HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Su Noor har sun Fara Shan nasu yaja mota ze hau titi …

Aishatu tace ba kace a napep zan koma ba seku tafi?

Y kaleta yace , insaki a napep din tuni kike min ? Atunanin ki na manta?

Tayi kasa d kanta !

Yace ban manta ba ,jeki hau ,ta bud’e motar zata fita yace d kudin d Zaki biyashi atare dake ko?

Yasan Bata d’auko komai ha ..

Ganin ze dameta d magana tace Mai eh !

Tana Shirin sa kafa ta tafi yace ,muga kudin ?

Cikinta y bada kululu!

Ya sake magana !

Tace na manta a gida ,Amman Yana sauke Ni zan shiga gida na karbo a wajen Inna na bashi !

Yace hmmm, ita Inna ajiya Kika Bata?

Tace ai nasan zan samu a wajen ta ..

Yace ,zade ki rabata d kudin ta haka kawai ,rufemin k’ofa mu tafi tunda Baki d na napep!

Zatayi magana yace ,nifa banason musu kiyi Abinda nace kawai !

Tace to Inna zaka kaini?

Yace gidan Saida mutane!

Noor tajiyo mgn har kwanyar ta ,tace laaa Dady kasan gidan d ake siyar d mutane?

Aiko gaban shi y Fadi ya manta d su acikin motar..

Y fara inda inda Yama kasa Bata amsa !

Aishatu ce tace, Noor bakiji me yace bane ,cewa yayi gidan sai da motoci ,…

Noor tace au senaji kamar sai d mutane yace Ashe ba haka bane ,ance ai masu ‘yankan Kaine suke Saida mutane ko aunty?

Aishatu tace kwarai ma kuwa ,kuma wuta zasu shiga ,ba kyau mutum y dinga fada ma kinji Noor d’ita ?

Noor tace,to aunty ALLAH na tuba ba abakina ba abakin wani sheda’n tuf! Tuf!!…

Seda kowa yayi dariya har dadyn su …

Ganin yayi kwakyariya ta gyara Mai Amman y saki Baki Yana dariya ta kulu ta dawo dashi da cewac….

Adinga gyara harce agaban yara sbd gudu kwacewar amsar bama yaro !

Lokacin d yayi daidai d isosar su gidan Inna ,ganin y tsaya t bude ta fita tace my Noor ne Haneef agaida Ammy d Alh .,…

Cikin tunanin furucinta tabar safwan ,ko amsa be Bata ba ,yashi ko magana Bata Mai ba….

 

Itako zata shiga kenan sukaci Karo d nawara ,Aiko nawara t Fara Mata oyoyo Tana tsokanar ta oyoyo Laila d majnun!

Sukayi ciki ….

Safwan dai Aishatu ta barshi d tunani ,da kyar yaja motar zuwa gidan Ammy zuciyar sa fal d tunanin Aishatu!

 

 

*Maman shaheed*????

[1/17, 4:52 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_Shafi na Arba’en d biyu_

 

 

“Bayan Safwan ya Isa gida ,kafin y shigo parlour da gudu su Noor suka afka d sallama suka cacime aunty hassana daga baya suka koma Kan Ammy d ussaina ”

Ammy tace aa ‘yan gidan aunty Aishatu andawo ?

Sukace eh Ammy ,Inna tace Tana gaishe ki d aunty Aishatu duk sunce agaishe ki da su aunty twins…

Ussaina tace muna amsawa masu Kaya daya ,hassana t harareta tace ,meyasa Baki Kai musu agajin canji ba?

Ussaina tace Dan Naga dadyn su zeje ne ai …

Ammy tace ,y Isa haka ….

Sai ga safwan y shigo d sallama fuskar sa d’auke d wani anuri ,Ammy seda ta tabatar d lalai yaron nata Yana cikin fara’a d walwala …

Tace Ashe ka biya ,Ina Nan inata jira ka dawo kace min ka manta na maida Kai ..

Safwan yayi dariya ,yace a haba Ammy d seki mayar Dani?

Tace kwarai ma kuwa ,abar yara d Kaya daya suyita Kwana su b wasu na canji aka Kai musu ba?

Yace da wanan Dan wanan ,Amman su wlh hankalin su kwance ko ajikin su wlh Dan da rigima ma suka rabu d wanan Noor din ….

Noor ta mikama Ammy Leda tace Ammy g naku Amman ku ragemin inyayi ragowa d Dadi ice cream din wlh…

Hassana tace Kai my Noor duk kinshanye Amman harda neman Kari ?

Haneef yace Nima sai Ankara min Dan yayi Dadi ,aunty Ussaina Sha kiji ..

Hassana t d’auka t Fara ba Ammy ta ba ussaina ta d’au nata ,Ammy dai cewa tayi sai y huce y Mata sanyi d yawa …

Ussaina dai cewa tayi ,tab bamu ko snow yake fitarwa haka zamusha ….

Safwan yace ,uwar magana be Baki kwadayi kawai…

Hassana tasa dariya ,har Noor d haneef seda suka tayata dariyar …

Ammy tace Ayi hankali d sanyi dai su Noor ma banaso Ana basu sanyin Nan ,Adinga rage musu sosai ….

Safwan yace ,wlh Ammy kinsan ba siya musu nake sosai ba ko sweet ban fiya siya musu ba” d dai dangin cake , biscuits ne to ,shima wanan ice cream din Dan mu rabu kalau ne ,

 

Noor tace ,Ammy kema bazaki Sha naki ba se anjima??

Ammy tace eh ,kishiya sa haushi!

Noor tace aunty Aishatu ma Bata Sha nata ba ,har d ita fa mukaje Dady y siya Mata y Bata ta tafi gida dashi …

Ammy taji dadin hakan ,tace Masha Allah,dadyn ku y kyauta min …

Shi kanshi y fuskanci hakan d yayi y faranta ran Ammy ,Amman kunyar maganar Noor tafi tsaya Mai Dan har keya seda y Sosa Noor kamar tmby akayi!

 

Ussaina tace ,inyeee Ashe har d Auntyn ku akaje Shan ice cream din Abu yayi ma’ana ,Tana boye fuska wai Kar Yaya safawan din y ganta …

Aiko y Wurgo Mata uwar harara ,na tashiga taitayinta …

Hassana tace yaya su Inna suna lpy dai ko?

Jin kalmar ta cikin hikima ba irin ussaina b ,yace lpy Lau suke hassana ta Dan har shiga nayi muka gaisa …

Hassana d Ammy sunji Dadi a tare suka ce Amman ka kyauta wlh …

Ussaina ko tun gargad’in d aka Mata Bata sake cewa ufan ba sai kwad’ayin ice cream d taketayi harda sama su Noor Albarka a nasu …

SAFWAN ne y hanko ta yace ,anji kunya rakumi da shanye ruwan Yan tsaki ,girma yayi gardama …

Ussaina tace ,to b tayi akamin ba ,bafa Abin d yaro y tsana irin Yama tayin Abu kaki ci ,haushi sukeji wlh …

Hassana tace gaskia ne ,uwar tsari babba ta gotale kawai …

Can Ammy tace akawo Mai Abinci ,Noor tace ai munci Abinci Amman dai zamu Dan Kara kadan muji girkin Ammy ko yakai na aunty Aishatu Dadi d dandano?

Harfa dadyn mu yaci Abincin Kuma yace da Dadi …

Noor ta gama falasashi gaban Ammy d su ussaina ,sai binta d Ido kawai yakeyi ,Yana cemata renon ussaina kawai !

Ussaina ta jata jikinta tace ba komai ,asan mutum asan cinikin sa yafi Dadi wanan nasan ko amakaranta bazata badani ba ..

Ammy dai cewa tayi ,kyaji dashi ,in yayi Dadi iyayen ki ne sukayi gasunan in beyi bama sudai sukayi ….

Ussaina tace Aiko Ammy ,kinsan iyayen Noor badai iya girki ba mussaman Aishatu another mother su Noor Dan t Dan daramu d girki duk d muma b baya ba nata kamar baiwane duk Dan safwan yaji take fadan haka ,kowa na wajen ya sani …

Shima Yana jinta ko kulata beyi ba ,Amman y tsinci kanshi d Jin dad’in yabon Aishatu d ussaina tayi ,har y tuno “Assignment” din ta tabarmai dazu d zasu rabu …

Ussaina kafin y jefo Mata amsa tabar wajen t tafi zubo musu Abincin …

 

Faten dankali ne kayan lambu da su hanta d Koda aciki yasha manja d Albasa ….

Daga safwan har su Noor kadan sukaci ..

Noor ta gama tsame kodar d hantar ta cinye ,taje kunnen Ammy tace girkin aunty Aishatu mu yafi naki Dadi ta gudu wajen hassana …

Kowa y dinga dariya har dadyn su ,Yana cewa Noor Ammy nawa kikema haka ko?

Duk duniya ba Wanda y kaita iya girki yarinya ,Dan shi naci na girma Kika ganni haka Yana nunata d yatsa.

Ammy tace ato son Gaya Mata dai ”

Noor t bude Baki tace ,Kai Dady dama ita ta dinga ma girki har kaci ka girma?

Yace eh Mana yarinya !

Noor tace ,Nima ai zanci girkin aunty Aishatu na girma har nafika girma Dady Tana kyalkyala dariya …

Haneef ma yace ,Nima ai nakusa girma na zama kamar Dady yarinya na fiki karfi ..

Duk suka samai dariya ,sunji kishin Haneef y motsa ….

 

Haka suka kwashi farinciki cikin wanan Daren kafin aka canjama su Noor Kaya zuwa sleeping dress ,aka musu addu’a ,Suma sukayi da kansu Dan kwanciyar barci ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button