HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Jin wanan kalma tafi komai Dadi ga Aishatu ,Dan sede tayi kwalar farin ciki ,Inna ko har gida tazo ta Mai godia d mama ….

 

Aishatu tanata samun karfin gwiwa d himma da kalaman da aunty zainab d nawara suke shigarma Aishatu cikin kwanyar ta Kan zaman Aurenta d safwan ,sun nuna Mata dama so daya take zuwar ma mutum Arayuwa,Dan haka y rage nata inhar tayi wasa d damar ta …

Aishatun Indo taji duk baya Nan su ta Kuma d’auka ,ta Kuma yadda da K’ADDARAR d ALLAH y jefo Mata cikin Rayuwar ta Dan haka Tana Addu’a wanan Aure y zamo Mata kyakywar kaddara !

Inna ma kulin cikin yima Aishatu nasiha take d nuna Mata duniya komai Dan ahankali ne ,tacire damuwa aranta d rungumi Abinda ALLAH y kaddara Mata d izinin ALLAH zataga nasarar hakan

 

Alhamdulillah! Indo ko yanzu Tana iya hada set na bag and shoe ,ran haka ko yanzu t rabu d Aunty Mai diki ta karu d wani Abu …

Mama d aunty zainab kulin cikin gyara Aishatu d Nawara suke in nd out ,ga shawarwari d da aunty zainab take cika musu kwanya d ita yadda ko basuyi amfani d wata ba zasuyi d wata …

Hydar y had’a shirya had a musu wani hadaden dinner party da hydar y daukin nauyin komai ,y Kuma jajirce Akan Dole safwan d Aishatu su halaci wajen Dan harda su y shirya komai ,Dan y karbi number safwan ya kirashi y sanar Mai d komai ,safwan duk yadda yaso goce ma haka haydar yaki bashi dama daga karshe hydar y nemi safwan d karyace komai Dan ALLAH, kuma zuwan shi wajen shine babban farin cikin kowa d ze halaci wajen ….

Safwan ba yadda y iya,ya karbi halacin d hydar yamai,har y sanar ma d Ammy dasu Yaya d hassana …

Ammy taji dadin karamcin d hydar y nuna ,ta Kara Jan kunnen safwan d y tabata ya halaci wajen…

Ussaina kusan tafi kowa farin ciki ,da jin dinner r aka shirya harda Amaryar su ,Dan haka Yaya y siyo musu anko d aunty sufaya da su Hassana Wanda zasu sa ran dinner Dan Taya kanin sa murna …

Da kanshi y sake dinkama kanin nashi ,boyel Mai tsada d kyau ,Dan zuwa gun dinna…

Su Ammy ma sunata Shirin su na tarban Amaryar su Indo Aishatu Mai Aikin d’anta ada ayanzu Kuma Amaryar SA Mai hankali d nutsuwa ga tarbiya d gani zasuyi Alfahari d shigowar ta cikin su tasan jikokin ta bazasuyi maraicin uwa ba …

 

Ammy ta umarci SAFWAN d ya gayama NAWAL ta Zo ta kwashe kayanta n can gidan Dan asan gyaran d za’aka Aishatu Kar ataba Mata Kaya taga anmata ba daidai ba ,y amsa d to ze sanar Mata ..

 

Harda yayi tunanin tura su ussaina y tuna irin rikicin da zai buyo baya Dan zata iya hucewa akansu y fasa ,Dan ko waya Bata hada shi d ita duk wata kafa d zata sadashi d NAWAL y tosheta …

D kyar y samu y kirata a waya ,tunda taga Kiran shi ,ta Fara shirya Rashin mutuncin d zata Mai kafin y nemi komawar ta gidan shi …

 

Bayan t d’auka ,batace komai ba yace nasan kina juna !

Tace kamar yadda kake jina ba!

Yace kiranki nayi n sanar Miki kiyi gagawan zuwa ki kwashe komatsen ki gudun karsu takurama amaryata Indo ‘yar Aikin ki Amman Ada Dan yanzu tun ranar d kikayi umarnin Kika barmata gurbin ki komai y Kamala Dan yanzu ta zama Aishatu matar safwan ,to inaso kizo ki Bata wadatacen waje Dan Tana bukatar hakan ! Kit y katse wayar ……

NAWAL ruwanta ne y Fara Shirin Hawa jinin ma kadan y rage y hau ,tsabar Bata ba safwan amsar maganar da ya gasa Mata Wanda yafi madaci daci ,bbn bacin ranta amsar d Bata mayar Mai ba ,Dan bashin d t biyo shi n munanan maganganun t kudiri aniyar zuwa d zazage Mai buhun bashi d yaci kafin t kwaso kayan karyayi tunani Tana mararin shi har yanzu …

 

Su Noor d Ammy Anata Hira ,ussaina n tsokanar su yaushe zasu wajen Aunty Aishatu ,Aiko Haneef y Soma rigima ,hassana ta Dana Mata duka a cinya Tana zata ja musu itako Ammy hararar ta takeyi kawai Tana cewa zata Fara ko?

Dake tun kwanakin baya kusan so uku hassana na kaisu dadyn sune yake zuwa y dauko su ,inba hakaba rigima suke Sha d su ussaina kafin su dawo ,shima ganin rigimar d sukeyi yace Adena kaisu tunda t kusa zuwa gaba daya ..

Jun wanan maganar ta faranta ran su Ammy gani sukeyi Yana mararin matar shi ne ,shiko yafi son farin cikin yaranshi sama d komai ….

 

Nawara t shirya musu lafiyayiyar walima d zasu gudanar ,Inna dai Bata kyarya iya Abinda zata iya shi takeyi ,na sha’anin biki t dage d kudin d safwan y ke Bata in yazo d kudin d Alhj su safwan y Aiko Mata dashi d Wanda Abban nawara y Bata da Wanda Indo ta Tara zata suyi sana’a duk ta had’a su take Shirin bigan kirji tayi wani Abun bajinta itama a bikin jikarta d ALLAH y rufama Asiri ta kowace siga …

 

Har yanzu safwan be bama Indo waya ba Ammy tamai magana yace so yake seta Zo Dan haka tace ba lefi Bata Kara Mai magana ba …

 

Ana saura sati 3 bikin tariyar Aishatu d SAFWAN …

NAWAL ta bugo sammako Dan ta San in ba haka tayi ba bazata Sami safwan a gida ba tasan yanzu baida mafaka sai gidan wanan Ammyn gwal din tasa …

Aiko taci sa’a Yana Nan ta shigo d ita d doccas d wata kawarta lawy ,tun wani bugun k’ofa d aka Mai yasan dangin marasa tunani ne ..

Bayan y bude musu b Gaisuwa b kalon mutunci ta shiga Tana karemai kalo ,har mabiyan nata …

Can tayi shewa tayi guda ango na INDODO bada kanka asare kaje kacema Ammyn gwal dinka y Fadi ,sai fa na gani akas zan tabatar sanan na sheda saboda na gani akas n kure ma makaryaci gudu yasa nazo muyi wanan game din Dan ALLAH Nanda sati 3 nazo nata Indodo Mai Aikin mu nida Kai Amman fa Ada
acikin gidan Nan Kuna hada shimfida d ita kana sata gaban mota Kuna keta unguwa d garin Nan a matsayin matar safwan …

Yayi Taki yace yarinya angama kijira 3 weeks din ki gani wawiya Mara tunani ,

Y fice daga parlor yace insun gama surufemai gidan Amaryar Sa Dan shi yanada abinyi …..

Aiko NAWAL ta yunkuro Tana huci Tana son fesar Mai da Abin d y taso Mata na tsananin bacin Rai Yama rainasu yamai dasu masu gadi? Ne ko ma’aikatan say zece su rufe Mai gida shi har y Gaya musu abinyi ,doccas CE dakatar d ita akan karta bishi ….

Shiko Yana jiyo hargagin ta ,y ficewar shi d mota ,me gadi y rufe Mai gidan …

Dama ba d’iban kayanne y kawo ta ba ,tazo masifane d amayar d Abin d yake cikinta ,gashi Bata Samu d gama amayarwa ba y barmata gidan Dan haka t hada kayan iya Wanda suka iya had’awa d niyar zatasa azo adiban Mata d tafi d kayan siturun ta dama d motar lawy sukazo …

 

Bayan tafiyar su me gadi y shiga y janyo parlour y rufe dama safwan y barmai key y dawo mazaunin gadin sa …

 

Me gadi nata murna Amarya ta kusa shigowa duk d bema San wacece Amaryar ba d murnar sa tafi haka…

 

Koda NAWAL ta koma gida Bata gayama mama yadda sukayi d safwan ba tasan ita zata ba rashin gaskia ,Dan haka t nuna Mata ma baya Nan suka d’ebo kayan suka taho ..,..

 

Aishatu d Nawara anata gyaran jiki ,ba lefi Aishatu tad’an saki jiki yanzu ganin nawara d take tare d ita ,itama gidan wani zata ,sadai ita Auren so sukayi d hydar d’inta ga kulawa d yake Shirin bama nawaran Suma sheda ne ,duk d itama safwan in agaban mutane ne yakanyi kokarin nuna kulawar say hanyar cewa ita matar sace Bata musayar kalaman soyyaya ba ,Amman bakamar su nawara ba ..

Amman tayi Alk’awarin Hakuri d juri a gidan shi matuk’ar zata samu farin cikin su Noor d su Hassana ba kowane zesan halin d zata shiga ba …

Biki nata matsowa bangarorin bikin duk sun gama shiri …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button