HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Ammy ta tafi bedroom d’inta dake Alhj su yayi tafiyar kwana 2.

Shima safwan y wuce d’akin d ze kwanta ,na gidan Ammy inda aka aramai …

Bayan y gama komai yayi Shirin bacci ,Dan y gaji …

Koda y kwanta Dan yin bacci ,baccin kin zuwa yayi sai Al’amarin d y faru tsakanin shi d Aishatu yake tunanowa…

Tun lokacin d Noor ta yabi Aishatu ,shima tamai kyau Kam ,to Amman mezesa y yabeta ? Babu huja kodan Tana matarshi a yanzu? To ai shi b Auren So da k’auna sukayi ba hasali ma kawai y cike wani gurbi da itane …

Duk yarda yaso watsar da tunani ko Abin da ya shafi Aishatu ,zuciyar sa t kwakwalwar sa sunki bashi hadin Kai sunmai gardama sun nunamai be Isa ba …

Har waya ya d’auka y Fara shiga kafafen sada zumunta ,Amman y kasa katabus ..

Sema tunanin ta d ya sake bijiro Mai d “Assignment” din d ta bashi akan furucin d yayi agaban su Noor sai ita Aishatu ce ta kwace shi da kyar yayin d y rasa Amsar ba Noor din ..

Har t ke gargadan SA d y San irin maganar d ze dingayi gaban yara ,gaskiya ta fad’a ,Amman meyasa ta fad’a Mai haka ?

 

Kai zahiri Aishatu (Indo) yarinyace Mai hankali d nutsuwa ga lafuza da tunani uwa uba iya girki kula d yara d duk wani Wanda y kusance ta tasan irin hakin d zata bashi gata dai ba wata wayayiya ba ba wata Mai zurfin lilimin Boko ba na addine dai ta samu ba laifi …..

 

 

*SAUDI ARABIA*
{“`madeenah“`}
**************
wani Mutum tadijo kamili Mai yawan sumar fuska ,yanada Haske Amman Bai Kai hasken larabawa ba Amman ya Dara bakake ….

Yana cikin masalacin manzon ALLAH s.a.w yanata Addu’a Yana zubar da hawaye Yana Kai kukan shi ga ALLAH Mai wanzar da komai ayayin da yaso …

Saka makon wasu mafarkai da wanan datijon yaketa jerawa a cikin wanan satin ,Akan wani Abu da ya shafi Rayuwar shi …

 

Kusan kulin sai yazo massalacin yayi wanan addu’a tun daga ranar d y fara mafarkin ,sakamakon inda yake Akwai tazara d masalacin yasa d ba kulin yake zuwa ba Amman yanzu kulin yake zuwa Yana Addu’ar ALLAH y cika Mai burin sa ya Amsa rokon sa …..

 

*********
Nawal Aiki aketayi ba Kama hanun yaro ,hakali kwance d takayi tunani yaranta d son ganin su ,yanzu ko tad’an watsar d Abun ,Amman takan tuna gwarzon ta duk d yanzu t canja Mai suna ,Amman fa ta sani aduk duniya bazata taba son wani Wanda y amsa sunan sa namiji kamar SAFWAN ba ..

Amman duk d masifar son d takemai baze Hana inya musguna mata ta kuntata Mai ba Dan Bata yadda d Auren rashin ‘yanci d Mata sukeyi Dan suna son mazajen su ba ,Adinga tauye musu ‘yanci Akan wani dalili na daban …

Ita ayanzu take Kara sanin kima d ‘yancin d mace Mai Aure ko Mara Aure takeda shi ma ,Dan haka shed’an yayi gaba sun bishi abaya ,Bayan su Kuma Ana musu busa d satewar shedanci ita d tawagar kawayen ta …

Dan ayanzu Akwai wani d yaketa kawo Mata Hari wai Yana son ta ,ita Kuma Taki bashi fuska ..

Su Laila d doccas harda Karin wasu kawayen su guda 3 ma yanzu ,sunata Koda ta ,ai miji ko saurayi sai Wanda ta zaba ,Dan haka Bata da fad’uwa a Rayuwar ta …

Tayi sha’anin ta yadda ranta yake so ,suna tare d ita iya wuya …

Auntyn ta wacce ta taba Kira kanwar mama, tun Tana kiranta a waya tazo taji meya had’ata d safwan ,NAWAL Taki zuwa Dan dama rashin madafa yasa ta taba kiranta Dan tuntuni kanwar su bata jikuwa waje daya, Koda tazo gidan mama Jin gulma Bata Sami NAWAL ba ,bataji lbr komai ba Dan ko dangin su ba kowane yasan aurenta y mutu ba ansan dai mace ce ita Mai freedom kamar yadda wasu suke gulma a dangin nasu ….

Dan haka NAWAL d ita d kawayen ta take sha’anin ta kawai ,hankalinta kwance …

 

********
Bayan Aishatu ta shiga gida tare d rakiyar nawara ,ta mikama Inna ledar d safwan y musu siyayan kayan ciye ciye …

Inna cewa tayi kundawo ,? Tace eh ..

Inna tace to kuci Mana Kya turo min nasan baze wuce kayan motsa Baki ba irin naku na ‘yan birni ,Ni ko zanci sai zuwa anjima b dayawa Kuma ,gudun karnaci abu Mai nauyi na kwanta …

Dan haka Indo t turama nawara ,nawara ta harareta t dau ledar suka koma d’akin Aishatu…

Koda suka shiga nawara ta Fara aikin tsokanar Indo Tana cewa Amarya d Ango Calugude! ,sunje Shan iska Calugude !! Hardama yaransu Calugude!!….

Aishatu dai cewa tayi dalla malama Zaki Fara ko ?

Nawara tace wlh Abun ya matuk’ar burgeni ,kun masifar dacewa wlh , ALLAH maganar gaskia kinyi Dace kamar yadda nayi na zaben my choice …

Wlh kema ALLAH y kawo Miki choice dinki har gida ,da sannu Zaki samu fada abirnin masarautar zuciyar shi inda Zaki Mirza milkin ki a gaban jikin sa aikin masarautar ki ta Bayan d yabo a cikin gidan ki d yaranku na yanzu d na Nan gaba d Zaki haifo Mana insha ALLAH…

Aishatu tace ,Nita kin fara bani tsoro inkika yi hassashe Kan magana se aka Abun y faru ,Dan ALLAH ki yi shiru Ni Banga wata baiwa a tare dake ba ,Tana hararar ta .

Nawara tace har yanzu kina da ja d BAIWAR d ALLAH yamin ko ? Kindai gani Kuma Abu y Faru …

Aishatu t harareta tace, gwaiwa ba baiwa ba dai …

Nawara tasa dariya ..

Tace ALLAH kawata serious wlh ki San me kikeyi ,ki yadda da K’ADDARAR da ALLAH ya Dora Miki ,ki mikama ALLAH lamarinki kiyi biyaya ga mijin ki ki nuna Mai kulawa kija yaran shi d dangin shi duk d nasan Baki d matsala tanan ,

Keda kanki kike fadamin yadda uwar yarancan take tafiyar d mijin ta ,yadda duk wani namiji Wanda yasan kansa zesan inshi ALLAH Yana irin matar yasan beyi Dace ba duk d yadanganta d yanayin mijin ,Kuma keda kanki kikance Akwai gyararaki d yawa d Zaki iyama Rayuwar ta inda zata Baki dama ,har kinsani mijinta baya son yadda takeyi ..

Keda ga Satan amsa a bayane ,kinsan meyake so kinsan abinda baya so ,harya rabu d ita saboda wani dalili ,kefa komai fa Yana hanun ki wlh inkin so safwan y gama zama naki ,ta sakar Miki komai hatta zaman d kikayi tasu ke kikeda gidan ..

Kula d yara,kula d megida,d matar gida,duk wani Abu na gidan ,tayi ganganci sakar Miki d hurumin komai Alhalin duk ba naki bane ,uwa uba tsana d tsangwama ko wanan ya Isa yasa ki nuna Mata *’Yar Aiki* ma tanada Rana takanyi sarauta ta shinfid’a milkinta a inda ba a dauketa komai ba face kaskantaciya Mara gata d ‘yanci ya Kamata ki karyata batun ta ki gyara Mata tunanin ta ,har gatse tayi fa muku dalla kawata dama fa Tana hanun ki ..

Ni zan wuce gida gobe zamu Dora daga inda muka tsaya Dan ALLAH ki yi zuzurfan tunani akai ….

Nawara ta d’au ice cream daya ,Indo t Kara Mata harda wasu kayan cin ..

Yace mezamuyi dashi inkin barshi ..

Sukayi salama a bakin k’ofa ta yi Addu’a ta rufe kofar ta dawo Tama mikama Inna ledar ,suka kwanta …

Ranar Aishatu Indo tayi zuzurfan tunanin da tadade batayi ba ,Akan maganganun su day nawara …

 

*Maman shaheed*????
[1/18, 8:22 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi n Arba’en d uku_

 

 

“Bayan Aishatu Indo ta kwana cikin zuzurfan tunani Kan maganganun da k’awar ta ta Gaya Mata ”

“Taba kawar ta gaskia ta fad’a Mata ,to Amman ita bazata aiwatar d komai ba harsetaga yadda zaman su ze kasance da dadyn su Noor”

 

Zata yi iya yinta wajen yimai biyayar Aure Amman fa tsakanin ta dashi kadaran kadahan ….

 

*******
Kwanci tashi ba wuya bikin Nawara saura wata 2 Dan Alhj su nawara y gama komai na Shirin shagalin bikin yaran nasa biyu nawara d Aishatu Dan ya dinkama Aishatu sababin Kaya na kece raini Dan taji itama ‘yace kamar kowace ya Mai ‘yanci ,ya Kuma Mata Alk’awarin ci gaba da karatun ta ,Dan ta Kamala sakandiri dinta d batasu mu kamalawa ba aikin gidan NAWAL shine ya mata shamaki da karasa babbar sakandiri dinta ,Amman fa sai mijinta y amince.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button