HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Washe gari aka salami safwan duk yadda yaso abarshi y koma gidan shi Ammy d Alhj d Yaya kinyarda sukayi su huzna ma ansami bakin magana harda ita a bada shawarar Kar abari y koma gidan shi kadai ,tunda matar shi tayi tafiya kamar yadda ya fada Mata a asibiti gwanda a barshi a gidan Ammy t d’auki nauyin duk wata dawainiyar shi alhj da Ammy suka danyi murna a matsayin ta n Yar uwarshi ,shiko kamar y nausheta yakeji …..

Hakadai bashida zabi y amince da shawarar su Ammy yaya d shi sukaje suka d’ebo wasu abubuwan da zai bukata ……

Dake huzna duk maganar da akeyi na Auren Indo ba’a tabayi agaban ta ba Dan haka Bata da lbr komai .

Dan haka safwan y koma part din d suke hutawa shida Yaya in sunzo gidan ….

Huzna anata kwarkwasa d feleke ita Mai jinya ,Bayan iya t Gama girki huzna t d’auki foodflacks d plate t tafi kaima safwan Abinci Koda t shiga Yana bacci akan 3seater ,Bayan ta gama kare Mai kalo cikin so d bege sanan ta ajiye kayan ta tafi d’auko ruwa d drink….

Bayan ta dawo ta ajiye t cigaba d kalon shi ,Bayan tayi Mai isarta ta tashi ,ta matsa kusa d kanshi Tana Dan bubuga kujerar Tana ambatan sunan shi …

Ganin Ana ta tayar Mai d kura y farka a hankali ,sukayi Ido 4 da huzna Aiko y sake bude Ido cikin tsana d takaicin ganin ta har Tana tashin shi daga bacci ….

Koda y farka sai ya juya kwanciyar shi Aiko tacigaba d magiya d kwarkwasa Tana kashe Mai murya Tana Mai magana akan y tashi yaci Abinci ..

Ganin inbai tashi ba bazata barshi ba Dan haka yace ta tafi zai tashi yaci ..

Ta makale murya ta fara Mai magiya ,jarabar nacin ta yasa y tashi t zubamai tanata binshi d kalo shiko tura Abincin kawai yake …

Can t fara Mai mgn Tana tmby shi sai yaushe NAWAL din zata dawo garin?

Nan y Sami amsar Bata a dakile , sai next week zata dawo ,Aiko hakan Yama huzna daidai zata isar da soyayyar ta cikin kwanciyar hankali zuwa zuciyar safwan yayin d b matarsa a tare d shi ba kazamar hadimiyar sa indo….

 

Gobene komawar Alhaji su safwan gidan Inna Dan haka Alhj da Yaya suka tsaida magana Akan Ammy CE zata Fara zuwa wajen Inna sbd Sudan zanta atunanin Sa zasufi fahimtar juna fiye d shi Dan Mata ne su gaba dayan su tunda b namiji a tsakanin su ….

 

Bayan Indo d Inna sun wayi gari da suka tashi suka gama ayukan su ,Indo ranar ko gidan Mai d’inki bataje ba sai tunani d takeyi..

lnna na kula da yanayin ta ko Abincin kirki t kasa ci ,lnna Ce ta kirata ta Kara Mata nasiha d Kuma karta dau Abin d zafi ta sasauta sunemi zabin ALLAH ..

Indo ta amsa ,jin duniyar ta Dan Mata dumi t shirya tace ma lnna zata gidan su nawara tajita shiru kwana biyu ,lnna ta gano manufarta Tana neman Wanda zata gayama matsalar tace Don shawara ko mafita ,sanin Hali d mutunci irin na iyayen nawara d nawaran kanta yasa Bata hanata ba tace tagaisheta da maman nawaran ma ….

Bayan lndo t shiga tayi salama ta Sami kanwar maman su nawara tazo gidan wata bazawara d Auren ta y mutu zainab ta gashe ta tagaishe da Abban nawara d maman nawara duk suna falo suna Hira akan mutuwar Auren aunty zainab din ..

Bayan lndo ta gaishe su ,suka amsa cikin sakin fuska d fara’a dake sum Saba ,ta tmby su nawara na Nan?

Kafin su Bata amsa nawara t fito d sauri ,mama tace to gatanan ma ta jiyoki ,Abban su Yana musu dariya Yana cewa kawa da k’awa,suka shige d’akin nawara suna murmushi ….

Bayan sun shiga nawara ta kawo ma lndo ruwa d juice d cincin ….

Indo ko kalon Abin d aka kawo Mata batayi ba ,nawara nata janta d hiran barkwancin ta Amman ko kulata takiyi Abin y fara ba nawara mamaki ..

Indo lpy ki kuwa? Meke damunki ?

Indo tace komai da komai nawara tsakani na dake zumunci ne ko nace ‘yan uwantaka Wanda ALLAH y had’a ,wlh lna cikin damuwa d rashin mafita Ina tsaka Mai wuya sai kuka y kwace Mata ,nawara ta rikice …

Da kyar nawara ta shawo kanta d rarashi ta tmby ta matsala ta ,cikin kuka lndo ta gayama nawara komai …

Nawara mamaki tayi da murna ,da ganin mafarkin ta Yana Shirin zama gaskiya?

 

Ganin Babu digon damuwa a tare d nawara lndo t Fara Jin haushi har Tana cemata dama yanzu Basu Kai matsayin d zasu raba damuwar su ba ,su magance tare ba?

Nawara t bama lndo hakuri ,ta Fara Mata magana cikin hikima d nutsuwa d bayani na tsakani d ALLAH ,har t tuna Mata d mafarkin da tayi ta taba fada Mata ta maida maganar wasa…

Aiko lndo ta tuno itama harda mafarkin d lnna tayi t gayama nawara lrin Wanda lnna tayi ,nawara Abin nema y samu ta Soma nunama lndo cewa insha Allahu Alkhairi ne ze biyo baya Dan ALLAH lndo karta bijire d rokon da sukazo dashi !

Ita dai lndo kuka kawai takeyi Tana tunano abubuwa da dama d balalai dubanin mutane su tayata ganowa ba…

Aunty zainab Ce Shirin shigo wa d’akin taji wasu daga cikin hiran su lndo d nawara ta koma ta sanar ma mama agaban Abba nawara ….

Aiko mama ta taso Jin ance lndo na kuka shima Abba y tausaya Mata duk d besan dalilin kukan ba ,har yake cema mama taje taji in Akwai bukatar gagawa d lndo take nema matuk’ar n kudine ko Wanda ze iya magancewa a tuntube shi domin bada gudumawar sa shima ,itama t talafi maraicin Yar karta barta tacigaba d zubar d hawaye kamar yadda bazata bar nawara ‘yarsu tsiyayar d hawaye a banza ba matuk’ar da Akwai halin taimakon ta” mama ta amsa da toh,d sauri mama d aunty zainab suka shiga d’akin ko salama Babu ….

Nawara nata rarashin lndo Tana Bata hak’uri d tausasan kalamai ..

Mamace t tmby lpy?

Nawara Tama lndo magana Kan cewa tayi hakuri sugayama mama komai ,mama duk daya suke a wajen ta aunty zainab ma kanwar Abba ce Kuma duk Abu dayane su …..

Indo Kai kawai ta daga Mata batare d tace komai ba …..

Nan nawara ta gayama mama d aunty zainab komai har Abun d ake ciki yanzu …..

Mama t jinjina girman maganar ,tajanyo lndo jikin ta ,ta tmby ta Abin da Abin da take tsoro cikin Auren ?

Indo t nuna Mata matsala ta NAWAL d Kuma atunanin ta ba sonta yake ba zai toshe wata kafa ne d Auren ta bawai Dan yanason ta ba ..

Mama ta jinjina maganar ta ce subar magana yanzu , anjima zata gidan lnna ,sanan Abba ma Dole y shigo cikin maganar lndo dake d nawara duk daya muka d’auke ku ,Abin d zamu Miki ko nawara iya Abun d zamu Mata kenan ….

Mama t tafi sanar ma da Abba komai ….

Aunty zainab t dinga rarashin lndo har ta dinga shigar Mata d lbr aurenta d yanayin ribar da hakuri d juriya yakeda shi d Kuma rungumar kaddara , har t Basu lbr rabuwar Auren ta ,dai lndo taji Ashe ita bama acikin damuwa take ba kawai gatane y Mata yawa ta samu miji na kere sa’a kamar safwan harda yaran sa yaran da tafiso a duniya yara renon ta masu Nutsuwa d birgewa gwanin Sha’awa g karamci d datakon da danginsa suke nuna Mata a rayuwa kodan wanan ta amince ko zaman kula d su Noor ne taje tayi duk d tasan b Auren so zasuyi b ,Bata son shi baya son ta …..

Can Kuma tace kai Aure cikin sati kamar Yar tsana ,gaskia bazata amince ba …

lndo nata tunani ,aunty zainab nata Bata Baki d hakuri d rarashi d yadda d Auren safwan duk d Bata ga alamun matsala cikin Auren ba sai Alkhairi d hasashen su yake Basu ….

Bayan mama ta gama b Abba lbr y tausayama lndo yayi Alk’awarin shiga maganar d wucewa gaba ,da cin Alwashin matuk’ar Raina kima ko Arzikin su ne yasa akazo neman aurenta cikin sati batare d jiran yardar yarinya ko tanaso ko Bata so ba shi ze wuce Mata gaba wajen karbo Mata ‘yancin ta d karfin shi d Aljihun shi inko ya ji d sulhu ko mutunci suke son Abun shima zesan yadda ze biloma Abin …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button