HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Mamace tace nawara kizo ki raka Aishatu gida ,kinsan yanzu ba matsayin ku daya ba ,darajar ta ta haura Taki !

Aunty zainab tace hakane Kam ,Amman Yaya Kar ama Yar tawa gori Mana itama fa ta kusa tako matakin ,Tana kalon nawaran ..

Itama bawaran cewa takeyi yauwa aunty nasan in kina Nan bazanji kunya ba ,Tana ma Indo gwalo …

Indo tace ,Mara kunya ki fada mama taji Mana ,d aunty tabarki ma d dakanki Zaki Bata amsa ko rasa kunya beran tanka?

Nawara tace a haba bankai Nan ba yarinya ,Indo tace indai kece kin wuce haka ma ….

Nawara ta mitsine ta ,indo t Rama ,sukasa dariya aunty zainab Tana kalon su …

Bayan nawara t raka Indo ,kafin suyi gida d kyar nawara tabar Indo ta leka gidan aunty me dinki ta nuna Mata su Noor ta sanar Mata zata dawo koyan dinki fa ..

Aunty tace ba matsala indai oga y amince kafin y d’auke Mana ke …

Indo tace ,to Tana Nan zuwa ,

Aunty Mai d’inki ta d’ebo abubuwan ci taba su Noor sunata godia ,nawara taja Indo zuwa gida ..

Bayan nawara ta gaishe d Inna …

Inna tace yanzu nake magabar ta ,nace Kar aga rashin hankalin mu Kar wani daga gidan su Noor yazo d’aukan su aga bakwa Nan , girma beyi Aiki ba kenan ..

Nawara tasa dariya tace ,mama ma ta Gaya Mata har aunty zainab ,yanzu bazata sake fita ba sai ta tamby izinin shi ,inya yarda har gidan mai dinki zata koma inbe yadda ba ko sai Amarya ta hakura Tabi umarnin miji…..

Indo ta harareta ,tace zance sekace babba!

Nawara tace ,d me kika d’auke Ni ,…

Inna Tana musu dariya tace a dai tmby Kam in bazaki iya tmby ba ki Bari ita nawaran ta tmby Miki ….

Nawara tace zata ma iya Inna kawar tawa ai tafara saki ,makaman yakin ta yarage kawai ta zubar ,shima ankusa ..

Inna ta mik’e tace kudai kuka sani …

Noor d haneef suna jikin Indo ,Indo t tsefe ma Noor Kai Tana tajewa nawara ta tafi gida da niyar zata dawo anjima …

Indo ta rangadama Noor kitso Mai kyau ,ta gyarata ita d haneef masu Kaya daya inji Indo a zuciyar ta …..

 

Har kusan yamma shiru Babu Mai zuwa d’aukan su Noor ,Indo ta Fara tunanin ko lpy ?

Ko baza Azo a daukesu ba ai ,ataho musu d kayan canji ,Amman Kaya daya yau kwana biyu …..

Gashi amkusa komawa school ….

Har Indo t tashi ta gama girkin dare ta juye a cooler …

Har magriba tayi ,ganin anyi sallah ,Indo t zubo musu jaluff din shinkafa d taliya suka Fara ci abinsu …

Shiko SAFWAN Yana can gidan shi tun yamma y taso daga office ,yasan inya koma gidan Ammy ,korashi Ammy zatayi d’auko su Noor..

Dan haka y tsaya a great Dan shi ,so yake sai dare yayi kafin yaje dauko su yadda ba kowane ze San yaje ba ….

Bayan magriba ankusa isha’i ma ,sanan safwan y iso kofar gidan Inna ,da kyar y tsaida yaro y aike shi gidan Inna a Kira su Noor…

Ganin an aiko Kiran su Noor ,Inna bazata Bari su tafi haka kawai ba batare d tasan waye ba ,inta Aiki Indo ganin ko waye bazata ba ,zatayi tunanin mijinta ne ,Dan yaka Sam bazata ba …

Inna tacema yaron tace me Kiran su Noor din ya shigo Dan ALLAH!

SAFWAN badan yaso ba y shigo Dan dai yaron yace wata datijuwa ce tace y shigo d indon Ce wlh baze shigo ba …

Yana mita a ranshi yayi sallama Inna t amsa ya shiga …

Inna tamai iso cikin d’akin Indo ta shimfida Mai darduma Mai kyau d laushi …

Bayan y gaishe ta cikin sakin fuska ,yace kinji mu shiru jiya wlh Aiki ne y hanani zuwa yauma anso kwatanta hakan nace Kaya dayane dasu barin zo n d’auke su gashi ankusa komawa school..

Inna tace eh wlh ..

Inna ta zubo mai Abinci ,tace yaci kafin ta Kira su Indon …

Yace ta barshi y k’oshi ,tace a haba kamar ta bashi mugun Abu ai ko Albarka yasa ,sadai inko be saba cin irin girkin su ba …

Ganin ran Inna kamar y baci ,yasa SAFWAN cewa wlh b haka bane nida n Saba cin Abinci Aishatu Kuma na Nan ai baze gagareni ba …

Inna tace a ai daban ,wancan cefanen kune lafiyaye Mai name ko kifi ,sai Abin da kuke so za’a dafa muku wanan ko sai Abin d aka muku tayi …

Ganin Inna dagaske take ,inbeci ko Loma 1 ba ,zata Jima Tana Mai fassara yasa y d’au cokali yayi Loma 4 kwarar har d gyaran 3 ….

Inna tace ko Kai fa ka birge Ni,har naji Dadi tayi ta samai Albarka d Auren shi d Indo …..

Bayan y rufe Abincin Inna t Kira Indo d su Haneef tace g dadyn su …

Haneef d gudu yazo y fada Kan dadyn shi Yana murna ,Noor ko wai sai d aunty Aishatu zata je wajen dadyn nata …

Dole Aishatun ta d’auko gyalen ta kamo hannun Noor suka shiga d sallama..

Jin muryar Aishatun sai d gaban SAFWAN y Fadi ….

Ta zauna nesa dashi ,Noor t je wajen dadyn ta Tana cewa laa Dady yanzu kazo?

Kaci Abinci inna Mai dad’i ko Dady aunty Aishatu ce ta dafa Mana …

Ya kakalo murmushin Dole yace ,eh my Aku sarkin surutu ….

Aishatu ta gaishe d SAFWAN,y amsa cikin sakin fuska har y tmby ta y fama d su Noor?

Tace ba wani fama Abinda ta saba dasu ,kamar Kar su rabu ma …

Yace ko abarsu ?

Tayi murmushi Mai kayatarwa ,tace eh wlh d naji Dadi ..

Yace ,kamar gaske ,kingaji fa nasani sunata saki magana yadda bakyason maganan Nan ,ga hidimomi sunata saki duk sun fada min ai …

Aishatu tace wlh b wani hidima saniya ai Bata gazawa d kawon ta ….

Yace kin tabata?

Tace eh!

Yace ko ban gaba bazaki gaza ba?

Batare d tagane me yake nufi ba ,tace insha ALLAH..

Yace ,Alkawari kikayi fa ?

Ta sake cewa na sani ,na dauka Kuma ,batare d tayi dogon nazarin manufar sa ba ….

Yayi murmushi yace nagode , ALLAH ya barku dasu noor

Taji dadin godiayar ,tace Amin batare d ta fassara maganar shi ba ,da su Noor ma ba dashi ba !

 

Yace su taso su tafi ,y farama Inna sallama …

Noor tace Dady ka kaimu Shan ice cream Dan ALLAH!

Yace to Haneef ma yasa murna yace yess my Dady …

Noor tace amman da Aunty Aishatu zamu ko Dady ?

SAFWAN y d’auke wuta y kasa Bata amsa !

Indo Ce tace aa Noor ni Ina gida Kinga Kuma gidan Ammy zaku wuce Cox ankusa komawa school …

 

Noor tace to inbamu tafi tare ba nidai baxan bi Dady ba Ina Nan tare dake !

ganin rigimar Noor da gaske take .

Yasa dadyn yanke shawarar tafiya d indon ….

Yace rigimamiyace renon Taki ,kije ki sanar ma Inna muje sai na saki a napep ki dawo ….

 

Zata yi magana yace ,yanzu fa kikayi Alkawari kince kin d’auka Kuma duk yanada daga cikin Alk’awarin d Kika d’auka ,Kuma dai kinji Noor tace inba haka ba bazata tafi ba plsss kije kawai ki fadama Inna ..

Badan taso ba sai Dan y d’aureta d jijiyoyin jikin ta ,ta tafi sanar ma Inna …

Inna tace Adawo lpy ,mijin kine ai ,

Ba wani shiri tayi ba Riga d skit ne a jikin ta daurinta t gyara t canja gyale tad’an shafa humra ta fito …

Yama Inna salama suka fita ,Noor tanata murna Tana cewa Aunty Aishatu kinyi kyau wlh…

Indo baya taso shiga it’s d Noor ,tace Haneef y shiga gaba …

Safwan yace ba haka nake ba ,niba driver bane gaba Zaki dawo …

Zatayi magana yace banason musu haka nake ,magana daya nake …

Dan haka ta hakura ta ,ta zauna a gaban yanata shak’ar kamshin humra …..

Ba Abin d akeji sai surutun Noor d haneef suko amgo d Amaryar sun zama kuramai ,Amman sunata karbar sakonin juna ta cikin zuciyoyin su Dan ruwan luv suke Sha tacan ….

Bayan sun Isa wajen ,ganin lokaci zai kure gashi Aishatu zata koma gida ,ya ce su jirashi y fita y siyo musu y dawo y mikama Aishatu nata d wata babbar Leda ,

Ta bude Baki tace Ni na k’oshi!

Y Mata wani kalo yace ba cewa nayi kinajin yunwa ba ,ki karba inkinje gida ki zubar ….

Ta Gane magana y Gaya Mata ,Dan haka t karba Tana cewa Kai wanan wane irin salo ne ,irin zaman d zamuyi kenan y zama Dan bakar magana ……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button