HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

 

NAWAL CE dinga rarashin mama har t samu t saki ranta ,NAWAL nason mama kusan soyayyar uwa d ‘yarta ,kawai taki ba mama hadinkai ne su dinga shawarta duk matsalar su subiyu ba tare d Abban ta yaji ba ,mama t samu matsala nee NAWAL tun Tana karama ta hanyar so d sangarta d Abba y dinga nunama NAWAL tun Tana karama har girman t har NAWAL take ganin shawara ko neman mafita a wajen Abban ta ta duk matsalar d taxo Mai dashi tafi samun gamsashiyar amsa tunda zebarta taci karenta Babu babaka sabanin mama d seta tsage gaskia t Kuma nuna Mata karya a bayane t Kuma Bata umarnin bin gaskia hakan yasa take ganin kamar Abba y fi son farincikin ta a shirme irin na NAWAL fa …….

 

**********

Indo an gama had’a Mata kekenta har t Fara Aiki d shi a gidan Aunty Tana fahimtar yadda ake koya Mata komai ,kafarta t Fara sabawa d takun keken sosai …

 

Bayan t koma gida taje gidan su nawara Dan sanar d ita t Fara zuwa koyon dinki jaka d takalmin ….

Bayan sunsha Hira nawara nata tayata murna d nuna Mata t dage t koya yadda y kamata…

Har nawara take cema indo wai tayi mafarkin ankusa bikin Indo Amman batasan waye mijin ba biki Kuma ganga ganga cikin kankanin lokaci akayiomai aka gama tanata murna …

Indo t gama sauraron nawara t turo baki tace ke wlh bakya rabo d shirmenki ke wani lokacin kamar Yar gulma kamar Yar baiwa Kuma na rasa wane zan ajiye ki ?

Da dai wanan shirmen naki ze faru sai n barki a ‘yar baiwa ,Amman Ina! d kamar wuya gurguwa d Auren nesa wlh ko kusa ko Alama Ni saurayin d kikace n Fara kulawa m n canja shawara Sena gama koyon dinki na ,Aure cikin kankanin lokaci sekace Yar tsakuwa ko wata Irin hamshakiyar mace wacce Auren dama kawai take jira tab !

Nawara tayi dariya tace ,Allah y tabatar Miki Dani Yar baiwar ce ,

Indo tace b Amin b wlh kedai d bikin ki y saura wata 5 Allah y nuna Mana musha shagalin..

Nawara tace wlh wata kilama kiga kinrigani Auren ,Abun Allah Kuma shi yake tsara komai a tsare …

Indo tace ,Allah baze amsa ba ,bakinki dai Allah y shirye shi …

Ni Kinga tafiyata d surutun ki Mara tushe bare makama ..

Sukayi sallama t tafi ..

“SAFWAN yayi bacci sosai ya tashi yayi sallah ,Ammy Tana sawa azo a duba shi har zuwa tashin shi yanzu ,ranar Yaya ma ko fita beyi ba ,tare sukaci Abinci d k’anin nashi ,ba wani sosai SAFWAN yaci ba koshi, y ma su Noor salama Yana cewa Ammy y tafi ….

Ammy Ce Tama Yaya maga d y karbi makulin motan safwan din y driving Dinshi har gida kafin y barshi …

Safwan kalon su kawai yayi y saki wani murmushi gano Ammy Tana zargin ko ba a hayacin shi yake ba …

Bayan Yaya y Kai safwan gida safwan y dinga tuna Mai d afa neman Mai Auren Indo su d’auki maganar sa mahimmanci kafin faruwar wani Abu …

Yaya y dinga jujuya maganar faruwar wani Abu Kuma ,wane Abu kenan?

Y tmby kanin nasa Amman yaki cewa komai ,shi kwnshi baya iya controlling kanin nashi y zamar Mai maiwuyar shi’ani yau …

Seda yaya y tabatar safwan y sausautawa ranshi daga damuwa sanan y bar gidan ,Koda ze fita seda safwan y sake Mai mgn afa neman Mai Auren kafin faruwar wani Abu ….

Yaya fita yayi Yana cemai baridai zamu tatauna ….

Koda Yaya y koma y sanar m d Ammy furucin safwan ,itama t dinga tmby akan meyake nufi d faruwar wani Abu ,

Yaya y nuna mata indai b matsala ama safwan yadda yakeso na tsorata d bacin ran d y shiga yau dinan Dan n rasa gane kansa ,

Ammy tace kaje gida gobe in kunzo sekuji shawarar d muka yanke d Alhajin ku …

Yaya y Mata sallama y tafi gida …

 

*Maman shaheed*????
[1/6, 8:15 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi n talatin d biyar_

“Safwan kwana yayi Yana tufka d warwara akan Al’amarin burinshi y zeyi y Aure Indo duk d ba digon sonta a cikin ranshi ,Kuma yanada dama iya sakin t d’aga baya ta samu Wanda takeso ta aura daya baya shi Kuma y sake auran wata matan d yayi yanaso fiye d son d Yama NAWAL…

Da wanan tunanin y kwana ..

Bayan Alhj su safwan y dawo gida ,Ammy taje sukayi magana t fahimta dashi akan safwan ….

Alhj yace a rabu dashi ,shirme yake wane irin zama zeyi d ita d betaba cewa Yana sonta ba ko so yake y yi Auren huce takaici d y’arinyar mutane ?

Kudubafa d kyau ,duk Wanda y goyi baya akayi abinan in ya cutar d Yar mutane t rashin Bata kulawar d namiji zeba mace yasani Yana da kamisho na Alhaki….

Ammy tace ,toh Alhj mude nemi zabin Allah ,wai baka Lura d tashin hankali d matsanaicin bacin ran d y shiga bane ,karfa wankin hula ya kaimu dare ,muduba matsar sa da Abun da yake bukata matuk’ar beci karo da addini ba Alhj..

Alhj y numfasa yace abari zasuyi mgn d safwan din …..

*******

Indo ta dage tanata koyon d’inkin ta hankalin ta kwance …

Inna nata samata Albarka d nuna Mata d rage tayikokari ….

Indo na gidan koyan dinki wani yaro y shigo gidan Ammy lnna wai Ana Kiran lndo a waje ….

Inna tace waye? Yaron yace shima besanshi ba ,da har zata Aika a Kira indon sai t tuna wani Abu tace aje ace Bata Nan ….

Saurayin badan ranshi yaso ba y bar kofar gidan su Indon,

Bayan Indo tadawo cin Abinci Inna take Gaya Mata ,indo t turo baki …

Inna t dinga Mata nasiha Akan ba wakanci tsakanin ta dlwane namiji ,rabuwa lpy shi yafi komai sauki ,duk taji tayi naam d gargad’in Inna t Mata Alk’awarin kiyayewa Kuma …

Adaren ranar inna tayi mafarkin kwatankwacin irin na nawara wai Anzo neman Auren Indo Anzo neman ma wani Wanda tsabar son d yakema indon har yakai shi g kwanciya a Asibiti Rai a hannun Allah ,akazo Ana magiya d rokon Inna d Indo su Amince Kar saurayin y mutu ,Indo kuwa juyin duniya Taki Amincewa ganin Taki yadda yasa Inna ma Bata amince ba kardai rashin Amincewar yasa saurayin rasa ransa iyayen sa suka shiga mumunan tashin hankali d kuka dangin saurayin suka dora Alhakin hakan Akan Indo da Inna ,ba indo ba har Inna sai d sukaji da sun San ze mutu d sun amince d bukatar su ,sunata kuka Suma …

Koda Inna t farka cikin kid’ima ta farka Tana tariyo Abin d y faru a mafarkin tanata addu’a…..

Koda t tashi d safe Abun Yana ranta t umarci Indo t siyo Mata kosai tayima yara kanana sadaka ..

Ta zaunar d Indo takebata lbr mafarkin d tayi ,Saida jikin indon yayi sanyi taji kamar gaske ,gani zata shiga damuwa Inna t sanar mata mafarki ai ba gaskia bane d kwantar da hankalin ta Addu’a d sadaka suna kawar d abubuwa da dama ,indon tace to Inna ALLAH ya amsa ,Inna tace Ammin ……

 

“Bayan safwan y tashi d safe y shirya a dadafe Dan ji yake jikin shi wani iri ,y tafi office ganin jiya beje ba …

Koda yaje gani daya zakamai ka gano damuwa a tare dashi ….

Amman in abokanen aikin shi sun tmby shi sai yace musu lpy ,gashi y kasa aikakomai ….

Can zuwa wani lokaci zazzab’i y Fara Shirin rufe shi ….

 

NAWAL dai t rarashe mama ,mama t cire komai aranta gudun Kar hawan jinin t y tashi ayanzu ma tanajin ta wani iri so take tace NAWAL tamata bp haushin d suka kunsa Mata yasa take ganin gwanda t tafi asibiti Likita y dubata sosai ….

Dan haka t shirya t Kira Abban NAWAL tace zataje dubiya asibi yace Mata adawo lpy Tama NAWAL sallama zataje dubiya asibi ..

Duk yadda NAWAL taso su tafi tare mama Taki , haka Dole NAWAL t hakura ,mama tayi tafiyarta likitanta t dubata tsaf y Bata magani y umarceta d ta rage damuwar d ke cunkushe a ranta tamai Alk’awarin insha Allah zatayi iya kokarin ta ,y Bata sati biyu t dawo asake gwada ta ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button