KUSKURE Complete Hausa Novel

Nawara tace sorry kawar ,ba Ayi haka ba mugama cin Abincin ,kinsan hydar zezo shiyisa nakeso naje n shirya kafin…
Bayan sun gama ci ,nawara harda Kari d su noor .
Nawara ta tafi Dan shiryawa kafin choice d’inta yazo ..
Indo Kuma ta gyara wajen …
**********
Ammy tanata neman SAFWAN Dan taji ko ya tafi d’auko su Noor..
Ta Kira shi a waya be d’auka ba …
Shiko Yana sane yaki zuwa dauko su wai Kar yaje aga kamar wajen Indo yaje Dan haka yayi shigowa gidan Ammy ,Yana gidan shi yabata neman wasu takar du…
Seda yaga Isha ‘i tayi ,sanan yayi sallah ya dawo gidan Ammy ,
Yana zuwa y wuce parlon Ammy yaga Bata Nan y bita d’aki y fara nuna Mata mantawa yayi d maganar d’auko su Noor shaf ,tashi dare yayi yanzu …
Ammy tace ,wlh nazaci ka tafi tun yamma ganin ankira magriba baka shigo bane yasa na kiraka baka dauka ba ..
Aiko yace Ni Ammy ? Kuma Banga kiranki ba ! Kinsan wani lokacin network Yana shangiya ,Sam be shigo ba …
Ko naje yanzu?
Ganin kamar agajiye yake tace aa abarsu zuwa gobe ,Dan tasan basu matsala indai suna tare da Aishatu…
Yaji Dadi dama irin abinan ne ,bason zuwa yakeyi ba …
Bayan yaci Abinci y k’oshi ,
Hassana tazo ta same shi tace Yaya Ashe su Noor se gobe?
Yace eh ,tace ALLAH kaimu..
Itako ussaina sarkin magana cewa tayi ,Yaya Amman dai anan gidan Zaku Fara zama kafin ka koma gidan ka ko ?
Ya Mata wani kalo ,tace toh Dan ALLAH Yaya matambaya ai baya Bata ..
Ammy Najin su ,tace gaskia Kam ussaina !
Jin Ammy tasa Baki yace ,to kin Bata anan ba anan zamu zauna ba !
Ussaina tace Kai Yaya guduwa zakayi d ita ?
Yace eh sace ta zanyi !
Ussaina tace Ni ba haka nake nufi ba Yaya ..
Hassana da Ammy suka sa musu dariya …
Can ussaina tace ,su Noor fa Amman anan za’a barsu ko daga baya ma kawo su ko yayana?
Ya Mata wani mugun kalo yace , se yadda Kika tsara Mana uwar mutane ,umarni kike bani ko shawara?
Tace Kai Yaya Ni namayi shiru bazan Kara cewa komai ba ..
Yace dadai yafi ,Mai surutu kamar aku kawai ,inda kuka banbanta d hassanar ki kenan …
Tasa dariya Tana cewa Kai Yaya bamu d banbanci wlh ,kodan ita halin ku daya ,sai kunga dama kuke surutu?
Ya Wurgo Mata wani kalo ,Saida ta matsa kusa d Ammy , Ammy tace gaskia t fada ai tanama tmbyy masu Amfani kana Bata amsa a hassale kamar ba ‘yar uwar ka ba ..
SAFWAN yace Kai Ammy ,ussainan na Taki wlh wani lokacin sai ahankali shiyisa muke fada d ita wani lokacin ,Kinga ai bamayi da hassana !
Ammy tace hakane Kuma ,…
Sanan y tashi y tafi d’akin d yake kwana …
Su hassana, ussaina ,Ammy suka dinga Hira akan Auren SAFWAN d Indo d su Noor ,ussaina na cewa abarsu a gidan Ammy hassana nacewa sai ki gayamai ..
Ussaina tace ,wacce Ni me ,Ido ba Dan ciki? Kinajin Abin d y gama gayamin Yana bani amsa a dakile …
Ammy tace badai ruwansu d maganar gidan shi ,su zuba Ido kawai ,musamman ke ussaina ….
Ussaina tace to Ammy ,can wayar hassana t hau Kara ,ta Kali idon Ammy t tashi ta tafi d’akin su Dan amsa wayar..
Ussaina tace ,aa lafalafan soyayya ,Yar uwata ki baro Mana d kyau …
Ammy ta kaleta tace, oh ussaina Dole ku dinga samun sabani d yayan ki ,hassanar ma sekin tsokana?
To ,ai nasani so kike kimin gulma ,to ai nasani saurayin ta kikeso ki fadamin ne ya kirata ….
Kema Kuma ai nasan ,me damun mu d way d har akesata a vibration ,ussaina Taki kunya d gudu t tashi tayi d’akin su ….
Safwan y shiga daki y kwanta y dinga tariyo, maganar ussaina …..
*Maman shaheed*
[1/16, 10:12 AM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????
BY
“`MAMAN SHAHEED“`
*KUSKURE*????????♀_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)
_shafi n Arba’en d daya_
“SAFWAN y shaga Daki ya kwanta y dinga Tariyo maganar ussaina”
Shi bema taba wani tunanin bada yaran shi ze tafi ba ,in be tafi dasu ba to waye ze bashi farin ciki a gidan ?
Su Noor ai sune ginshikin zaman gidan ….
Cikin tufka d warwara y kwana ranar ….
Bayan gari y waye ,huzna ta adabe shi d Kiran waya y dinga Danna Mata busy ,yaki daga wayar ta …
Bayan y shirya yaje ya gaishe da Ammy d Alhj su y karya yayi Shirin tafiya office ,y musu sallama …
Ammy ta dawo dashi d cewa ya yi kokarin zuwa y taho dasu Noor karya ce mata y manta ….
Safwan yace to Ammy zan taho dasu …
********
Washe gari Indo ta tashi ta gyara gida ,Tama su Noor wanka ta sake cire musu kayan su ta wanke , Inna nata cikasu d kayan siyarwan ta su Aya d gyada d alawar Madara sunaci suna Mata Santi Tana jansu d Hira hankali kwance ita kanta Tana son yayaran har ranta ….
Bayan Indo t Kamala komai kayan su sun bushe ,ta mayar musu ,ta daukesu sukaje gidan maman nawara Dan su gaishe ta …
Cikin fara’a d wasa mama ta karbe su ,suka gaishe d Abban nawara shima Yana tsokanar su Yana musu wasa sunata mayar Mai d amsar tsokanar d yake musu ,batare d sunmai rashin kunya ba Dan yarane masu Nutsuwa Basu iya rashin kunya ba Sam ….
Itako Indo Tana wajen aunty zainab d nawara ,suna hirar jiya d hydar y dinga cema Indo Amarya ,daga baya tsokanar sa ta Kore ta …
Aunty zainab ta Dora d ,ma Indo bayani Mai ratsa jiki akan Aure d abin da ya shafi Aure ,Tana Mata bayanin nauyin d yahau kanta ayanzu ,Dan ko Ina zata sai ta tmby mijin ta kafin ,take cewa har gidan d’inkin d zata cigaba d zuwa t sanar Mai hakin sane in ya yarda tacigaba d zuwa inko be amince ba tayi hakuri ,Dan nauyi d kula da ita ya koma kanshi andaura anshafa Fatiha …
Jikin Indo yayi sanyi duk tasan haka Inna ma Tana yawan Mata tuni Dan dakyar ta barta tafito yanzu ma Dan tasan gidan su nawara zatazo shiyisa ta barta tasa hijab harda nikab Dan kare fuskar ta daga ‘yan bani na’iya ‘yan unguwa ..
Taji ita dama ba’ayi Auren Nan ba ,tashiga takura haka kawai shi Yana can Yana fita Abin shi …
Aunty zainab ba iya Nan ta tsaya ba ,har dabarun rike miji d nunama miji so d k’auna seda ta Fara nuna Mata ,duk d indon Taki Bari ma su hada Ido ,Dan kunya ….
Nawara sai murmushi take Mata ,itako Indo sai Wurgo Mata harara takeyi …
Bayan aunty zainab ta gama ,suka shiga Hira Kuma ,anan Indo ta sake ta Fara hirar Kuma ,Aunty zainab nada kirki ta d’auki Indo kamar ‘yar ta haka kawai taji Indo na birgeta gata tasan darajar mutane ,kadarar Aure CE kawai ta fad’a Mata aka tabata d yaranta d mijin ta ,Amman badan taso ba tabarma ALLAH komai Dan ita Bata iya aikin sabo ba ,tsafi ko wani sihiri Bata iya ba Dan haka ta fawalawa ALLAH komai ….
Sunsha Hira nawara taba Indo littafin d tace zata Bata ,Taki karba Indo Tana hararar nawaran..
Sai d aunty zainab tasa Baki sanan ta karba ..
Aunty zainab ta gaya musu Abin d zasu Fara ci tun yanzu da Wanda zasu guji ci yayin jinin hailar su ,irin su cocumbar,da abubuwan da suka shafi Zaki ,suna harfar ma mace da matsala yayin d take jinin haila takiyaye su harsai ta Kamala ….
Sanan ta musu bayanin abinda zasu dinga gyara kansu tun yanzu base lokaci y Zo kusa ba ,ta umarce su day Amfani d ruwan dumi yayin tsarki da tsaftar lungu da sako tasan su d tsafta Amman tace sai sun Kara Dan tsaftar gidan miji sai andage matuka …
Ta babasu addu’o’en neman tsari da kariya daga sharin duk wani Mai Shari ,har tace Akwai addu’a d zata Basu su riketa suyi kafin shiga gidan mijin su insha ALLAH badai mutum ba sai ikon ALLAH…
Sunata Mata godia ,ta hanasu Tana cewa ,in Bata gyarasu ba wa zata gyara ,tamkar ‘ya’yan cikinta ta daukesu Basu d bambamci d yaranta duk d dama yaran nata ne ,sukayi dariya ..