KUSKURE Complete Hausa Novel

Ganin t shagala d tunani Noor nata Mata magana ,yasa nawara t dawo d ita duniyar d’aurin Auren ta …
Amarya yarinyar ki fa ta Gaza samun walwalar ki yau ,Dan kiris y rage tayi fushi d sabuwar momyn ta …
Aiko ussaina tasa dariya sufaya ma suna cewa ‘ya Bata fushi d momyn ta ai ..
Ganin duk sun fahimci inda t Lula ,yasa t kirkiro murmushin Dole t jefama Noor t dauketa ta rungume Tana tambayanta Haneef …..
Noor tace Yana wajen yayan dadyn mu suntafi d’aurin Aure…
Jin an ambaci d’aurin Aure tasan Kuma natane ,yasa ta tsaida tmby tace to my Noor y Ammy fa ?
Noor tace Tana gida tanata murna Ana biki yau a gidan …
Kowa seda yayi dariya ,nawara t cema Noor bikin wa akeyi ne?
Indo t gala Mata harara kowa y gani ,sukasa dariya ,Noor tace Nima ban sani ba ! Aunty Ussaina bikin wa akeyi ma?
Ussaina tace bikin Aunty Aishatu mukazo mana !
Indo Bataso amsar d ussaina t bayar ba ,Dan haka tayi fuska …
Aiko Noor tayi shewa tayi tsale t dire a jikin Indo ,laaa Ashe bikin kine aunty Aishatu Zaki zama Amarya ? Amman Zaki dinga zuwa gidan mu ko?
Dake b wayo ,abinka d yaro batasan Aure seda ango ba ..
Indo t gyada Mata Kai ,Alamar eh Mana ,ussaina zatace wani Abu hassana t hanata ,Dan t Lura Indo so take a sayama Noor wani Abu …..
Dan haka suka dinga Hira Noor ko na makale d Indo duk inda tayi …
11:30am mad’aura Auren Indo da safwan sun had’u duk d Ango be karaso ba Yana hanya amman waliyan amgo d Amarya suna Nan ,
Abban nawara shine waliyin Amarya d abokanen sa d wasu ‘yan unguwa masu mutunci ,…
Abokin Alhajin su SAFWAN Mai suna Alhaji Saminu Ahuta shine waliyin ango sai abokanen Alhj d ‘yan uwan Ammy d wasu daga abokanen safwan Wanda Yaya y gayato sai abokanen yayan ,waje dai yacika makil ….
“`AN DAURA AUREN *SAFWAN DA AISHATU* AKAN SADAKI DUBU TAMANIN LAKADAN BA AJALAN BA“`
“Wanan shine Abin d y daki dodon kunen ango d karasowar shi kenan shida yayan shi d wasu abokanen sa ”
Wani faduwar gabane y ziyarce shi ,Wanda a yanzu baida lokacin Mai fassara ,sai rintse Ido d yayi ….
Ana hango shi akafara zuwa Ana Mai ,murna Ana gaisawa dashi ,ganin Yaya y tsare shi d Ido yasa ,shi saurin sakin fara’a Kar Yaya y jefo Mai tmby d baze iya kare kanshi ba ..
Tun daga lokacin y saki yake Wanda yafi kuka ciwo ,y dinga dagama mutane hannu suna gaisawa cikin sakin fuska d fara’a …..
Ganin fara’a safwan y faranta ran Yaya yaji Babu wani Abu aranshi sai Abun d baza’a rasa ba ,Dan tun yanzu yayi Alk’awarin shiga Rayuwar gidan kanin nashi gudun zargin shi y zama gaskia akan ‘yar mutane d aka Basu Amana ….
Anata rabon goro d sweet na d’aurin Aure anata Addu’a ta nemanma Auren Albarka ….
Abban nawara yasa aka Fara fito d takeaway Ana rabama mutane ,ganin Ana rabo har Wanda Basu halaci d’aurin Auren ba seda sukazo karban nasu rabon …..
Haneef na makale d hanun Yaya duk inda yayi Yana biye dashi …
Yayane y dinga sawa Ana kashe musu hotuna shida kanin nashi d su Alhj d abokanen sa d Abban nawara d sauran abokanen su ,Ango Dole y saki jiki Yana fara’ar Dole aka dinga kashe hotuna …….
“Kirjin Indo ne yayi mumunan bugawa sakamakon wani yaron makocin su d y shigo da Abin takeaway Yana yagar kaza Yana cewa wlh sun sheda hajia Indo kinzama Amaryar Wama ? Oho nidai naci na k’oshi ALLAH y baku zaman lpy d Yaya masu Albarka kamar yadda naji manya na fada ,ya gaishe d Inna y fita d gudu d kashin kaxar sa Yana taunawa….
Awajen Indo ta sulale ta Fadi ,ita Bata Suma ba ita Bata motsa ba …
Hassana d sufaya suka yo kanta d gudu ,Inna ma rudewa tayi ta taho Kan jikar tata d ta rage Mata kuka har y kwacema Inna ….
Nawara ma ihu tasa ta Fara jijiga Indo Tana Kiran sunan ta ,aunty Mai d’inki ma tanata jijigata,Noor ma kuka d ihu tasa Tana cewa wayo aunty ki tashi duk sun rufu akanta …
Aunty zainab ce ta Lura t kifta ido da kuma hanun ta d ya motsa ,duk acikin su b Wanda y kula d hakan …
Dan haka tace ,kuyi shiru Dan ALLAH ba Suma tayi ba kawai dai yanayi nee ta shiga na wucin gadi ,Amman idon ta y motsa d hanun ta ….
Sai a lokacin kowa y Lura ,nawara t Kira sunan ta ,ta bud’e Ido t kaleta ,taga hawaye a fuskar Inna t talabo fuskar inna tace innata kuka Kika?
Meya same ki ?
Inna tayi saurin share hawayen ,tace b komai tashi ku shiga daki …
Ganin mutane duk sun zagaye ta ‘tace yadai hassana?
Sufaya d aunty zainab,da aunty Mai dinki sukace ba komai muna tare da Amaryar mune kawai tashi mu koma daki …
Suka kamata sukayi daki d ita ,inda nawara ta d’auki Noor tayi d’akin Inna d ita tanata rarashin ta Saida ta lalab’ata d kayan cincin d fanta tayi shiru t gyara Mata fuska Kar Indo t Gane tayi kuka….
D gudu Noor ta hau jikin Indo ,Tana cin abinta taba indon ta bud’e Mata fanta tata ….
Noor t dinga tursasa lndo wai itama taci ,sanin dabarun biyema yaro yasa ta karba taci badan Tana so ko Sha’awa ba …..
Har nawara t karo musu ,Indo turawa takeyi kawai har t toshe wani kafan …
Nawarace t gayaci hassana d ussaina d hidaya Dan karbo musu nasu Abincin d Abin Shan su a gidan mama …
Niki Niki suka dawo d Abinci kuwa ,Nan aka shiga zubama kowa ,suka dinga ci Ana Hira Ana Raha Banda Amarya d jikin ta y gama la’asar tunda taji andaura Mata Aure d ubangidan ta .,..
Suna cikin cin Abinci ,Yaya y Kira hassana yace Mata Yana kofar gida Haneef yace sai ankawo shi wajen Amaryar baban sa …
Tayi dariya t tafi karbo Haneef din..
Bayan t dawo ,Haneef y tafi wajen Indo ,ta rungume shi Tana Mai magana a kune ,
Sai murmushi yakeyi,
Nawarace t kamo haneef Tana cewa yazo t zubamai Abinci ,Aiko y noke kafada yace shida aunty Aishatu zeci …
Hidaya tace to gareki Amarya ,sekuci gashi Nan anzubo muku ..
Indo badan taso ba ta karba ,ta Soma bashi itama tanacin kadan2 har sukaci iya ,Abin da zasu iya ci ….
Ansha Hira ansha shafta a gidan Inna ranar ,sudai d haka sukayi yinin d’aurin Auren indon …
Ita dai Indo ,jiki ba kwari take aiwatar d komai kowa y Lura d hakan ,Amman atunanin su komai ze zama lbr ….
Su hassana, Ussaina,aunty sufaya,hidaya,Basu bar gidan Inna ba sai d Yama lis gab da magriba,Bayan ansha artabu d su Noor wai bazasu tafi ba a gidan Inna zasu kwana ,ganin kukan d sukeyi harda majina Inna t roki Alfarmar a barsu ko zuwa gobe Azo a d’auke su ….
Haka suka tafi suka barsu …
Aunty Mai d’inki ma ta tafi ….
“Bayan sun koma gida ,kafin Ammy ta tamby su ,suka Bata lbr dambarwar d aka Sha har aka bar su Noor acan …..
Dadyn su yanaji Amman bece komai ba Yana cin Abinci ,sai a lokacin y tuna d Auren Indo d yayi ko ba komai yaran sa za suyi farin ciki da hakan uwa uba matsalolin su da yi musu hidima….
Indo ma ranar batayi kwanan tunani ba sakamakon su Noor d suke damun ta da hirar su …
Nawara ma gidan mama t tafi t kwana d aunty zainab ,daga Inna sai Indo da Noor d haneef aka Bari a gidan ….
Ammy ma tace ma SAFWAN gobe sai yaje ya dauko su Noor Dan me d’auko su a wajen Indo sai shi ,inba haka ba bazasu dawo ta dadin Rai ba .,..
Badan yaso ba y amsa d ALLAH y kaimu goben ,y tashi suka raka Yaya d aunty sufaya suka tafi gida shima y wuce inda ze kwanta zuciyar sa cike d tunani …..
*Maman shaheed*
[1/15, 8:34 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????
BY
“`MAMAN SHAHEED“`
*KUSKURE*????????♀_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)