HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Ba NAWAL ba kowa na wajen ya sarama safwan yaji dadin tura Mata takaicin d tazo t kunsamai aciki,yanzu baida ragowar bacin ranta a tare dashi tunda ya Rama …

Itako tsayuwa tayi n dakiku kadan ,Bata tab’a tunani ko mafarkin zai iya firta hakan ba ,Amman Kuma gani a aikace shine yi ba furtawa ba ..

Dan haka tace ,aikin banza d wofi ..

Na gani akas ,fada ba cikawa ai aikin banza ne ….

Safwan yace Ammy Indo nakeso d aure cikin satin Nan ,kinji Ammy ta uwa Mai maganin kukan d’anta ?

Ammy t gano NAWAL takeso a kunsama takaici tace..

Dana safwan baka taba nema daga gareni ko Abban ka ka rasa ba ,Auren ka d Indo kamar an shafa Fatiha ne , ALLAH ya nuna Mana har y baku zuriya tagari…

NAWAL ji tayi kamar andoka Mata guduma a zuciyar ta ..

Shiko safwan besan sanda y taso daga gado ba yazo y rungume Ammy Yana Mata godiya ,shi kanshi Yaya sun birge shi …

NAWAL ko t rasa abinyi ,sai d tazo kusa d Ammy tace ..

Fada b cikawa aikin kawai ne ,inyar ke Kika haifi safwan Ku aiwatar d Abin d Kika furta a matsayin ki na datijuwar kirki ,inko sati y wuce baku aiwatar ba kinzama tatijuwar banz….

Bata karasa ba Yaya y taso zai mareta Dan y gama fusata ,Aiko Ammy ce rike hanun sa d y sauke a kumatun NAWAL…

Ammy ce tace Zaki Sha farin mamaki , kidai tanadi tsiman tare hawaye d maboyar bakincikin Dan insha Allah ,Nanda sati b fashi sadai ikon Allah!

 

NAWAL a fusace t fita daga d’akin ,har sun kusa Karo d Alh d hassana ,t wuce su fuuuuu!

Ganin t a hargitse yasa Basu cemata ufan ba …

Sai d suka shigo hassana take tmby meya kawo aunty NAWAL Aiko Ammy ganin Ahj su yake saurare t Gaya musu duk irin fitsarar d NAWAL din tayi ….

Hassana ta ciji yatsa taso Tana wajen Amman taci Alwashin sanar ma ussainar ta sai sun tsula Mata up Suma …

Alhj dai hakuri y Basu ,Akan karsu kulata su Mata uziri renon mahaifin tane ,y sanar musu yau zeje gidan Inna neman ma safwan Auren Indo …

Safwan shiru yayi maimakon suga Yana murna , har Abin yaso Basu mamaki ,Amman ganin ko bashi d lpy ne ko bacin ran d NAWAL t kunsa Maine Bai gama sakeshi ba yasa suka rabu dashi sukayi Alk’awarin Sama Mai farin ciki kawai da bama NAWAL kunya tunda t Raina mutane..

“Rai a bace NAWAL t Isa gida , ranar kowa rasa gane kanta yayi har Abban nata ,itako mama ganin tanata kunci Taki Gaya Mata damuwar ta tafita harkar ta …

*Wash…………..*????????‍♀????????‍♀

*Maman shaheed*????

???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE*????????‍♀_????????
( ‘Yar Aiki Ko Matar Gida)

 

_shafi N talatin d bakwai_

 

Haka zuciyar NAWAL ta karaci Radadi d Jin zafin kalaman safwan d Yaya har Ammy ,Dan seda t Kara Dora aniyar rashin sasauta musu ko t dawo gidan safwan….

 

Safwan dai Yana asibiti yana samun kulawan Likita d Ammy yayin d Abba y d’auki hassana Dan rakiya zuwa gidan Inna domin fad’in bukatar safwan..

Indo nata koyan d’inkin t yau har Aunty Mai d’inki ta dauketa sun shiga kasuwa Dan siyo kayan jakankuna d sold din takalmi Dan Indo d gaske take haik’an ,sunata siyayan su Ana nuna Mata duk inda ake siyar d kayan d’inkin jakar d su fata …..

Hassana Ce ta shiga gidan Inna bakinta d’auke da sallama ,

Cikin fara’a da nuna kulawa Inna t amsa ta karbeta har take cewa kinko Taki sa’a indon Bata Nan ..

Hassana tace ayya ,ba komai ..

Inna t Fara tmby su Noor suna lpy da baban su ?

Hassana ta Dan canja fuska ,Alamar Akwai damuwa !

Inna tace lpy dai suke Yan biyu kinyi shiru?

Cikin yanayi damuwa ,hassana tace wlh Yaya safwan (dadyn su Noor) shine ba lpy Yana asibiti Rai a hannun Allah ,y fara samun sauki muna murna NAWAL tazo jiya t kare Mai tanadi kinsan y sawake Mata auren sa ,har Ammy d dangin mu Saida t zaga tacima mutunci bakiga Abin da tamai ba a gadon asibiti lnba, gashi ance me y kamu d hawan jini a dalilinta gashi yanzu Yana bukatar kulawar mace a kusa dashi ,har Addu’a tamai wai in Allah y yarda beze sake samun macen Aure ba ,sai hawaye suka Fara Shirin fitowa daga ldon hassana (ohh Ni faty hassana harda Karin gishiri d Maggi a bayanai)..

Inna ko tun lokacin d hassana t Fara biya Mata ,taketa rafka salati d hailala d jajanta Al’amarin Tana sake gaskata maganar d Indo ta Gaya Mata akan matsalolin NAWAL uwar d’akin ta …

Inna ma duk jikinta yayi sanyi ,har Tana cewa Alfarmar annabi da Al_Qur’ani Addu’a ta beze kamashi ba seya hadu d wacce ta fita Alkhairi insha Allahu haka dama ‘yarnan take?…

Jin kalaman Inna ,hankalin hassana y Dan kwanta ,Dan batasan y Ahj ze doshi Inna d maganar Auren Indo d safwan ba ,Kar duniya taga ma kamar ba’ama Indo adalci ba ko Dan angansu talakawa shine za’azo Ayi Auren huce takaici d ita ko Dan su ba wasu bane za’azo neman aurenta ace Kuma cikin sati daya agama komai har d’aurin Auren ,Alhalin b haka bane su sunfi so y auri Indo ma sunsan Bata d matsala Kuma y taimaka Mata y taimaki kansa Dan su Babu bambanci tsakanin su da talakawa a adalci irin Wanda suka taso aka dasa musu a zuciyar su Dan haka b rashin gata ko talauci ko wulakanci zesa a nemi Auren Indo cikin sati bane (wanan duk tinanin hassana ne)…

Can hassana tace laaa Inna tare muke d Alhajin mu fa ,Akwai magana d zakuyi Mai matuk’ar mahimmanci d kima Dan rok’o mukazo Inna Dan girman ALLAH Inna Kar ki bijirema rokon mu Dan ALLAH ki yarda ki amince awajen ki muke nema! Addu’a ki da Amincewar ki muke nema kawai Inna ….

Inna tayi saurin dakatar d hassana ,yo Yar Nan Ni wacce tsiyar gareni d har zakuzo nema ? Inna n zaro ido..

Itadai hassana magiya tayi Tama Inna Tana d’aureta d jijiyoyin jikinta ,

Inna ma jikinta y fara sanyi ,a ganin ta komai suka nema zata iya musu ,sudin na daban ne acikin shahararun masu kudi ……

Inna tace t d’auko tabarma d sabuwar salaya d makocin su ya dawo daga saudiya y kawo Mata tsaraba t shimfidama Alhajin nasu …..

Aka shinfid’a Mai , Inna t umarce ta d ta Mai iso ,zuciyar t cike d tunanin me suke nema a gareta ko Kan komawar Indo ne gidan su?

Indai shine tun yanzu t amince ma ,har yazo d kanshi ai sunfi karfin komai a wajen su …..

Koda Alhajin y shigo ,Inna ta Mai sannu d zuwa cikin mutunta juna d girmama juna suka gaisa y fara tmby lpy ta d lpy kowa n gidan duk d yasan Indo Ce kawai a gaban ta ….

Bayan sun gaisa shi kansa sai y nemi y rasa ta inda zai Fara ..

Inna ce t Fara d cewa, auw na manta y me jiki Ashe ubangidan Indo ba lpy har Abin y kaishi ga kwanciya a Asibiti ?

Nan Alhaji y Dan samu kwarin gwiwa magana har y gano inda zai isar d rokon shi g Inna …

Ya Fara d cewa ,eh wlh Yana can Yana fama wlh kusan matsala sa cema t kawo Ni nazo rokon Alfarma d taimakon gagawa a wajen ki Dan soyayyar d kikema Allah d ma’aikin sa ….

Inna tace ,Allah yasa dai lpy Alhj meya kawo maganar Alfarma muda ba komai ne damu b ba wani mukaba ajiya ba bare mu karbo …

Alhaji yace ,kugodema ALLAH ,tunda har munga Abin roko d agareku duk d mudin bamu dauki kamu wasu daban acikin Al’umma ba face duk daya muke ganin kanmu …

Inna tace tabas itama shedace akansu ,t yaba Hali irin na ahalin gidan sa Wanda duk tarbiyar sace Dan shi y koyar dasu hakan har suka Saba suke aiwatarwa har yazaman musu jiki ,uwa uba rashin kyamatar marashi ..

Alhaji yace ,Inna Kafin n Fara isar d kokon barar mu karkiyi tunanin rashin galihu ko ganin kaskanci d Raina Arzikin ku ko Raina galihun Abun da nazo nemane yasa nazo neman Abin d nazo nema a gare ki ,wlh ko kusa ko Alama face samun masalaha d ganin mutunci d karamci yasa zanyi hakan ,a inda nake ganin nafi karfin hakan,duk d bukatar hakance t taso cikin gagawa…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button