KUSKURE Complete Hausa Novel

Kafin yaron ya tafi ,Inna tace y leka gidan Aunty Mai dinki y Kira Mata Indo yace su Noor sunzo…
Koda yaron y tafi ,Yana fada d sauri cikin azama t taho ….
Tana shigowa tayi arba d ussaina kafin t k’arasa wajen ta su Noor sun taho a sukwane sun cacimeta ,itama rungumesu tayi irin ta missing dinsu dinan ,ji tayi kamar Kar su rabu …
Sai d suka Dan saketa ta samu t zauna kusa d ussaina Tana gaishe t cikin sakin fuska d faran faran ,bayan Inna t mikoma ussaina pure water suka Dan taba Hira ganin sauri take taje ta duba yayanta safwan ….
Ga shi ussaina ta rasa yadda zatacema su Indo zatabar su Noor anan…..
Can dabara t Fado Mata in tace za tafi tasan maybe su Noor suyi rigima ta barsu Dan haka tayi shahadar cewa zasu tafi …
Aiko su Noor sukace su abarsu ,Haneef harda buya a bayan Inna da yaga ussaina t Mike Tana gyara gyalen ta …
Ganin Noor ma t koma t cacime Indo Tana ita abarta anan Dan ALLAH aunty Ussaina…
Ganin rigimar su d Shirin kuka d sukeyi ,Inna tace in Babu damuwa Yan biyu t barsu ko zuwa anjimane Indo t mayar dasu Dan Allah..
Ussaina Anzo wajen d takeso ,tace to Inna na dawo n daukesu anjima ,su Noor sukayi dariya ..
Ussaina t ma su Indo sallama ,suka rakata iya kofar gida ta tafi zuwa asibiti…
Koda ussaina t Isa angama sama safwan ruwa kafin a mayar Mai dashi aka kaishi laboratory Dan Mai gwaji ,Bayan tmbyy d Likita ya Mai y bashi amsa cikin k’osawa ,harda zuciyar sa d take yawan fad’uwa d bugawa ..
Bayan nazari d ganin gwajin d Dr Yama safwan aka sanar ma da alhj d Yaya cewa ..
Safwan nafama d damuwa a zuciyar sa jinin sa gab yake d hawa koma ace y hau duk d ba irin hawan d za’ace y kamu d hawan jini bane Amman dai Akwai yiwuwar kamuwa d hawan jinin matuk’ar ba’a kiyaye ba …
Likita y Basu magani d Sha’awar wari y Kara samai wani ruwan…
Alhj d Yaya sun tausayama safwan ,ganin Ammy t damu d son Jin condition din d yaron t yake jiki aka kirata gefe ake sanar Mata akayi sa’a ussaina taji ,Aiko t gayama hassana, huzna da safwan ne kawai basu San me Dr y fada ma su Alhj ba …
Ammy salati t dingayi ganin zata sama kanta damuwa d yawa Alhj y kwantar Mata d hankali da cewa bafa cewa akayi y kamu b Yana iya kamuwa in ba’a kiyaye ba ,yanzu farin cikin sa kawai zamu Nemo duk Abin d zai sashi farin ciki d kwanciyar hankali ashirye nake d yi Mai ko meye matuk’ar be sab’a shari’a ba …
Bayan safwan y farka ,hassana d ussaina d huzna d sufaya har tazo ta kawo abinci suna tamai sannu ,Kai kawai yake daga musu ,suka koma daga waje ..
Alhj d Yaya d Ammy suna tare d safwan ,Ammy ce ta umarci Yaya d y d’aga mata safwan y samu yaci Abincin d suffaya t kawo tunda duk Abincin d aka kawo Mai daga gida yaki ci ,ga gwaten dankalin turawa Mai alayahu na manja ko zai iya Sha …
Koda aka d’ago shi d kyar yake iya bude Ido Dan azabar bacci d yaci karfin shi ,Yana Loma daya yayi n biyu d na uku yace shifa y k’oshi …
Ammy nata lalabashi akan yaci ,alhj Yaya ma lalabashi suke y Kara cokali 5 da kyar ,Alhj yace su barshi haka tunda yace y k’oshi ..
Cikin magagin bacci ,safwan yace Alhj y mgn Auren d nace ku nemar min?
Ba Alhj ba kowa na Wajen Yama rasa bakin magana ,Ammy d Alhj tunani suka Fara kardai ace sanadin rashin lpyr sa kenan d har hawan jini yake barazanar neman kamashi ?
Shiko Yaya yasan hakan baida nasaba d Rashi Amincewa maganar sa d sukayi …
Safwan y sake cewa Alhj bakace komai ba fa ,da gaske nake ku nemomin aurenta a yau dinan kafin Mai faruwa t faru Dan komai na iya faruwa inhar …..
Kafin y karasa Ammy ta shafa kansa tace yi hakuri safwan ba komai zamu maka yadda kake so ,Amman k Bari k Kara samun sauki tukunna kaji?
Safwan yace ai samun sauki na naji magana Mai kyau ,Alhj yaje nema min Auren “Kuma Anbashi to daga wanan lokacin n warke daga cuta ta …
Duk tausayin dansu y Kama su ,Ahj y dinga kwantar Mai d hankali d Ammy har Yaya ma ,kanin nasa y fara bashi tausayi …
Sun yanke shawarar zasu Fara tuntubar Inna d maganar ko hankalin safwan y kwanta …
Safwan bawai Dadi yaji b d Alhj y amsa zeje ,kawai dai ya amince ze kunsama NAWAL takaici Amman ko kadan baya farin ciki d Auren ….
*********
NAWAL ban Gaya Miki ba ?
NAWAL tace mefa! Kawata?
Yau naje asibiti Naga kanwar mijinki d muka taba had’uwa ,nake tmby waye b lpy kinsan me tace?
“NAWAL tace sai kin fada min ”
Hmmm gogan naki fa yanacan Rai a hannun ALLAH ,waya cemai Ana rabuwa damu a kwana lpy , duk Dan d y Hana uwarsa baci to shima ai baze rintsa ba wlh Yana asibiti Rai kwakwai mutu kwakwai ..
NAWAL Saida wani mugun faduwar gaba y ziyarce ta ,da akwance take dai d ta mik’e Dan sauraren news akan safwa “Amman atake t d’aura Aure d taurin Kai d bakinb ra’ayinta na baza t gusar d rauni d tausayin d suka bijiro Mata a zuciyar ta ba “saima taji dadin lbrn kawar tata ..
Tace hmmm ahab baze iyaba sai d Ni nasani ,Ni Kuma wlh Ina Nan na tanadan Mai rashin buhubuhun Rashin MUTUNCI kala kala ,tunda har y raba igiyar d take tsakani na dashi ko idona Dana Abbana be gani ba uwa uba yaranmu ,wlh sai na karta Mai rezar wulakanci a tarihin Rayuwar mu dashi ,sai yasan yayi d Yar halak …
Gobe zanje asibitin ma n Kara rikitashi da somin tabin RM din da zan aikata Mai, dan y kwana d sanin sai y Sha artabu kafin n nakoma gidan shi …
Suka kashe wayar suna shewa ….
Yamma tayi ,sai a lokacin Ammy ta umarci ussaina taje d taho d su Noor, hassana d Ammy d huzna d suffaya duk Alhj yace su koma gida shima gashinan zuwa ,abar Yaya a wajen shi y kwana dashi …
Washe gari d safe , kafin kowa yazo NAWAL t Zo asibiti batare d t fadama mama gaskia inda zata ba …
Koda tazo t dingama Yaya d safwan kalon wulakanci ….
Yayane y dakatar d ita ,d cewa ke renon uba ,girman uba ,sangartar uba ,ki kama kanki karya gudu y barki me kikazo yi renon uba girman tsakar gida tunda kin nuna uwar d t haifeki Bata Isa dake b kindauki gurbin ta kin karama datijon birin ki …
Aiko NAWAL tace Kar ka sake ko kusa ko Alama Yaya kake ko yayo ? Kar k zagan min Mai sharemin kukana!
Yaya yace Aiko watarana shi zesaki kukan kunci,kukanda ko takadar tsire baze iya Baki ki share hawayen d ita ba bare ki samu Arzikin tissue ,ko farin cikin d ze share miki…
Aiko t Fara surfa musu rashin Arziki shida safwan din da ko kalon t beyi ba, atunanin ta son tane y kawo shi ga kwanciyar asibiti shine Bari t Fara Rama wilakancin d y musu kafin yazo Biko ….
Ammy t shigo d’akin ,Amman masifa d fitsarar nawal Bai Bari taga Ammy b t cigaba d rashin kunya ,Ammy Tana Kara mamaki d halin NAWAL d y bayana a fili yanzu ..
Safwan ko ji yake kamar y tashi y wanketa d Mari y had’a Mata d Jini d majina koya huce ..
Yaya ko tsayawa ga dokar ALLAH ne shima da tuni y mazgeta ..
Koda Ammy taga alamar fitsarar nawal din gaba tayi ba baya ba ,tace NAWAL kin kyauta d wanan dubiya Taki Mai cike da tashin hankali d karama Mara lpy ciwo ,amman ki sani ciwo yasan gidan kowa ,zoki fice Allah y shiryeki y ganar dake …
NAWAL batasan Ammy t shigo b amman ganin ta h
Gama Jin komai ,kawai taga to meye? Kawai gwanda ayita t kare kafin t dawo cikin su ko d’ansu y mutu d son ta aranshi a gadon asibiti …
NAWAL har t juya zata fita safwan yayi magana karon farko tun shigowar nawal..
“`Yace Ina gayatar ki Shahararen d’aurin Auren“` *AISHATU (INDO) DA ANGONTA SAFWAN* “`Rana ita yau dafatan in Baki samu zuwa ba Zaki rakamu d bakin ciki d Dana sani da nadama Mara amfani“`