KUSKURE Complete Hausa Novel

Indo t sunkuyar dakai Tana murmushi ,haka kawai taji nishad’i na dibanta …..
Sundanyi Hira tsakanin safwan d Indo amman nawara duk ita take asasa hirar ,har safwan y musu sallama yaba Inna kudi d kyar t karba seda y dinga Mata magiya d roko …
Yacema Indo duk Abinda take bukata ta Mai magana kafin Nan d kwana 4 kafin a d’aura Auren…
Nawara ta amsa d toh ango mijin Amarya …
Nawara t rakashi har bakin motar shi ….
Abban nawara y Kira ,Alhajin su SAFWAN y sanar Mai d komai game d yadda yadda bikin d tariyar ,dama safwan y Gaya Mai yace b komai sungode d karamci sai D’aurin Auren idan sun had’u …
Anata gayatar mutanen d suka Dace d’aurin Auren Aishatu d safwan …
Kowa na gidan y sani har iya Mai Aiki d hidaya Dan hartace ta tsokani Indo ma sun had’u d nawara sunsha Hira ..
Duk Abinan d akeyi huzna Bata sani ba sakamakon rashin wuni a gidan d batayi Tana yawon gidan kawaye ,har t Kama yau zata koma garinsu Dan Shirin komawa makaranta ..
Bataso hakan b Dan Bata cimma burinta ba Akan safwan d’inta ,Amman yanzu zatayi babban shiri Dan har hajiyar ta zata sanar ma Dan tashiga maganar ko safwan ze yadda d ita …
Har Tasha suka kaita hassana d ussaina Dan ji sukayi kamar zasu rabu d Kaya…
Safwan ma har kudin mota suka Bata d Yaya d Ammy har Abba hakan y faranta ranta ta kara yadda d cewa suna sonta yanzu zata bayana kudirinta kowama y sani d ta sake dawowa Dan haka zata Fara yada manufarta ta waya ….
Gobe d’aurin Auren Indo d safwan a masalacin unguwar su ,angayaci mutane musamman dangin safwan din sai wasu daga Yan uwan Abban nawara d maman nawaran sai ‘yan unguwa d mijin aunty Mai d’inki …
Indo ko ji ta dingayi kamar a Shirin film wai aurenta ? Shikenan ta zama matar Aure ? Gani Tana so tasama kanta damuwa su aunty zainab d hidaya dama tazo d nawara d aunty Mai d’inki suka dinga janta d raha d wasa seda suka dinga sata fara’a ta hanyoyi kala2 Dan kusan a gidan suka wuni Don aranar aka kawo akwatunan Aurenta guda 5 masu tsada d kyau shake suke d Kaya makil ..
Su maman nawarane Akan kayan ,sai wasu yardadun makotan su …
Kowa y yaba d kayan sunata sa Albarka ,Indo ko idonta ko akwatunan be kalaba ,su hidaya da nawarane suketa Bata lbr Tana rufe fuska Tana Jin kunya …
Ammy d wata kawarta ne suka kawo akwatunan ,sukata Hira d maman nawara Dan har sun Saba ,mama n cema Ammy ga amanar ‘yata Nan dai n baku …
Ammy d kawar ta suna cewa sun karba , ALLAH y tayasu rik’o ..
Anata Raha d dariya Abin gwanin birgewa d Sha’awa ,aka gama girkin Alfarma daga gidan mama aka kawo d su drinks …
*MAMAN SHAHEED*????
[1/14, 12:55 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????
BY
“`MAMAN SHAHEED“`
*KUKUSKURE*????????♀_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)
_shafi n talatin d tara_
“Bayan kowa y watse daga Inna sai aunty zainab sai nawara d Indo ,su aunty zainab suka matsama Indo sai taga kayanta ,badan taso ba amince ta bisu “suna d’agawa suna nuna Mata,wani ta kala wani taki kalo dan basune agabanta ba,nawara sai tsokanar ta take Tana ware Wanda zata dinga d shagalin biki afadar kawar tata”
“Ita dai lndo harara take makoma nawara ,itako sai gwalo take Mata ..
Inna nata karantar yanayin jikar tata Dan t tabatar d tayi naam d Auren ko haryanzu Bata gama Amincewa ba,tunanin ta y Gaza gano Mata hakan ganin ta take ba yabo ba falasa dai kawai ……
Ranar nawara agidan su Indo ta kwana ,kwana tayi Tana bama kawarta shawarar ta kwantar da hankalin ta tasama kanta hakuri d juriya d Mika lamarin ta zuwa ga ALLAH da sannu zai isar Mata akan komai da taci Karo dashi a Rayuwar ta ,duk Abun d kaba ALLAH zabi da sannu zakaga daidai insha ALLAH….
********
Washe gari da safe ,gidan Ammy Anata shiri Dan anan za’a hadu a wuce unguwar su Indo d’aurin Aure …..
Mama d Abban nawara sun bada order duk wani Abu da za’aci asha a restaurant Mai kyau d dandano na Yan d’aurin AURE Dan tun jiya mama ta Hana Inna aiwatar d komai tunda b taro zasuyi ba sai taron masu shaida Auren AISHATU D SAFWAN Dan haka zasu d’auki nauyin komai sukace …
DaTaimakon Yaya y sa kanin SAFWAN y fara shiri ,Dan har ya fara zargin wani Abu game d k’anin Nasa ,atunanin Sa so d kaunar NAWAL ne yake hanashi sukuni d har baya bayana over farincikin sa Akan Auren shi d Indo Alhalin shi yasa aka nemar Mai d Alk’awarin zebata kulawa ….
Dan haka y shareshi batare da ya nuna Mai ba ,ganin b wani shiri yakeyi b ,abokanen sama ba kowane yasan d d’aurin Auren ba ,Dan haka Yaya y Mai d’inkin boyel d wani yadi Mai kyau d tsada Wanda sukaji matsiyacin Aiki ,be ba kanin nashi ba sai yau da safe d turare Dan gaske d agogo _lnka Isa kaima kasa_ d takalmin _komai na babba yafi na yaro_ ya nuna Mai boyel din zesa ….
Safwan ko ganin soyayya ce tasa yayan nashi yamai wanan gudumawar “dan da wata sabuwar shadda sa zesa Riga d wando dama yanada kusan kala 4 a ajiye danshi ma’abocin sabon dinki ne Koda yaushe Dan haka ma Alhj su be damu d y Mai mgn Akan kayan d zesa ran d’aurin AUREN ba …..
Su hassana ma sun dinka wani shegen material ita d ussaina d Noor d hidaya Dan sun Dan karata aciki harda aunty sufaya matar Yaya ..
Shi Kuma Yaya ya dinka musu wata arniyar shadda shida Haneef iri daya yaba ussaina yace t samai anko y musu …..
Dan su sundage se sunje gidan Inna ,amatsayin ‘yan uwan Indo suke b dangin miji ba Dan sun zama daya , Ammy taso t hanasu Amman Yaya yace t barsu ,shiko safwan kodan farin cikin yaranshi baze goyi Bayan a hanasu ba ….
Bayan sun shirya sufayya suke jira Dan so suke a d’aura Auren suna can …
Itama Indo mama ta musu wani d’inkin gagawa Dan tasan ba Abin d suka tanada ,Dan haka ta dinka musu wani code less t musu anko harda aunty zainab ,Amman na Indo y banbanta d nasu t kowane siga …
Aunty Mai d’inkin Indo ma t musu Ankon wani material ita d Indo Mai kyau Mai matsakaicin kudi d’inkin yayi kyau …
Mama har Inna t dinkama sabuwar atamfa ,d aunty zainab t kawo musu kayan d sasafe Inna harda guntun hawaye tanata godia d shima Abban nawara d mama Albarka Tana cewa na ALLAH basa karewa …
Cikin gagawa nawara ta tirsasama Indo ta tashi ta shirya ta Mata wata kwaliya dake dama Tana koyan kwaliya Indo kamar ba ita ba fanc ……
Nawara ta dinga d’aukan su hoto ita d Indo Amaryar yau ,aunty zainab ma nata tsokanar su ….
Suna cikin hotuna hidaya t karaso t shigo aka dingayi d ita har d Inna Saida nawara ta d’auke su ….
Indo dai haka kawai taji jikinta y fara sanyi ta rasa dalilin hakan ….
Kowa y shirya nawara aunty zainab ,Inna sai hidaya su kadai agidan ,mama Tana gida Tana jiran Abincin Yan d’aurin Aure….
Misalin karfe 11:8am su Hassana ,sufaya,ussaina,Noor,sun iso gidan Inna …..
Daga baya ma aunty Mai d’inki ta Isa, tagaishe d Inna ta shige cikin su aunty zainab sunata Hira ..
Jama’ar gidan Ammy,
Suka shigo d farin cikin ,suka gaishe d su Inna d aunty zainab ,ganin su ne y Kara sanyayar ma d Indo jiki ,tasan cewa yanzu ba mafarki ko tatsuniya akeyi ba ,shikenan ta faru ta kare dagaske aurenta ze tabata d ubangidan ta mijin uwar d’akin ta, ita wanan Aure d aka nacema batasan dawane suna zata Kira shi ba, gaskia d da Hali d anfasa d tanada iko d tayi gagawan dakatar d Auren Dan batasan zaman d zatayi d ubangidan nata ba a matsayin me zata gidan shi bade Mata ba kamar yadda Bata tab’a tunani ko mafarkin shi a Wanda ze zama mijin taba ,innaa tazarar d nisa …..