HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

 

Ammy ma ganin safwan y kwana biyu be Zo b gudun rigimar su Noor Dan shi sukema rigima wai sai y kaisu wajen Aunty Aishatu yasa y Dan Dena zuwa akai akai …..

Koda Ammy t kirashi tace Tana son ganin shi zasuyi mgn akan NAWAL y shiga tashin hankali yasan shikenan Abin d y saya ze budu Dan haka ya amsa d zaizo indai Aiki yamai sauki ,ammy tace Allah y kawo shi lpy ,y amsa d Amin ..

Ranar safwan d NAWAL kwanan tunani d Abin d zeje yazo suka kwana Dan an birkita kwanyar su sun shiga Rudi d gudun Abin d sukaki sanar ma kowa duniya zata sani yanzu ,kowa na ganin lefin Dan uwansa ,ita Tana ganin shi y jefata a cikin halin d take ciki shima Yana ganin taurin Kai d juyama so d kaunar d yake Mata baya y jefashi a cikin halin.

 

*Maman shaheed*????

???? *WRITING*????

 

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi n talatin d biyu_

 

 

Safwan y kasa zuwa gidan Ammy har aka kwana aka hantse..

NAWAL ma t ki idar d sak’on mama ,Yar sai d mama tace wai baki fada Mai sakona bane NAWAL shi dadyn su Noor din?

“NAWAL tace laa mama n sha’afa Kuma munyi waya dashi f Amman ze kirani anjima zan Gaya Mai ,Koda bana gidan Nan Dan yau zanje gidan kawata lailai daga can zan wuce Aiki ..

Mama tace karkiga Dan mijin ki y barki ki dawo gida kafin y dawo ki dinga tafia sakaka kamar tinkiya fa ,kin Gaya Mai Zaki gidan natane ko aikin Nan d kike zuwa fa kulin sai kin sanar Mai in Zaki fita banason shashanci irin naki fa NAWAL ..

NAWAL d Fara dibibicewa Alamar asirinta gab yake d tonuwa tace ,eh mama Ina Gaya Masa ,Kuma y San d zanje gidan shi y ce najema y amince d bazan Miki mgn ba..

Mama tace to ai shikenan ,Amman dai karki sake ki sake cemin kin manta d sak’on d nace ki Gaya Mai .

“NAWAL tace zan Gaya Mai mama bazan manta ba ..

Mama tace to Allah yasa ki manta ai inada number shi nadai fi so y kiranin ne ….

NAWAL jikin t y Kara sanyi , t tashi taje t shirya Bata tsaya ko Ina b sai gidan Laila kawar su ita da doccas Dan jiya bataje Aiki b Bata d lpy kunsan Mai yaron ciki..

“Safwan bashi d zabin d y wuce zuwa gagawa g Kiran Ammy Dan baya Saba umarnin ta NAWAL ko wani Abu d y shiga tsakanin su baze say fara Saba umarnin ta ba Dan haka yayi shahada ya je bayan y dawo daga Aiki…

Koda y shiga su Noor sunata tsale d murna dama Basu Jima d dawowa daga gidan su Indo ba suda hassana sunje kaimata kayanta d suka d’ebo Mata a gidan su Noor dawowan su kenan..

Aiko suka dinga b dadyn su lbr ,ga wani farincinki da anushiwa d y hango a tatare d yaran nasa Yana sake jinjina k’auna dake tsakanin su d Indo ..

Ammy dai hakuri tayi d mgn d takeson Masa sbd su Noor d huzna d suka ki Basu dama ,ita huzna t kafa t tsare Taki barin wajen ,su Kuma sunata bashi lbr sun hanashi sauraron Kiran Ammy ga haushi dama duk y cikashi agane d kalon e huzna take Mai …..

Saida Akayi sallah magriba Ammy d safwan suka Sami damar ganawa a parlour Alhajin su ..

Safwan duk yadda yaso dojewa ko gyara Al’amarin tsakanin shi d NAWAL ,Inna mafi a’ala y fada Mata gaskia kawai ba boye2 tsakanin sa d mahaifiyar shi Mai share hawayen shi Dan haka y Gaya Mata komai tun farkon faruwar lamarin har umarni d taje gida d y Mata har maganganun d t gagabza Mai d tazo diban kayan ta ..

Ammy t jinjina Al’amarin matuka ,t yi mamakin yadda NAWAL din t canja takuma yi mamakin d iyayen NAWAL din Basu taba zuwa Dan Jin ba’asin maganar b amatsayin su n Wanda sukafi NAWAL tunani da hankali ,tunda su basuje ba aisu kamata yayi suji dalilin komawar yarinyar su gida ko t waya …

Kusan minti 10 b Wanda yace komai sa daga baya Ammy tace yaje y ci Abinci kafin Alhaji y shigo ,bazasuce komai b sai Abin da sukaji daga gidan su NAWAL din ..

Safwan ji yayi kamar y sauke wani dutse Mai nauyi akan sa ,Amman zuciyar sa namai daci sosai …

 

Bayan safwan yaci abinci ,Alhajin su y dawo Ammy t labarta Mai komai kamar yadda SAFWAN y sanar Mata…

Shima Al’amarin bemai dadin sauraro ba ,dake datijon arzikine yace gobe zeje gidan su NAWAL din da kanshi Dan bambance daidai d rashin daidai ….

NAWAL sunsha Hira d Laila Mai Amfani d Mara amfani batabar gidan b sai d taci Abincin dare ,dama kayanta Yana Jakarta n Aiki daga can asibiti ta wuce suka hadu d doccas suka Dora daga inda t tsaya …

 

Washe gari Koda NAWAL t koma gida tun d ta shiga dakinta Bata Bari sun had’u d mama ba ,mama n Lura d manufar t Dan haka t fita hanyar t tunda tasan tare zasu wuni a gidan…

Bayan Abbah su NAWAL y gama shiryawa Yana Shirin fita …..

Alhajin su safwan y kirashi a waya yace Yana gidane?

D mamaki yace eh Yana gida !

Alhajin su safwan yace gashi a kofar gidan.

Abbah su NAWAL ya fita y shigo dashi yamai iso a parlour shi ….

Bayan mama tazo sun gaisa jikinta y gama Bata Akwai matsala sanan t tafi d’akin NAWAL..

Koda NAWAL taji zuwan Alhajin su safwan tuni t rikice tasan yau kashinta y bushe …

Mama ma t gama hango tashin hankali a tare d NAWAL din t umarce ta d taje t gaishe shi …

Hali d taurin Rai d rashin nadama ,Yana tatare d NAWAL t shiya fito n fito d kowaye Akan safwan Dan atunanin ta shi y kasa jure rashin ta ya Aiko bikon ta ita Kuma wlh sai ta gasa Mai gyada a hanun ta ko zata koma Kuma sai ma tayi shawara in zata koman tasani baze taba iyawa ba idan ba ita a Rayuwar sa Kuma Tana Nan Akan ra’ayin ta iya Rai d mutuwa Aiki tundaga Nigeria har outside in hakan y Sami iya Tama sadai y ajiye nashi ra’ayin …..

Da wanan tunanin t Isa parlour t tsuguna t gashe d Alhajin su safwan bayan y amsa t fito t koma d’akin ta Tana Jin kanta Yana wani Kara girma ita g wacce akazo Biko.

Bayan sun gaisa , Alhaji su safwan ya ce dama maganace akan yara muna zaune bamusan meke faruwa b sai jiya d mahaifiyar shi take tmby shi ,sbd kyakyawar fahimta d Kuma basa boye Mata duk matsalolin su Dan kafin su tinkareni d matsala su sun sanar Mata wani Abun sai a wajen ta zanji kamar yadda wanan ma daga gare ta naji..

Abbah NAWAL yace fito min amutum Dan n fahimce ka ban fahimta b har yanzu ..

Alhaji su safwan yace to ,ita Yar taku bakusan dalilin zuwanta gida ba Amman kuka barta t ke zaune a matsayin ki wadanda kuka fita tunani d hangen nesa bayan kunsan tun aurenta Bata tab’a zuwan muku gida harda kwana ba sai a wanan lokacin Kuma baku tumtube mu ba har sai d tayi wari yanzu mukaji muka biyo danjin duka bangarori biyun?

Abbah y fara hasala d maganganun Alhaji …..

Yace nifa idan n fahimce ka kana nufin matsalace t gifta tsakanin NAWAL d safwan?

Alhaji yace kwarai kuwa Kar kace min baka d lbr Mana?

Abbah yace gaskia bamu d lbr nasan dai kwanaki tazo har muke hirar aikin t Akann safwan din bayason tayi Aiki nake cewa hakan b daidai bane Dan ai duk rufin Asirin sune d yaransu ,Amman Bata ce mana matsala suka samu b tadawo gida …

Kafin Alhaji y yi magana ,Abbah y kwalama mama Kira su taho d NAWAL…

Nan mama t Kira NAWAL suka zauna , Alhaji su safwan y fara Basu lbr kamar yadda dansu y sanar musu wato safwan ..

Aiko ,ba mama ba d hasashen ta y zama gaskia ,har Abbah NAWAL din beji dad’in boyewar d yarsa tamai ba ,..

Y Kuma sanar ma da Alhajin su safwan cewa t rufesu cewa tayi yayi tafiya ….

Aiko mama t Fara yima NAWAL fada sosai Kan Bata kyauta ba ganin mama zata wuce gona d iri yasa Abban NAWAL dakatar d ita……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button