KUSKURE Complete Hausa Novel

Yaya ma y Kara jadada godiya Kan Aure d akaba kanin shi ,y musu fatan zaman lpy d rayuwa Mai dorewa …
Bayan su Alhj sun tafi ,suka dinga yaba karamci irin na Abban nawara d haka ake shigema marayu gaba d wasu marayun Basu yi kukan maraici ba …
Shima Abban nawara gidan Inna y shiga y samu ,lnna y Mata bayani n fahimta y Bata hak’uri akan hukuncin d y yanke batare d ya ji ra’ayinta ba ,y nuna Mata badan rashin kimarta ko cancanta yasa yayi haka ba ,yayine Dan hango Alkhairin Abin d mutane da dama suke hangowa …
Y tmby Inna ko yaron yanada wani aibu d be cancanci a bashi Auren b a sanin ta ? Ko be fito gidan mutunci ba?
Inna tace wlh Bata d shaku akan tarbiya,mutunci ,halayen gidan iyayen sa ko wata matsala dashi ,yarone managarci …
Abban nawara y nisa yace shima be yi saurin yanke hukuncin ba seda ya tsananta bincike akanshi d iyayen shi ..
Abin d yasa be tsaya jin t bakin Aishatu ba kuwa ,Dan yasan Bata d hujar kin auren sa be wuce irin shirmen su n Mata ba ,kotace Tana tsoron tsohuwar matar Sa ko tace ita bazata auri ubangidan taba Wanda Addini be Hana hakan ba , kotace Akwai abinda yake nufi d Auren nata ,duk naji wadanan ne g Aminiyar ta nawara ,wanan kuma duk b huja bace Mai karbuwa , Addu’a itace Mai matuk’ar mahimmanci acikin wanan Al’amarin …
Yace Inna ko kinada wani abunda Zaki fadamin?
Inna tace, ai ba komai duk kun gama komai ,abinda zance be wuce biyu zuwa uku ba..
Na farko lokacin d aka dibanma bikin yayi kadan sosai ..
Na biyu y kamata a bamu lokaci Dan samun yadda zanyi namata kayan daki daga Abinda ALLAH y hore Mana nida ita ..
Na uku rikemin amanarta ,Dan Amana nabasu wlh duk Wanda y cutar d BAIWAR ALLAH Nan ALLAH zesaka Mata Dan marainiyace Ni kadai n rage Mata sai ku dasu da kuka shigo Rayuwar ta .
Sune abinda zance sai fatan zaman lpy , ALLAH yasa hakan shine mafi Alkhairi atare damu dasu Baki daya ,zan babata hakuri Kuma zan tataushi zuciyarta in ALLAH y yarda ..
Abban nawara yaji dadin bayanin Inna ..
Yace maganarki t farko ,Nima Ina jinjina Abin Dan yanzu a yadda sukeso Nanda kwana biyar kenan ,Amman indan sunki yadda d yadda mukeso a daga ko a Kara lokaci zamu iya d’aura Auren Amman baza’a kaita ba sbd inaso tayi farincikin d Auren d zamu Mata ,tunda bikin nawara saura wata 2 sai a hadasu amusu biki daidai d d’aurin Auren nawaran nasan hakan zesata farinciki intaga itama kawar tata gidan mijin ta zata tafi Kinga sai akaisu gidan mijin Rana daya ,anawa shawarar fa kenan …
Zanji daga garesu su ,gidan mijin nata zuwa anjima yadda ake ciki zakijini ..
Maganar ki ta biyu Kuma ,sun d’auki nauyin yimata komai Wanda uba yakema ‘yarsa ,Dan Dani naso yi wlh,amnan y hadani da ALLAH Akan karnace zanyi jayaya dashi Dan haka n sake Mai ..
Maganar ki ta uku Kuma , na jadada musu wanan maganar dagani harsu munsan Aishatu Amanace agare mu y zama wajibi mu kiyaye maraicin ta ,duk mun yadda wanan Baki d matsala insha ALLAH “in Akwai Abin da kike son cewa ko bukata k’ofa abude take Ina d lokacin sauraron ki ko ba yau ba ..
Inna tace b komai ,ta gode kulawa d shiga Al’amarin su ta yaba d halin datako , ALLAH ya Albarkaci zuriyar sa …
Yace Amin y tashi y koma gida …
Yasa ,ya sanar ma da mama yadda sukayi d Alhj su SAFWAN har yadda sukayi d Inna ..
Indo d nawara sunzo fita sukaga Abba ,Indo t tsuguna t gaishe shi ,Bayan y amsa t Mike zasu tafi ,ya kirata y Fara Mata nasiha Mai ratsa jiki nasigar d ko mahaifinta iyakar wacce ze Mata kenan …
Nanda Nan zuciyar Indo ta karye ..
Dake gaskiya yake Gaya Mata ,Kuma namiji NE ,y Cigaba d magana y sanar d ita yadda sukayi d Alhj su SAFWAN y nuna Mata y amince y Bata hak’uri y nuna Mata itama yarsace kamar nawara karta yi yunkurin banbanta kanta d nawara ..
Har y Gaya Mata shawara d y yanke Kan aurenta y yarda a d’aura ko Bata tare yanzu ba ,sai Ayi bikin tariyar ta d bikin Auren nawaran Nanda wata biyu ..
Jin wanan jawabin na Abba y Dan sanyaya ran Indo ,Yana tamby ta hakan y Mata ,Ina kunya ta hanata amsawa ,sai nawarace ta amsa d eh Abba yayi wlh t amince kunyace t hanata mgn Abbah mungode Abban mu ..
Murmushi yayi Yana yaba kawance irin nasu ,mama ma godiya tamai Tana cewa ta amince ALLAH yasa ayi damu …
Aunty zainab ma ta fito tabata musu dariya Tana musu wasa wai amaren su guda biyu ,sunkusa cashewa su rakashe …
Shidai Abba tashi yayi yabar musu wajen ,mama ma binsa tayi ..
Aunty zainab t dinga tsokanar su ,Tana Basu shawarwari d yadda zasu kula d kansu d mijin su ,aunty zainab t kware t kowane fanin a gidan Aure kadarace kawai t rabata d mijin ta d yaranta biyu mace d namiji sakamakon kishiya Yar tsibu d aka kawo Mata t ditar d ita d bala’in tsafinta …
Dan haka tundaga yau t k’udiri aniyar gyaran amaren guda biyu in and out kuwa ….
*********
Da dadare safwan y Zo godia gidan Abban nawara ,tare d tirsasawar Alhaji su Dan beso zuwa ba Saida yaga Kar Abba y fahimci wani Abu shine y taho …
Bayan sun gaisa d Abba ,y sanar Mai shine SAFWAN ,suka sake gaisawa d Abban nawara ..
Abban nawara y sakar Mai fuska sosai yayita Mai Hira d nasiha d rike Indo marainiyar ALLAH tsakani d Allah d Bata kariya Akan tsohuwar matar shi …
Safwan duk ya cemai zaiyi iya kokarin shi ,y dinga Mai godia ..
Abba y gayamai yadda Abin ze kasance gudun Kar Indo t kuntata ko taci gaba d kin auren Dan dakyar ta amince d nasiha d taimakon ALLAH suka samu ta yadda ..
Dan haka za’a d’aura Auren Nanda kwana 4 Amman Bazata tare a gidan kaba sai Nanda wata biyu , kafin Nan ta Kara kwarewa akan sana’ar d take koyo ,Kuma kafin lokacin yayi daidai d d’aurin Auren kawarta aminiyarta nawara sai na hadasu n musu shagalin bikin su tare Dan taji cewa itama yatace Kuma Mai gata d ‘yanci kamar duk wata ‘ya …
Safwan yace to hakan yayi ,y gode ALLAH y Kara girma ,suka danyi Hira d Abba kafin Abba y umarce shi d yaje y gaishe d Inna …
Badan yaso ba y tafi ,yasa aka gayama Inna safwan ne ze shigo …
Tasa nawara taje ta shigo dashi tasan kotama Indo magana aikin banza ne b iya zuwa zatayi ba Dan sabuwar kunyar shi d ta dorama kanta ..
Cikin zumudi d murna nawara ta tafi t shigo dashi ,gudun Kar Inna taga kamar tursasamai Auren jikarta akayi ya saki ranshi y aro fara’a y yafa a fuskar shi …
Nawara tamai sallama ,cikin sakin fuska y amsa tamai iso zuwa wajen Inna …
Bayan sun shiga y duka y gaishe d Inna ,ta amsa cikin kulawa d yabawa ..
Yayi shiru yanata murmushi …
Nawara tace ango y shirye shiryen?
Y Sosa k’eya Alamar kunya yace munatayi har kema Ashe ankusa Ina naki ango ?
Sai taji kunya ganin anfara ‘yar kunya yasa lnna t tashi tabar wajen Tana Indo kizo ku gaisa Mana …
Indo badan taso ba tace toh Inna Ina zuwa …
Ganin Taki fitowa nawara taje ta taho da ita ,ta zauna nesa d safwan ko kalon ta beyi ba …
Ba Dan kwali akanta daga doguwar Riga sai gyale d ta yara har kanta fuskarta tayi kyau …
Ta fara magana ,Dadyn su Noor Ina wuni ?
Y d’ago a hankali yace lpy Auntyn su Noor ,y gidan Inna tunda kin kuji su Haneef !
Tace laa wlh b haka bane dinki nake koya shiyisa kaga Kuma Yana bukatar Nutsuwa d zama waje daya …
Yace lalai Kam ALLAH taimaka ..
“Nawara tace Amin Ango mijin Amarya”
Indo Tama wani kalo ,Ashe safwan n kalon ta ,yace karya t fada ?