaci ,Dan d y samu sasauci..

Amman kash be ga halin hakan b ,Dan in y bayana Mata damuwar sa a matsayin ta n wa agare shi ?

“Kawai cemata yayi karki damu Baki d laifi a Al’amarin wani Abun base angaya Miki ba a lamarin NAWAL Dan kinji kin gani d dama ,kawai ita wata iri CE Kuma b haka take b ta aro wasu halayen wasu Kuma dama nata ne t Adana su sai d lokacin bukatar su t taso Mata t d’auko t Dora ma kanta d Rayuwar ta Dan ayanzu ma Tana gida sanadin kin bin umarni na d munanan kausasan kalamai d take Amfani dashi take Gaya min ,duk yadda naso ganar d ita Taki fahimta d n fuskanci kanta hayaki yake kawai n seta ta zuwa gida Dan bazan zauna d macen d Bata bi umarni na ba ba’a haifeta ba gaskia …..

Maganganun shi sun saka Indo kuka tun farkon Fara mgnr shiko be sani ba suko su Noor suna bayan mota sunata game d wayar dadyn su d Haneef y karbo musu ,safwan d Indo kuwa suna waje bakin motar …

Indo kuka take sosai ,safwan Jin shashekar kuka y d’ago Dan ganin inda yake fita hawaye ne wani n bin wani a idon Indo …

Mamakine y cika shi ,Yana tmby ita Indo wace irice haka Mai tausayin Wanda baya tausayin ta? Indai haka take halinta Abin koyi ne ,Dan haka yake farin ciki d alakar yaran shi d ita Dan ayanzu yanajin ko a gidan su Indo yaran shi zasu iya Rayuwar cikin tarbiya d samun kulawa d tsafta Dan basu makusa ta ko Ina sai na rashin wadata ,rashin wadata kuwa ai ba rashin zuciya ko tarbiya bane ,Allah Ne y zaba musu Rayuwar tasu a haka ba’asan tanadin d y musu Nan gaba ba ko ranar gobe kiyama ba Allah shine Mai yin yadda yaso a lokacin d yaso ……

Tausayi ,yabon Hali irin n Indo y dinga shiga zuciya d ilahirin jikin safwan ,Yama rasa ,hakuri zai Bata ko rarashin t zeyi ?

Inna duk b na dauka ,Dan b kowa bace a gare shi face ‘yar uwa a musulunci wadda Aiki d taimako y had’a shi d ita sai yanzu d yake Mata irin son d yaranshi suke Mata n mutuncin t ……

Cewa yayi zamu tafi ki gaishe d Inna ,zansa hassana t d’ebo Miki wasu daga kayan ki t kawo Miki ,be jira amsawar ta b y shiga mota y Mata key ya juya y seta hanyar fita daga layin su Indo y harba Dan tafiya gidan su Ammy……

 

Indo a wajen y barta tanata mamaki d tunanin Hali ko dabanci irin na NAWAL ….

Ganin bame cemata t koma gida in zata kwana a wajen yasa ta koma gida d hawaye far idon ta …

Duk d dare ne Amman Akwai wutar lantarki Dan haka Inna t gano hawayen d ke kwance a fuskar jikar tata ….

Gaban Inna ne y Fadi ,t janyo Indo t Fara tmby waya rasu?

Indo jijiga Mata Kai kawai tayi ba magana.

Inna sai d t Fara Mata magana fada2 sanan ta samu bakin bama inba lbr komai d Bata fadama Inna ba dacan baya n samun sabani d sukayi bayan komawar ta d’aga gidan Inna har komawar ta gidan Ammy har zuwa yanzu d ta dawo gidan Inna …

Inn salati d hailala ta dingayi Tana mamaki d Jin dacin Al’amarin Dan duk mutumin kwarai Yana bacin Rai inyaji lbr wani Abu d yasa sunnar ma’aiki tayi rawa t fuskar saki ko Kora ko wani hatsaniya d y gifta cikin Auren ma’aurata ,mussaman masu so d k’aunan junan su irin su safwan d NAWAL…..

Inna cewa tayi zata gidan su NAWAL din danyima NAWAL fada d bama iyayenta hakuri ….

Indoce tayi saurin takatar d ita ta hanyar sanar Mata d duk wasu dabi’u d halayar NAWAL d indon t boyema Inna d Bata tab’a fada Mata ba sai yau d tayi dalili …

Inna tayi mamakin zurfin ciki d hakuri irin n Indo d ta gada a wajen mahaifan ta da baban t d maman ta badaga Nan b wajen hakuri d jurema wuyar rayuwa kafin su shud’e a doron duniya …

Ranar dai d Jin zafin sabanin d y shiga tsakanin NAWAL d safwan Inna d Indo zasu kwana …

Bayan sun iso kofar gidan su Ammy ya umarci su Noor su fito y shigar dasu Dan y wuce gida y huta …

Sai a lokacin Haneef yake tmby dadyn shi Ina Indo?

Murmushi yayi kawai Yana mamakin son waya irin na yaran zamani d kamar d son waya ake haifar su ……

Noor m t Kama su a maidasu gidan Inna ,ganin zasu Mai tijara ya taba dama zai Sha fama wajen rabuwar su d Indo wayar sace t taimakesa y samu y taho dasu batare d sun Ankara ba …

Nan dai yata rarashi d wayo d dabara y samu y kaisu wajen Ammy ,y Mata salama y tafi gida …

Koda safwan yayi sallah isha’i y saka Abinci a gaba Yana ci ….

Tunanin Indo ne y Fado Mai .,..

Ba komai yake tinawa b sai kukan d taci Akan NAWAL ,y Kara jinjinama tausayin ta d cika cikakiyar mutun wacce duniya zata iya Alfahari d ita .,…..

Yanata tunano irin kyama d wahalarwan d NAWAL take yima Indo Kuma y tabata indon m tasan d haka ,Amman take dorama kanta lefin d Bata d ko digon haki aciki ta Kuma sani Amman ta dage Tana Mai zargin d sa hanun ta aciki ,inba mutumiyar kirki ba wace zatayi haka?

 

Abun haushi d ya barota tanata kuka ko rarashin ta beyi ba y barta a tsaye a wajen ,sai yaji be kyauta ba Sam …..

Yana Kai lomar Abinci Yana kaicon NAWAL ,d tasan irin yadda Indo t dauketa ita d yaranta d irin zaman tsakani d Allah d takeyi dasu d tun farko itama Bata zauna d ita d niyar d tayi rayuwa d ita ba n matsayin Mai Aiki wulakantaciya Mai nema a Karkashin t t dinga Mata Abin d be dace ba d har yanzu t dau tsanar duniya t Dora Mata Akann Abun d basa hanun ta aciki …..

Kwana yayi Yana mafarkin kyawawan halayan Indo …..

***********
Washe gari su Haneef d gyada d ayar Inna y karya su Hassana d Ammy sunata tsokanar sa …..

Kowa yaci ayar Rai d kwadayi Amman Banda huzna bakin ciki zai karta Noor t dinga Mata gwalo Tana cemata Dadi y barta ……..

Huzna t sake kuluwa suko sun d’auki Abin duk cikin wasane Dan haka Basu Hana Noor ba….

 

********
Bayan sani daya komai Yana tafiya yadda yake..

NAWAL d mama anata takun saka maman bin duk wani motsin NAWAL Dan gano gaskia Dan tayi komai d hujja ,itako sahoramar Bata sani ba …

Tanata mamakin yada safwan baya Kiran NAWAL a waya kamar yadda y saba gashi itama har yau safwan be kirata y gaishe ta ba d Dane kuwa d tuni y gasheta t waya kusan so nawa…

 

Ammy ma jikin t y fara Bata Dan NAWAL Bata tab’a zuwa gidan b tun d aka kawo su Noor ,sai so daya d hassana t Gaya Mata NAWAL d mama sun kirata sun gaisa d su Haneef tun daya shi Basu Kara Kira ko zuwa ba har yau….

Bayan kwana 5 ,Ammy t yanke shawarar tmby safwan Anya lpy kodai aikin ne y Hana NAWAL leko su ai ko a waya ta kirata Dan tagaisheta ai….

Itama mama t tirke NAWAL Kan t cema safwan y kirata tanason magana dashi …..

Nan idon NAWAL y Raina fata t Fara kame kame da kyar t samo mafita t ninke mama baibai d cewa to Mana abari sai gobe ,Ramin karya kurare ne mama tace Allah ya kaimu d Rai d lpy , NAWAL ko Amin Bata Samu damar cewa ba .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button